03.E.3 Script - WordPress.com

20
SCRIPT TITLE Written by Name of First Writer Based on, If Any Address Phone Number

Transcript of 03.E.3 Script - WordPress.com

SCRIPT TITLE

Written by

Name of First Writer

Based on, If Any

AddressPhone Number

THE BEGINNING OF EPISODE THREE

INT. GIDAN ALHAJI SADAU/FALO - DAY25 25

A nuno Alhaji Sadau yana zaune akan kujera gabansa kuma takardu ne a baje yana ta lissafi, hannunsa na hagu kuma kalkuleta ne a rike. Ya daura gilashinsa a saman hanci.

ALHAJI SADAUGabadaya jimla miliyan dari uku da saba’in kenan. Yauwa.

Yaci gaba da lisafi, Dansa Kamal yai sallama ya shigo falon,

KAMALSalamu Alaikum.

ALHAJI SADAUWa’alaikumus Salamu.

Ya nemi waje ya zauna a kasa, Alhaji Sadau ya dubeshi ta saman gilashi,

ALHAJI SADAU (CONT’D)Kamalu yaya akai?

KAMALIna wuni Abba.

ALHAJI SADAULafiya. Yaya akai?

KAMALDama Abba nazo ne batun motar da kace idan har na kammala karatuna zaka saya min ne. Shine nazo sake maka tuni, yau wata biyar kenan da kammala karatuna.

ALHAJI SADAUShine kazo ka sake min tuni?

KAMALEh.

ALHAJI SADAUHakane.

Alhaji Sadau ya cire gilashin dake idonsa ya ajiye a gefe, ya dubi kamal sosai.

ALHAJI SADAU (CONT’D)Ban san kai shashasha bane sai yau.

Kamal ya firgita,

KAMALShashasha kuma Abba?

ALHAJI SADAUKwarai! Katon shashasha kuma sakarai. Yo in banda kai sakarai ne, yaya za’ai na debi makudan kudade haka na sai maka mota? Haba kamalu, nawa nake da shi, dududu nawa na tara? Kana son ka fara girman kai kana hada kanka da ‘ya’yan wasu kou? To ahir din ka.

KAMALAllah ya huci zuciyarka Abba. Ni dama ba wai ina nufin ka bani kudin ne gabadaya ba, amma ko dan ciko ne ka min dan Allah idan dai har da hali.

ALHAJI SADAUAn ki a cika makan. Wato ina ta gargadinka da kai kanka yanda Allah bai kaika ba amma kana ta gujewa maganata kou? Na tambayeka mana.

KAMALTo Abba.

ALHAJI SADAUMotar nan dama waye yai maka alkawarin zai saya maka?

KAMALKai ka yi.

ALHAJI SADAUTo dadin baki ne kawai. Ba motar da zan saya maka, dama gatse nai maka dan na auna hankalinka; naga ko kana da hankali ko a’a. Ashe kuwa hasashena gaskiya ne baka da hankali ko kalilan.

KAMALAllah ya baka hakuri.

ALHAJI SADAUAmeen. Idan ya bani ka kwace. Tashi ka bani waje.

Ya bishi da kallo har ya fice daga falon,

2.

ALHAJI SADAU (CONT’D)Katon banza katon wofi.

Yaci gaba da lissafinsa.

ALHAJI SADAU (CONT’D)Nan ya zama miliyan tara kenan can kuma miliyan sha daya.

Camera ta dauke wajen.

FADE OUT.

INT. GIDAN ALHAJI HASHIM/FALO - DAY26 26

A nuno Alhaji Hashim yana tsaye a falo shi da Hajiya Zuwaira.

ALHAJI HASHIMBayan wannan ba komai kuma kou?

HAJIYA ZUWAIRAA’a babu. Sai dai abu daya da ka manta.

ALHAJI HASHIMMe kenan fa?

HAJIYA ZUWAIRABaka ce min I Love You Ba.

ALHAJI HASHIM(yai murmushi)

I Love You sosai.

HAJIYA ZUWAIRAHmmm Nagode. To a dawo lafiya kuma Allah ya kiyaye hanya Ameen.

ALHAJI HASHIMAmeen Ameen.

