Modibbo Kilo (1901-1976) Rayuwarta da Ayyukanta (Ta Biyu ga Nana Asma'u Bin Fodiyo a Karni na 20)

332
Modibbo Kilo (1901-1976) (Ta Biyu ga Nana Asma’u a {arni na 20) Rayuwarta da Ayyukanta

Transcript of Modibbo Kilo (1901-1976) Rayuwarta da Ayyukanta (Ta Biyu ga Nana Asma'u Bin Fodiyo a Karni na 20)

Modibbo Kilo (1901-1976) (Ta Biyu ga Nana Asma’u a {arni na 20)

Rayuwarta da Ayyukanta

ii

iii

Modibbo Kilo (1901-1976) (Ta Biyu ga Nana Asma’u a {arni na 20)

Rayuwarta da Ayyukanta

Dr. Sa’adiya Omar

iv

© Dr. Sa’adiya Omar, 2013

ISBN: 978 – 125

Bugawa:

Kamfanin Xab'i na Jami'ar Ahmadu Bello,

Jakar Gidan Waya 1094, Samaru, Zaria, Nijeriya.

Tarho: 08065949711

Adireshin Yanar Gizo: www.abupress.org

Imel: abupresslimited2005”yahoo.co.uk

v

Sadaukarwa

Na sadaukar da wannan littafi ga Mallam Ibrahim

Gandi Junaidu, wanda shi ne mafari, kuma mai

fafutukar a rubuta littafin. Mallam Ibrahim ya yi burin

ganin littafin ya fito lokacin rayuwarsa, amma Allah bai

nufa ba. Allah Ya gafarta masa, Ya ji}an sa, Ya sa

aljanna ce makoma a gare shi da mu baki]aya. Allah

Ya albarkanci zuri’arsa.