Daidai lokacin da yake karbar jakarsa a hannunta Umar ya shigo falon cikin fushi,

ALHAJI HASHIM (CONT’D)Kai kuma fa? Me ya faru, kuma wa ka tabo?

UMARAbba ka shiga tsakanina da Musa Direba ya fita a harkata, idan ba haka ba ransa zai baci.

3.

UMAR (CONT’D)Motata ya dauka fa da safen nan.

ALHAJI HASHIMWace motar kuma ke gareka?

UMARAbba motar da kace ka canja min jiya ita naje dauka kuma ban ganta ba.

ALHAJI HASHIMAu! Motar da kace ta sayo kayan miya ce, ita kuma kaje zaka dauka?

Umar yai shiru yana sosa keya,

ALHAJI HASHIM (CONT’D)Tuni na sa aka mayar da ita kamfani ai. Taka kuma da kake hawa, na sayar da ita da safen nan.

UMARTo ni wacce zan na hawa kenan?

ALHAJI HASHIMTa aiken gida mana. Ita zaka na shiga yanzu, haka ma idan mutanen gidan basu da abinda za’ai musu da motar.

UMARTa aiken gida kuma?

ALHAJI HASHIMKwarai kuwa. Ni matsa kaga na wuce zan makara zuwa wajen aiki.

Ya kewaye shi zai wuce,

HAJIYA ZUWAIRAA dawo lafiya.

ALHAJI HASHIMAmeen Ameen.

Ya sa kai ya fice. Itama ta shige cikin gida. A nuno Umar ya bata rai sai huci yake yi.

DISSOLVE TO:

4.

EXT. WAJEN SHAKATAWA - NIGHT27 27

A nuno Umar yana zaune shi da Abokansa a kasan laima a wajen shakatawa su uku da shi cikonsu na hudu kenan. Suna zaune suna cin shawarma da kuma lemuka ajiye kan teburinsu.

HABUWai meke damunka ne yau? Gabadaya sai wani bata rai kake ta faman yi tun da muka zo nan.

RABENima abin da nake shirin tambayarsa kenan ka rigani. Abokina me ke faruwa ne?

UMARKu dai ku bari kawai. Wai ace kamar ni Umar, dan Alhaji Hashim, ni za’ai wa abin da akai wa yau.

KAMALMe aka maka?

UMAROld Man dina mana. Wai dan Allah dan kawai ya siyo min mota jiya na kusheta, shine yau da safe kawai yasa aka maida motar wajen da aka sayota, ya kuma sayar da tawa motar. Yanzu haka da motar kanina Saleem nake yawo.

RABETab! Gaskiya Old Man din ku ya kwafsa.

HABUGaskiya bai kyauta ba. Ace babban gaye irinka dan hamshakin mai kudi a garin nan, amma ace wai baka da ‘yar motar nan ta hawa. Ai girma ya fado kenan.

RABETo yanzu wane mataki ya yanke zaka dauka?

UMARWane mataki zan dauka kuwa, illa na dauke ta Ummanmu gobe. Idan yaji haushe ya sayo mata wata.

5.

RABEKayi daidai wallahi.

KAMALAmma baka tsoron bacin ransa da kuma abin da zai biyo baya idan ran sa ya baci.

UMARShi bai ji damuwar bata min rai ba sai ni ne zan damu dan na bata masa rai? Ba abin daya dameni da bacin ransa.

KAMALKai Rabe da kai Habu ku ba abokan kirki ba ne. Maimakon ku ba shi shawarar yadda zai ba wa tsohonsa hakuri, amma sai kuke kara ingiza shi yana kara shiga jeji. Hakan da ku kai kuna ga abin kirki ku kai?

HABUKaga Malam. Mu fa ba wa’azi muka ce ka zo kai mana ba.

RABEKuma ma ai gaskiya muka fada. Ta yaya za’ai ace Babansa ya masa haka bayan duk irin kudin da yake da su makudai. Wannan ai yawa ne.

UMARNi matsalata da kai kenan. Babu dama mu yi abu sai ka fara yi mana wa’azi sai kace kai ka haifemu.

RABEAto. Kuma idan tsoron Allah ne ya fi mu ne.

HABUKuma ma wa zaka nunawa tsoron Allah?

KAMALKu zan nunawa tsoron Allah! Na tabbatar na fi ku tsoron Allah dan ba zan ki fadawa mutum gaskiya ba dan gujewa bacin ransa.

Ya dubi Umar,

6.

KAMAL (CONT’D)Ka sani da dama daga cikin mutane suna kwadayin irin damar da kake da ita yanzu, amma basu samu ba.

Ya kai kofin dake hannunsa bakin ya sha kadan sannan yaci gaba,

KAMAL (CONT’D)Kayi amfani da damarka ta hanyar da t dace tun kafin ta kubuce maka. Da nine nake da irin Old Man din ka Wallahi tsabar biyayya zan iya kwantawa ya bi ta kaina.

UMARM e k a k e n u f i d a w a d a n n a n maganganun?

KAMALIna nufin a tsarin rayuwa ta rayuwarmu Mu Da Iyayenmu ... Sai Allah! Wannan wani babi ne mai girma da mai hankaline kadai yake ganewa.

Umar yai tsuka yaci gaba da cin shawarmarsa. Sauran abokan biyu suka kyalkyale da dariya suka tafa,

HABU DA RABEYa Ustaz.

DISSOLVE TO:

INT. GIDAN ALHAJI HASHIM/FALO - DAY28 28

Alhaji Hashim yana zaune a cikin falonsa Saleem yai sallama ya shigo Alhaji Hashim ya amsa, Saleem ya nemi waje ya zauna.

SALEEMAbba ga ni.

ALHAJI HASHIMYauwa Saleem. Ka iso?

SALEEMEh Abba.

ALHAJI HASHIMYau saura kwana biyu Graduation din ka kou?

7.

SALEEMEh Abba.

Ya dauko wani abu a cikin kwali ya mika masa,

SALEEM (CONT’D)Menene wannan Abba?

ALHAJI HASHIMAlkawarinmu ne da mu kai na cika maka.

Ya sa hannu ya karba, ya bude kwalin. A nuno wani Qur’ani mai kyau a ciki. Anyi masa Wrapping mai kyau yadda gaban kawai ake iya gani. Ya dago ya dubi mahaifinsa da mamaki,

SALEEMAbba Qur’ani ne a ciki.

ALHAJI HASHIMEh Baban Umma. Wannan shine kyautar da nai niyyar baka.

SALEEMAbba ni da na tambayi mota kuma sai ka bani kyautar Qur’ani.

ALHAJI HASHIMIhmn. Ba kai farin ciki ba ne da hakan?

SALEEMA’a. Na yi.

Ya dan yi shiru kadan sannan yaci gaba,

SALEEM (CONT’D)Amma Abba mota kai min alkawari kuma sai ka ban Qur’ani... Ai...

Ya mike tsaye a fusace ya fice daga cikin dakin.

ALHAJI HASHIMSaleem... Saleem!

Yaki kulashi ya fice daga falon. Ya mike tsaye ya leka ta taga, a nuno Saleem a waje ya shiga motarsa ya fice daga cikin gidan a fusace. Alhaji Hashim ya dawo ya zauna shiru a kujera cikin takaici. Ya dauke Qur’anin ya maida shi cikin kwalin, ya rike Qur’anin a hannunsa, yana girgiza kansa cikin takaici.

FADE OUT.

8.

EXT. GIDAN ALHAJI HASHIM/FARFAJIYA - EVENING29 29

Alhaji Hashim ya fito daga cikin gidansa rike da jaka a hannunsa, Direba ya karba ya bude masa mota. Yana shirin shiga kenan Umar ya fito daga cikin gidan da sauri,

UMARAbba... Abba... Abba!

Alhaji Hashim ya fasa shiga motar ya dakata,

ALHAJI HASHIMYaya aka yi?

UMARDama kudin da na tambayeka ne Hajiya Baba ta bani, amma sai naga dubu tamanin kacal, ni kuma na san dubu dari na tambayeka.

ALHAJI HASHIMAbin da nai niyyar baka kenan.

UMARAmma Abba ai ka san ba zasu isheni ba.

ALHAJI HASHIMMe yasa ba ka da godiyar Allah ne Umar? Tafiya Excursion nan da Kaduna kwana uku kacal, kana nufin kace min dubu tamanin ba zasu isheka ba? Ubanka waye a garin nan? Ni fa ba kowa bane illa Hashimu dan Malam Iro daga Hunkuyi. That’s All.