vi

Qumshiya

Sadaukarwa

Godiya

Muqaddima

Gabatarwar Mawallafiya

Babi Na [aya: Salsala da Rayuwar Modibbo Kilo

Salsalar Modibbo Kilo

Haihuwar Modibbo Kilo

Neman Ilminta

Aure da Iyali

Ayyukan Modibbo Kilo

Ayyukan da ta yi a Sakkwato

Ayyukan da ta yi a Makka

Yanayinta da Halayenta

Kwarjini da Karamar Modibbo Kilo

Wasiyya da Rasuwar Modibbo Kilo

Wasiyyar Modibbo Kilo

Rasuwar Modibbo Kilo

Babi Na Biyu: Rubutattun Waqoqin Modibbo Kilo

Nazarin Wa}ar Hijirar Modibbo Kilo da Zamanta a

Makka

Wa}ar Hijira da Zaman Modibbo Kilo a Makka

Nazarin Wa}ar Al}ur’ani

Wa}ar Al}ur’ani

Nazarin Wa}ar {abli da Ba’adi

Wa}ar {abli da Ba’adi

Nazarin Waqar Nasiha Game da Gavvai Bakwai

Wa}ar Nasiha Game da Ga~o~i Bakwai

Nazarin Wa}ar Taya Murna ga Al}ali Umaru

vii

Wa}ar Taya Murna ga Al}ali Umaru

Nazarin Wa}ar Burin Modibbo Kilo na Zuwa

Makka

Waqar Burin Modibbo Kilo Na Zuwa Makka

Nazarin Wa}ar Hikaya

Wa}ar Hikaya

Nazarin Wa}ar Hatsin Bara

Wa}ar Hatsin Bara

Babi Na Uku: Rubutun Zube

Labarin Manzancin Annabi Muhammad Da

Halifancin Sahabbai Da Mulkin Daular Usmaniyya

Farkon Al’amarin Mujadaddi Nuruz Zamani,

Labarin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello

Labarin Abubakar Atiku sha}i}in Muhammadu Bello

Labarin Sarautar Aliyu [an Muhammadu Bello

Labarin Sarautar Ahmadu [an Atiku

Labarin Sarautar Aliyu {arami [an Muhammad Bello

Labarin Sarautar Ahmadur Rufa’i [an Mujaddadi

Usmanu

Labarin Sarautar Abubakar Atiku {arami Mai Ra~ah

[an Muhammadu Bello

Labarin Sarautar Mu’azu [an Muhammadu Bello

Labarin Sarautar Umaru [an Aliyu

Labarin Sarautar Abdu [an Atiku [an Mujaddadi

Usmanu

Labarin Sarautar Attahiru [an Ahmadu

Labarin Sarautar Attahiru [an Aliyu Babba

Labarin Sarautar Muhammadu [an Ahmadu

Labarin Sarautar Muhammadu [an Muhammadu

Labarin Sarautar Hassan [an Mu’azu

viii

Labarin Sarautar Abubakar [an Usmanu

Labarin ‘Yan’uwan Mujaddadi Usmanu

Labarin Matan Shehu Usmanu

Labarin ‘Ya’yan Shehu Maza Da Mata

Labarin ‘Ya’yan Muhammadu Bello

Labarin Rasuwar ‘Ya’yan Shehu Usmanu

Labarin Abdullahi [anfodiyo

Labarin ‘Ya’yan Abdullahi Fodiyo

Wasiyyar Modibbo Kilo

Babi Na Huxu: Waqoqi a Kan Modibbo Kilo

Wa}o}in Fa]ima Zuwa Ga Modibbo Kilo

Nazarin Wa}ar Ha]uwar Fa]ima da Modibbo Kilo

Ha]uwar Fa]ima da Modibbo Kilo

Nazarin Wa}ar Godiya ga Modibbo Kilo

Nazarin Wa}ar Bankwana ga Modibbo Kilo

Wa}ar Bankwana ga Modibbo Kilo

Ratayen Waqoqin Modibbo Kilo

ix

Godiya

Da sunan Allah mai rahama mai jin}ai.

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai Wanda Ya

ba ni ikon rubuta wannan littafi. Yabo da sallama a bisa

Annabimmu Muhammad, tsira da amincin Allah su

tabbata a gare shi da Alayensa da Sahabbansa da

wa]anda suka bi tafarkinsu har zuwa ranar sakamako.

Muhimmiyar godiya da addu’a ga Mal. Ibrahim

Gandi Junaidu wanda ya ]ora ni bisa tafarkin bincike a

kan wannan shahararriyar Malama ta Sakkwato. Hakan

ya faru ne bayan na gabatar da takardu a kan Nana

Asma’u (Uwar Gari) da ‘yar’uwarta Maryam (Uwar

Daje) duka ‘ya’yan Mujadaddi Shehu Usmanu

[anfodiyo, a taron }ara wa juna sani na Cibiyar

Nazarin Hausa, Usmanu Xanfodiyo University, Sokoto.

Malam Ibrahim Gandi ya ja hankalina a kan cewa,

akwai wata babbar Malama, Modibbo Kilo wadda ba a

fito da ita fili ba, don haka ya shawarce ni da in

yi }o}ari in yi bincike da rubutu a kan ta. Mun yi fa]i

tashi da shi wajen neman bayanai, har lokacin da na

fara rubuta wannan littafi, amma Allah bai }addari ya

ga }arshen rubutun da fitowar littafin ba. Ibrahim

Junaidu, Allah Ya lullu~e ka da rahamarSa.

Ina godiya }warai ga iyalin gidan su Modibbo

Kilo, cikinsu akwai Alhaji Abubakar Garba Takardawa

da Alhaji Umar Faruku Usman da Al}ali Riskuwa

Abdul}adir da Malam Abdullahi Al}ali da Hauwa’u

Al}ali Isa (Sutura) da sauran iyalin wannan gida,

wa]anda suka kar~e ni hannu bi-bi-yu, suka kuma ba

ni cikakken goyon baya da bayanai. Taimakonsu ya ba

x

ni }warin gwiwa, ya kuma sau}a}a mini yin wannan

aiki cikin walwala. Allah ya saka musu da alheri.

Ba zan manta da taimakon da abokin aikina

Malam Ahmad Abdullahi Sokoto (A.A. Sokoto) ya yi

mini ba wajen gyare–gyaren rubutun da aka buga da Computer , yin haka ya rage mini lokacin dubu rubutun.

Allah Ya saka masa da alheri.

Godiya ga Halima Ladidi Ibrahim wadda Malam

Ibrahim Gandi kan kira ‚ ‘Yar Kurmar Dokta Sa’adiya‛,

domin kamar yadda Modibbo Kilo ke tare da mai

hidimarta Kurma, haka Ladidi ke tare da ni wajen fa]i-

tashi na neman bayanan wannan littafi. Allah Ya saka

mata da alheri.