Ya kira Direba da hannu, Direba ya matso,

ALHAJI HASHIM (CONT’D)Nawa ne albashinka a wata?

DIREBADubu tamanin da biyar.

ALHAJI HASHIMNauyin mutum nawa ne kuma akan ka?

DIREBABiyar.

ALHAJI HASHIMKudin suna isarka ko basa isarka bukatun ka?

9.

DIREBACi da sha da sutura da kyautatawa iyal aina duk a c ikin wan nan albashin nawa nake yi. Wani lokaci ma har adashe nake shiga a cikin wannan kudin.

Ya dubi Umar,

ALHAJI HASHIMKudin da yake isan wani rayuwa tsawon wata guda, kai da nauyin kowa bane akanka kake ce min ba zasu isheka kwana uku ba. Me ka dauki kanka ne? Kai waye?

UMARKoma dai menene ni dai Abba kudin nan sun min kadan.

ALHAJI HASHIMTo ba zan kara maka ba. Idan kuma ka raina dawo min da kayana.

Umar yaki mika masa komai,

ALHAJI HASHIM (CONT’D)Ka bar wajen nan tun kafin raina ya baci.

Umar ya fara kunkuni,

ALHAJI HASHIM (CONT’D)Ka bace min da gani. Ka bace min da gani nace!

Umar ya fara ja da baya yana kananan maganganu,

UMARAbba ka tara kudi kawai baka so muci. Wannan ai mugunta ne!

ALHAJI HASHIMSai kazo ka kasheni ai.

UMARAi dan ina tausayin su Umma ne shi yasa nake daga maka kafa. Amma ba dan haka ba, da tuntuni zan kara maka gudu zuwa lahira. Naci karena babu babbaka, na sakata, nai walwala yadda raina yake so.

10.

Direba ya rike bakinsa, Mai-Yankan Fulawa ya yarda almakashin da yake hannunsa, Maigadi ya bude baki tare da daura hannu akansa. Alhaji Hashim yai shiru ya rasa abin da zai ce. Umar kuwa ya ma fice daga gidan. Alhaji Hashim ya juya cikin gidansa cikin tsananin takaici ya koma, ya fasa fitar gabadaya. Ma’aikatan suka dubi junansu aka rasa mai magana a cikinsu. Camera ta dauke wajen.

CUT TO:

INT. GIDAN ALHAJI HASHIM/DAKI - NIGHT30 30

A nuno Likita yana duba Alhaji Hashim, ya gama duddubashi ya maida kayansa cikin jakarsa, ya dubi Hajiya Zuwaira da Hajiya Larai dake tsaye suna kallonsu, Hajiya Saratu kuma na tsaye a bakin kofa,

LIKITAHajiya ba komai ba ne ya sameshi illa dai jininsa ne da ya dan yi sama kadan. Wannan kuma ba komai ba ne na bashi magungunan da zai samu bacci sosai, zuwa safe insha Allahu yaji sauki.

Ya mika musu wata takarda Hajiya Larai ta karba,

LIKITA (CONT’D)Sai ku nemi wadannan magungunan.

Ya dubi Alhaji Hashim,

LIKITA (CONT’D)To Alhaji ni zan koma. Dan Allah koma menene yake damunka kayi kokari ka rage yawan tunanin akansa.

ALHAJI HASHIMInsha Allahu Likita. Nagode kwarai da gaske.

LIKITAAllah ya kara sauki Ameen.

Ya mike tsaye,

LIKITA (CONT’D)Hajiya na barku lafiya.

HAJIYA LARAIMungode Likita. Allah ya saka da alheri.

11.

Ya fice daga dakin. Hajiya Zuwaira ta zauna a bakin gadon,

HAJIYA ZUWAIRALarai sai ki hado masa abinci marar nauyi. Ki soya masa dankalin turawa da kuma kwai. Na dama kunu yana cikin Flask akan Dining Table. Ni zan zauna anan wajensa ko zai bukaci wani abu.

HAJIYA LARAITo.