Da yake fa]in wannan bincike ya kai }asar Saudi

Arabia, na sami mutanen da suka taimaka mini da

bayanai a kan rayuwar Modibbo Kilo a garin Makka.

Cikin su akwai Hajiya Kulthum, ( Gwaggo Gambo) da

Safiyyah (Ni’imat) da Hajjah Hafsah da Hajjah

Ruqayya. Ba don bayanan da na samu a wurin su ba, da

wannan aiki ya sami gi~i. Ina godiya gare su, Allah Ya

saka musu da alherinsa.

Ina addu’a ga maigidana, marigayi Dr. Omar

Bello. Allah ya jiqansa, ya kuma lulluve shi da

rahamarsa, amin. Ina kuma sa albarka da godiya ga

‘ya’yana Muhammadu Foduye (Fodio) da Fatima

Bajjo-Mango da Ikram da Taybah da Usman Mo]agel

da mazaje da matayensu, wa]anda suka ba ni taimako

da goyon baya da yi mini addu’a domin samun nasarar

aikin. Allah Ya }ara yi muku albarka ya yi wa

rayuwarku jagora.

Ina godiya ga ‘yan’uwana sha}i}ai, Hajiya

Ramatu Inuwa Dutse da Dr. Shamsuddeen Usman,

Minister a ma’aikatar National Economic Planning

xi

Abuja, kuma tsohon Ministan ku]i a Nijeriya, wa]anda

suka taimaka mini da addu’a da kuma gudunmawa

domin buga wannan aiki.

Ina mi}a godiyata ga Malami Aliyu {asarawa,

wanda ya yi gwagwarmayar buga wannan littafi a

Computer. Allah Ya saka masa da alheri.

Fili ba zai bari in kawo duk wa]anda suka

taimaka mini wajen ba da bayanai da tallafi da addu’a

ba. Don haka ina godiya ga dukkanin wa]anda suka sa

hannu a wannan aiki, ta hanyar addu’a da fatar alheri,

saboda na san fitowa da muhimman mata irin su

Modibbo Kilo, wa]anda suka yi wa Addinin Musulunci

hidima, ba }aramin alheri ne ba ga al’umma. Allah Ya

kar~i wannan aiki a matsayin ibada gare mu, Ya kuma

ba mu sakamako na alheri.

Wa Akhiriu Da’awana Anil Hamdu Lillah, Wassalamu

Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuhu.

xii

Muqaddima

Na fara da sunan Ubangiji Allah Mai gamammar

kyauta nan duniya, Mai kevavvar kyauta gobe lahira.

Tsira da aminci su tabbata ga Manzonsa Muhammadu

da Alayensa da Sahabbansa, da masu bi bisa tafarkinsu,

har ranar Al}iyama.

Ina mai roqon Ubangiji Allah, Ya ba ni iko da

basira, Ya kuma yi mini jagora ga gabatar da wannan

gagarumin aiki na Dr. Sa’adiya Omar, Ya kuma amfane

mu da hikimomin da suke qumshe cikinsa, amin.

Kafin in ci gaba da gabatar da wannan gagarumin

aiki, ina son in bayar da bayani ka]an, ga wanda bai

san yanayin yadda wasu irin su Modibbo Kilo suka

tashi, suka rayu a cikin sa ba. Ina kuma fatar a gane

cewa, abin lura a nan shi ne, littafi kowane iri kuma a

kowane harshe, abu ne da ke bazuwa ko’ina cikin

duniya, tun ma ba duniyar ga tamu ta yau ba. Haka nan

kuma, duk da bayanan da ke ƙumshe a cikin wannan

littafi, ya kamata a san bagiren da Modibbo Kilo ta rayu

kuma ta sami nata sani. A nan ina nufin Birnin

Sakkwato, wanda Muhammadu Bello ]an Usmanu

Xanfodiyo, Allah Shi yarda da su, ya kafa.

Muhammadu Bello kuwa yana cikin waxanda suka yi

jihadin xaukaka Musulumci.

Jihadi a musulunce, na nufin, qoqari tare da

jimriya a kan niyyar da mutum ya qudurta. Su Shehu

Usmanu Xanfodiyo kuwa, sun qudurta da’awa fi

sabilillahi da duk abin da ya qumsa na tafiyar da

karantarwa da jawo hankalin jama’a zuwa Musulmci,

kai har ma da sadaukar da rai ga yaqi in ta xauro. Sun

mayar da mafi qarfinsu ga yaxa addini ta kowace

xiii

hanya, tun ma ba karantarwa ba ga maza da mata.