Ta juya ta fice daga dakin. A nuno ita da Hajiya Saratu suna hararar juna. Hajiya Saratu ta karaso cikin dakin,

HAJIYA SARATUAllah ya kara sauki Alhaji.

Ya gyada kansa kawai. Ta fice daga dakin,

HAJIYA ZUWAIRAIna zuwa Alhaji. Na manta wani abu a wuta.

Itama ya gyada kansa kawai bai ce komai ba. Ta fice daga dakin da sauri.

MATCH CUT TO:

EXT. GIDAN ALHAJI HASHIM/FALO - NIGHT31 31

Hajiya Zuwaira tana fitowa daga dakin Alhaji Hashim tabi bayan Hajiya Saratu. Tana isota ta finciko Hajiya Saratu da karfi,

HAJIYA SARATUKutuma...

HAJIYA ZUWAIRAKi min shiru!

Ta daka mata tsawa. Hajiya Saratu ta hadiye maganar da take shirin yi, tai tsuru tsuru tana kallonta,

HAJIYA ZUWAIRA (CONT’D)Lokaci yayi da ya kamata ki sani ke da danki, idan baku daina cusawa Maigidan nan bacin rai ba wallahi muna dab da muyi muku dan banzan duka.

12.

HAJIYA SARATUDuka? Mu zaku...

HAJIYA ZUWAIRAKi min shiru nace!

Ta sake daka mata tsawa sannan taci gaba,

HAJIYA ZUWAIRA (CONT’D)Anya kina ma da burin shiga aljanna kuwa? Kin tarwatsa masa farin cikin gida, kuma kullum cikin cusa masa bakin ciki da bacin rai kike. Me kike so da shi ne? Ko so kike sai kinga bayansa sannan ki huta? Ki amsa mana!

Ta matso kusa da ita, yadda suna iya jin numfashin juna,

HAJIYA ZUWAIRA (CONT’D)Idan baki da hankali ya kamata kiyi karatun ta nutsu.

Ta juya ta koma dakin Alhaji Hashim, Hajiya Saratu ta fara haki tana rarraba ido.

HAJIYA SARATUKaga ‘yar iska ina kallonta shiru shiru haka ashe shegen karfi ne da ita haka kamar talauci.

FADE IN:

INT. GIDAN ALHAJI HASHIM/FALO - NIGHT32 32

A nuno Alhaji Hashim yana tsaye a cikin falonsa yana rike da carbi. Yai shiru kawai. Hajiya Saratu ta shigo cikin falon ta zo ta dauki kwanukan dake cikin falon ba tare da tace da shi komai ba. Ta juya zata fice,

ALHAJI HASHIMSaratu.

Ya dakatar da ita, ta waigo ba tare da tace da shi komai ba,

ALHAJI HASHIM (CONT’D)Hakika kinci amanar soyayya.

Ya saurara ko zata tanka da yaji tai shiru yaci gaba,

13.

ALHAJI HASHIM (CONT’D)Idan na tuna da soyayyar da muka yi da ke lokacin muna saurayi da budurwa, na kuma kwatanta su da irin halayenki a yanzu, tabbas kinci amanar soyayya. Idan har ke ba m ayau dari ya b a ce , to ke macuciya ce. Kin yaudareni na hada zuri’a da ke bisa makaryaciyar soyayya, kin kuma zalunceni kin tarwatsa min gida.

HAJIYA SARATUNi kuma na tarwatsa gida? Ta yaya?

ALHAJI HASHIMKo baki tarwatsa min gida ba, to tabbas kin bada gudunmawa mai karfi wajen tarwatsa farin ciki da zaman lafiyar gidan nan.

Yai shiru sannan yaci gaba,

ALHAJI HASHIM (CONT’D)Ba dan tausayinki ba da kuma rike amanar iyayenki da nake yi ba, da tu nt un i n a s ak ek i k in ko ma kauyanku. Amma wannan arzikin da na samu, bai kamata naci shi babu ke ba. Kece kika fara zama da ni tun bani da shi kafin kowa, a kullum na tuna haka na kan yi alfahari da ke na kuma yafe miki laifin da kike min; ina daukansu a matsayin sakarci.