Lokacinsu sani ya yaxu tsakanin maza da mata.

Farkon abin da suka fi mai da qarfi gare shi,

kamar yadda na ambata, shi ne sani, wanda shi ne

gimshiqi kuma wajabtacce ga musulumci. Makarantu

sun havaka a lokacin jihadi, ba a Sakkwato kaxai ba har

ma kamar su Kano, Katagum, Adamawa, Ilori, Bidda,

Marwa a Kamaru da Baucin Yakubu tun ma ba Katsina

ba, inda aka yi wani babban masani da aka sani da

Xanmasani kafin lokacin Jihadi. Malamai sun mai da

qarfi ga yaxa sani iri-iri, kamar su Fiqihu, Tauhidi,

Tarihi, Xibbu, Siyasa, Tsarin Mulki da kuma harshen

Larabci. A karatu da sani ba a bar mata a baya ba.

Malama Asama’u xiyar Shehu Usmanu Xanfodiyo,

wadda aka fi sani da Nana Uwar Gari, ta yi fice. Ta

rubuta littafi har tamanin da shidda (86). To Modibbo

Kilo tana cikin waxanda wannan damar ba ta wuce su

ba, kamar yadda za mu gani cikin wannan littafi. Don

haka sai mu yi farin ciki, mu gode wa Dr. Sa’adiya.

Omar da ta yi bincike mai zurfin gaske, ta gano muna

wannan Modibo kuma ban shakkar cewa har yanzu da

wasu irin Kilon waxanda ya kamata a binciko.

A wannan lokaci ba a bar mata a baya ba, domin

kuwa a tsarin addinin musulumci, sani wajibi ne ga

namiji da tamace. Mata sun yi karatu kuma sun qware

kamar maza, sun kuma yi rubuce-rubuce da dama a

fannoni daban- daban. Amma a nan, wannan ba shi ne

manufata ba. Manufata a nan, ita ce in gabatar da

wannan gagarumin aiki na wata gagarumar malama da

ta gano muna wata gagarumar malama.

Kullum ana cin karo da binciken da ba a zata ba.

Sani kullum daxa yaxuwa yake yi, har inda ba a zato.

Ayukkan mata na tarbiyantarwa, a gari kamar

xiv

Sakkwato kuma a qasa kamar Nijeriya, ya yaxu ya

wuce Cadi da Sudan har zuwa Makka. Irin wanga

binciken ne, ake kira, ‘a ja kwaranga ta ja kurmi’.

Wajen bincike da allura, Dokta Sa’adiya Omar, ta yi

zama, ta yi karo da galma, Alhamdu Lillahi. Dokta

Sa’adiya Omar ta binciko, ta kuma gano muna wata

gagarumar, mashahuriyar malama, mai suna Modibbo

Kilo, wadda ta yi rubuce-rubuce, bayan karantarwa da

tafsirin Alqur’ani mai girma. Dokta Sa’adiya Omar, ta

yi bayani isasshe a kan Modibbo Kilo, ta mayar da

qarfi, ga rubuce-rubucen Moddibbo Kilo na waqe da na

zube, wanda ya zo a cikin Ajami da Larabci.

Littafin ya yi bayanai masu gamsarwa, a

vangaren Harshe da Adabin Hausa. Dokta Sa’adiya

Omar ta yi wa wannan aikin cikakken adalci, yadda duk

ya kamata. Ta bayar da bayani a kan Modibbo Kilo

cikin tsanaki ba tare da wani son zuciya ba. A cikin

wannan littafi da ya qumshi tarihin Modibbo Kilo,

wanda Dr. Sa’adiya Omar ta lemo muna, na dukkan

hikimomi da fasaha da hangen nesa na Modibbo Kilo a

yalwace, daga Nijeriya har Makka, ta hanyar kawo

abubuwan da suka gudana a tsakanin Nijeriya da Cadi

da Sudan da Makka. Wannan aiki ya tabbatar da

qoqarin masu Jihadi, na ba mata sani, yadda addinin

Musulumci ya tanada. Modibbo Kilo kuwa ba ta yi

kuren amfani da wannan zamar ba.

Kamar kowane harshe ga bayyana al’ada da

zamantakewar xan-adam, Dr. Sa’adiya Omar, ta gwaji

cewa, ta qware ga yin bayanin sarqaqiyar rayuwa da

canje-cajen da ta qumsa a cikin wannan aiki, yadda duk

malamar Harshe da Adabi ya kamata ta yi. Hakika

wannan gagarumin aiki, ya qumshi cikakken tunani da

zai amfani manya da yara har ma da xaliban Hausa da

xv

masu binciken adabin Hausa a matsayin Jami’a da

sauran makarantu.

Ina daxa fatar, Maxaukakin Sarki Allah, Ya

amfane mu da abin da wannan littafi ya qumsa, Ya

kuma ba waxanda suke da niyyar bincike, gano muna

taskokinmu, waxanda suke voye, irin na su Moddibo

Kilo, amin. Ita kuma Dr. Sa’adiya Omar, mun gaishe ta

da qoqari kuma muna fatar ta ci gaba da irin wannan

bincike. Daga qarshe, muna roqon Allah, Ya saka mata

da mafificin alherinSa, amin.

Prof. Ibrahim A. Mukoshy

Department of Nigerian Languages,

Usmanu [anfodiyo University,

Sokoto.

30-08-2013

xvi

Gabatarwar Mawallafiya

Ina cike da farin cikin rubuta wannan littafi, saboda

ganin cewa shi ne littafi na farko da aka rubuta a kan

Modibbo Kilo, mace wadda ta shahara wajen ilmi da

karantarwa da rubuce-rubuce a }arni na 20. A wajen ba

wa wannan littafi suna, na }ara da cewa, Modibbo Kilo

mace ce ta biyu ga Nana Asma’u. Na kwatanta ta da

Nana Asma’u, ]iyar Shehu Usmanu [anfodiyo, saboda

a nawa ra’ayi ba ta da abokiyar kwatanci kamar ta,

ganin irin }o}arin da ta yi na neman ilmi da

karantarwarta ga al’umma da rubuce-rubucen da ta yi

da sauran al’amuran sadaukar da kai da ta yi zuwa ga

addini.

A nawa gani Modibbo Kilo wata tauraruwa ce

mai kama da Nana Asma’u wajen karatu da karantarwa

da rubuce-rubuce,wadda aka samu a nata }arni na 20,

amma hasken tauraruwarta bai bayyana ba sai yanzu.

Ganin cewa ban ci karo da wani aiki da aka yi a kanta

ba, ya sa na ]aura ]amarar farko, na du}ufa domin in

fito da ita ga idon al’umma wa]anda ba su san da ita ba,

in kuma fara kawo ayyukanta wa]anda suke ~oye,

wa]anda na yi fafutukar za}ulowa domin nazari.

A wajen rubutun wannan littafi, an tsara shi zuwa

babi-babi. A babi na farko an fara kawo tarihin

Modibbo Kilo. Wajen binciken tarihin, an gano cewa

Modibbo Kilo ]iya ce, kuma jika ga manya-manyan

Malamai wa]anda suka shahara, suka yi hijira domin

Allah. Mahaifinta da sauran malamanta sun ba ta

zuzzurfan ilmi, sakamakon haka ta zama babbar

Malama wadda ta karantar, ta yi tafsiri ta kuma yi

rubuce-rubuce na zube da wa}a. Ga halaye, Modibbo

Kilo mai tsoron Allah ce da tsentseni da duniya da

xvii

sauran halaye da ]abi’u masu kyau wa]anda ke jan

mutane zuwa gare ta.

Babi na biyu ya zo da ayyukan da Modibbo Kilo

ta yi a kan rubutacciyar wa}a. Kafin a kawo wa}o}in,

wa]anda aka fassara daga ajami zuwa boko, sai da aka

yi musu gajerun nazarin jigo, domin a gane sa}on da

kowace wa}a take ]auke da shi. An fara da wa}ar

Hijirar Modibbo Kilo daga Sakkwato zuwa Makka.

Wajen warwarar jigon an fara binciko, kuma aka

rattaba hanyoyi ko garuruwa da }asashen da ta yi ta

ratsawa wajen yin wannan hijira. Hakanan an kawo ire-

iren mutanen da ta ha]u da su da wahalhalun da ta sha

da abubuwan al’ajabi da ta gani kafin ta kai ga inda ta

hara. Duk wa]annan wahalhalu da ta sha, ta yi dauriyar

su ba don kome ba sai don Allah da manzonSa kamar

yadda ta ce. A wa}ar an gano irin zaman da Modibbo

Kilo ta yi a Makka da taimakon da ta yi na sanar da

mutane addini da tabbatar da cewa hijirar da ta yi ta

Allah da manzonSa ce.