Yai murmushin takaici,

ALHAJI HASHIM (CONT’D)So hana ganin laifi. Nai zaton zaki canja halayenki, ki zama mutumiyar kirki. Amma a yau na cire tsammanin hakan. Tabbas ke ce matsalar gidana ke da danki. Amma ba zan yi muku baki ba. Inai muku addu’ar Allah ya shiryar da ku ya kuma yafe muku.

Yai shiru kadan sannan yaci gaba,

ALHAJI HASHIM (CONT’D)Nai nadamar kasancewarki uwar ‘ya’yana. Nai nadamar saninki a rayuwata. Nai nadamar halaccin da nake miki a yan zu.

14.

(MORE)

Nai nadamar komai da ya shafeki. Fice ki bani waje.

Ta tura baki zata fice,

ALHAJI HASHIM (CONT’D)Mata nagari ko da sun san su ke da gaskiya ba da hakuri suke ga mazajensu. Na yafe miki duk da baki tamabaya ba. Inai miki addu’ar Allah ya shiryeki Ameen.

Tai shiru alamar maganarsa ta ratsata. Ta sunkuyar da kanta kasa ta fice daga falon. Ya bita da kallo har ta fice. Ya daga hannayensa sama,

ALHAJI HASHIM (CONT’D)Allah ka zamto shaida, na yafewa Saratu da Umaru. Ina kuma fatan ka shiryesu don rahamar.

Yai ajiyar zuciya cikin takaici, aka dauke wajen.

FADE OUT.

EXT. WAJEN SHAKATAWA - NIGHT33 33

A nuno Saleem yana zaune a karkashin laima wajen shakatawa yana shan laimu. Yana zaune shi kadai yai shiru yana tunani.

UMAR (V.O.)(yana mag ana a ci kin zuciyarsa)

Duk da nasan mahaifina bai kyauta min ba, dan abin da yai min alkawari daban, shi kuma abin da ya bani daban, amma bai kamata na nuna masa bacin raina ba. Kamata yayi ace na nuna masa jin dadina; na kuma boye bacin raina, na kuma gode masa duk da a cikin raina ba haka bane. Gaskiya ban kyauta ba. Bari naje na bashi hakuri.

Ya shanye sauran lemun, ya mike tsaye da sauri ya dauki makullan motarsa ya nufi hanyar fita daga wajen.

DISSOLVE TO:

15.

ALHAJI HASHIM (CONT’D)

EXT. GIDAN ALHAJI HASHIM/FARFAJIYA - NIGHT34 34

A nuno Direba da Maigadi suna zaune akan benci a bakin get suna cin gyada.

DIREBATun da nake ban taba ganin abin mamaki mai ban tsoro ba irin na yau.

MAIGADIMe kenan haka?

DIREBAUmaru da Alhaji dazu! Kai! Yaron nan bai da mutumci Malam. Ko kalilan. Wallahi da na haifi da irin Umar, Allah gwanda na mutu babu haihuwa.

MAIGADIKai ma kenan da shekarunka basu kai nawa ba. Tabbas idan Umar bai shiga taitayinsa ba, bala’in da zai same shi a rayuwa nan gaba, sai ya gwammaci kida da karatu.

DIREBAAbin babu dadi ko kadan. Sai kace a mafarki.

MAIGADINa rasa me yaran nan suka nema a rayuwa suka rasa. Amma kaf gidan in ka dauke Hajiya Zuwaira da Abubakar babu wani wanda Alhaji zai kalla zuciyarsa tai sanyi.

DIREBANi ba wannan ba ne ba ma...

Direba ya katse maganar da yake yi, duk suka maida dubanu kan Umar ido wanda ya fito da gudu daga sashen Alhaji Hashim ya nufosu,

DIREBA (CONT’D)Kai lafiya? Menene?

UMARAlhaji ne... Alhaji ne...

MAIGADIMe Alhajin yayi? Dukanka zai yi?

16.

DIREBABiyoka yayi?

Duk ya girgiza musu kai yana haki,

UMARAlhaji ne..... Yace ku shiga sashensa ku same shi.

DIREBAMe yake faruwa ne?

MAIGADIKai menene haka ne wai?

Ya kasa magana sai alama kawai da yake tayi musu da hannu,

DIREBAKayi magana mana.

UMAR(ya daka musu tsawa)

Yace ku je yanzun nan!

DIREBAMuje mu ji dalilin kiran.

Duk su kai sashen da gudu Umar kuma ya fice daga gidan a guje.

MATCH CUT TO:

INT. GIDAN ALHAJI HASHIM/FALO - NIGHT35 35

Direba da Maigadi suka shigo falon Alhaji Hashim a tare,

DIREBASalamu....

Ya kasa karasa sallamar, sakamakon ganin Alhaji Hashim a kwance a kasa da su kai yayi dumu-dumu da jini. Gefen cikinsa kuma wuka ce a soke, sannan goshinsa ga harbin bindiga. Duk su kai carko-carko aka rasa mai karasawa kansa,

MAIGADIInna lill ahi Wa I nna Ilai hir Raji’una.

DIREBA(ya fara hawaye tare da gir giz a k ans a c iki n takaici)

Ya kashe shi... Ya kashe shi...

17.

(MORE)

Ya kashe shi... Wallahi ya kashe shi kamar yadda ya fada.

Maigadi yai baya ya fice a dakin da gudu yana kiran sunan Matan gidan.

MAIGADIHajiya Zuwaira... Hajiya Zuwaira... Hajiyoyin gidan nan... Wayyehoho jama’a... Jama’a!

Hajiya Larai da Hajiya Saratu shigo cikin dakin da gudu duk su kai turus da ganin Alhaji Hashim kwance cikin jini. Hajiya Saratu ta fashe da kuka, sannan a hankali ta durkushe akan gwuiwoyinta ta fashe da kuka mai karfi, Hajiya Larai kuma tai tsaye kawai ta kasa karasawa kan Alhaji Hashim tana ta kallonsa kawai tana hawaye. Hajiya Zuwaira ta karaso cikin dakin da gudu, ta isa kansa, ta tsuguna,

HAJIYA ZUWAIRAInna lill ahi Wa I nna Ilai hir Raji’una.

Ta leka shi ta tabbatar da cewar tabbas ya mutu, ta sa hannunta ta rufe masa idanuwansa, ta mike tsaye ta koma cikin Corridor ta bar dakin, ta jingina da jikin bango, a hankali ta saki kuka mai ratsa zuciya, ta kuma fara yin kukan mai dan sauti kadan, sannan ta bi jikin bangon ta durkushe a kasa tana hawaye,

HAJIYA ZUWAIRA (CONT’D)Wayyo Allah duniya.

Taci gaba da kuka mai tsuma zuciya da ban tausayi. A nuno cikin falon kuma kowa yana kuka. Hajiya Saratu ta dubi fuskar Alhaji Hashim; fuskar dake yi mata murmushi har bayan rai, ya mutu da murmushi a fuskarsa. Ta sake fashewa da kuka ta kuma dubi wani hoto dake kallonsu; hotonsa babba, ta sake fashewa da kuka sosai. Hajiya Larai dake tsaye har yanzu ta zube kasa a sume. Hajiya Saratu ta dubeta ta dauke kai, ta sake fashewa da kuka,

HAJIYA SARATUKaico! Kaico! Wayyo duniya!

Babu wanda ya kula da suman da Hajiya Larai tai duk kowa yana ta kansa. A nuno wani hoton Alhaji Hashim dake makale a falon, yana murmushi, a hankali aci gaba da daukan hoton har ya cika Camera sannan a dauke wajen.

CUT TO:

18.

DIREBA (CONT'D)

EXT. SOMEWHERE ON THE STREET - NIGHT36 36

A nuno Umar a zaune a cikin motarsa yana hawaye da kuma kuka mai karfi. Ya bugi sitiyarin motar ya kuma kara fashewa da kuka. Ya duba bayansa, ya hangi gidansu, ya girgiza kansa, ya tayar da motarsa, ya tashi da cin taya ya bar wajen. Daidai lokacin da motar jami’an tsaro take shan kwana, shima yana shan kwana. Ya hau kan titi sosai, ya dau hanya ya filla aguje yana tafe yana kuka mai karfi.

THE END OF EPISODE THREE

LABARIN HIKAYARMU KENAN FA MU DA IYAYENMU DAI NA DAUKOHIKAYAR DA MAI HANKALINE KADAI ZASHI GANE. ITACE DAI NA DAUKO

19.