‘Wa}ar Al}ur’ani’, ta zo ne da bayanan

abubuwan da ke cikin Al}ur’ani mai girma, wato abin

da ya shafi surorinsa da kalmominsa da haruffansa da

ayoyinsa da hizbi-hizbinsa da sumuni-sumuninsa

da }ira’o’in karatunsa da yadda ake sujadodin

karatunsa da sauransu. Wa}ar {abli da Ba’adi

na }unshe da bayanai game da kurakuran da ke sa a

yi }abla da ba’ada cikin salla da kuma kurakuran da ba

su sa a yi su. A wa}ar ‘Nasiha Game da Ga~o~i

Bakwai’ kuwa, Modibbo Kilo ta yi wa jama’ar

Musulmi maza da mata nasiha ne, game da yadda za su

kiyaye ga~o~i bakwai na jikinsu. A wa}ar ‘Taya

Murna ga Al}ali Umaru’, Modibbo Kilo ta nuna farin

ciki da murna a lokacin da aka na]a kawunta Al}alin

xviii

Wurno Umaru, a matsayin limanin masallacin Shehu na

Sakkwato. ‘Burin Modibbo Kilo na ta sami tafiya

Makka da Madina ta kuma yi zamanta a can, ya zo a

cikin wa}arta ta ‘Burin Modibbo Kilo na Zuwa Makka’.

*Hakanan ta rubuta ‘Wa}ar Hikaya’ domin ba da

bayani ne dangane da wani labari da kakanta Al}ali

Abdullahi ]an Ladan Rame ya ba ta, game da gasar da

ya yi tare da wani mutum. A wa}arta wadda na bai wa

suna ‘Hatsin Bara’, saboda tana }unshe da abubuwa

daban-daban, Modibbo Kilo ta kawo al’amarin kiran da

Shehu Usmanu [anfodiyo ya yi da kuma kar~ar kiran

da jama’a suka yi da wasu labaran su Shehu da nasiha

da garga]i ga Malamai da Sarakuna da al’amarin

zamanta a Makka da sauransu.

Babi na uku ya kawo rubutun zube na Modibbo

Kilo kuma duk da na sami bayanin cewa Modibbo Kilo

ta yi irin wa]annan rubuce-rubuce, wa]anda mafi

yawancin su ba su kawo ga hannu ba, duk da hakanan

na sami wani muhimmin aikinta na rubutun littafi, a

inda ta kawo ta}aitattun bayanai game da wasu

Annabawa da halifancin sahabbai da kuma mulkin

Daular Usmaniyya.

A babi na hu]u ne aka kawo wa}o}i wa]anda

aminiyar Modibbo Kilo, Fa]imatu ta rubuta gare ta.

Wa}o}in sun ha]a da wadda Fa]imatu ta yi bayanin

farin cikin da ta yi a lokacin da ta sadu da Modibbo

Kilo da wa}ar godiya da ta yi gare ta saboda ilmin da ta

sanar da ita, Hakanan da wa}ar bankwana da ta yi mata

a lokacin da za ta yi hijira zuwa Makka.

A }arshen wannan littafi an kawo ratayen

wa}o}in Modibbo Kilo wa]anda suka zo cikin ajami

domin mai karatu ya }ara tabbatar da ayyukanta na

asali ba juye ko fassara ba.

1

Babi Na [aya

Salsala da Rayuwar Modibbo Kilo

Salsalar Modibbo Kilo

Modibbo Kilo ]iya ce ga Al}ali Mahmudu ]an

Muhammadu Ashura ]an Sheikh Mahmud Hafiz ]an

Musa Hafiz ]an Abubakar Amiru Barambo.

Mahaifin Modibbo Kilo, Al}ali Mahmudu,

Fulata-Borno ne, wanda ya taso daga Kukawa ta }asar

Misau, cikin }asar Borno, ya yi hijira zuwa }asar

Mujaddadi Shehu Usmanu [anfodiyo. Mahaifin

kakanta Muhammadu Ashura, shi ne Mahmud Hafiz,

shi kuma ]an’uwa ne ga Gwani Mukhtar wanda ya

kar~i tuta a hannun mujaddadi Shehu Usman

[anfodiyo kuma ‘ya’yansa da jikokinsa su ne suke

sarautar Sarkin Misau.

A lokacin da ya zo Sakkwato sai aka ]ibar masa

fili a garken Nana Asma’u, aka yanka masa wurin zama

a shiyar Gi]a]awa. Ya rasu ya bar ‘ya’ya tara. Matarsa

Aminatu, ta haifa masa Maryamu wadda ta tafi Makka

ta rasu a can da Shehu Usman (Muhtin Sakkwato) da

A’ishatu Kabo da autarta Saudatu (Modibbo Kilo).

Matarsa Safiya ce ta haifi babbar ‘yarsa Modibbo

Hadizatu da Modibbo Nana Asma’u da Modibbo

Hauwa Inna Garka. Sai matarsa Fa]imatu ]iyar Malam

Sa’idu ]an Bello, wadda ta haifi ]ansa Buhari Moyi,

shi ma ya yi muhtin Sakkwato. Sa]akarsa

Jimma }arama, ita ta haifi ‘yarsa Fa]imatu wadda ake

cewa Amiru ko Auta, da yake ita ce autar gida kuma ita

ka]ai mahaifiyarta ta haifa.

2

Mahaifin Modibbo Kilo, Al}ali Mahmudu, yana

da sauran sa]aku wa]anda ba su haihu da shi ba,

Jimma babba Batambala wato wadda ta fito daga

Tambuwal da Inna Ubai da Ayya, duka wa]annan

sa]aku Gobirawa ne.

Mahaifin nata babban malami ne wanda

Modibbo Kilo ta bayyana ta hanyar jero wasu

kalmomin siffatau na Larabci wa]anda ta siffanta shi

da su. Ta kira shi Al-alimu kabirun ta}iyyun al-Abidus salihul waliyyu, wato babban masani, mai tsoron Allah,

mai yawan ibada, salihi kuma waliyyi, a wa}arta mai

suna ‘{abli Da Ba’adi Cikin Salla’.

Sunan mahaifiyarta Aminatu, amma ana ce mata

Mamma, ]iyar liman Usman ]an Ahmadu ]an

Abubakar Ladan Rame. Al}ali Abubakar Ladan

Rame ]an kawun Shehu Usmanu [anfodiyo ne kuma

yana ]aya daga cikin mashahuran mutane wa]anda

suka yi hijira tare da Shehu. Ya zama al}ali a zamanin

Shehu. Kakan nata, Liman Usman shi ya zama liman na

farko a cikin zuri’ar Ladan Rame, sannan ya yi al}alin

Kware. [an’uwa ne ga al}ali Abdullahi wanda ya yi

hijira da Sarkin musulmi Attahiru ya kuma rubuta

Risala, a cikin ta ya yi bayani game da sha’anin zuwan

Nasara a shekarar 1903, a inda ya ba da za~i 3, hijira

ko ya}i ko sulhu, to shi sai ya za~i hijira kuma ya yi ta.

Haihuwar Modibbo Kilo

An haifi Modibbo Kilo wajajen shekarar 1901, a garin

Sakkwato, a shiyar Gi]a]awa a unguwar Takardawa

(bayan gidan marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan

Sakkwato). Dalilin kiran shiyyar Takardawa shi ne, don

ana na]a Magatakardan Sakkwato daga shiyar. Sunanta

na yanka Saudatu, amma an fi sanin ta da la}abin Kilo,

3

wanda aka yi mata saboda an haife ta a lokacin da

Sarkin Musulmi Abdurrahman ]an Atiku ya na]a

mahaifinta Al}ali.

Neman Ilminta

Tashin Modibbo Kilo ba ta son wasa sai karatu.

Modibbo Kilo ta fara karatu a hannun mahaifinta Al}ali

Mahmudu kuma gare shi ta yi saukar Al}ur’ani, tun

tana da Shekara kusan 7. Ta yi tushin wannan karatu

wajen malamarta Modibbo Fa]imatu wadda ake kira

‘Yar Dije ‘yar }asar [un]aye. Mahaifinta Al}ali

Mahmuda da Modibbo Fa]imatu sun ci gaba da

karantar da ita littattafan sani, irin su Usuluddini da

Ahlari da Ishmawi da Izziya da Risala da {ur]abi da

Lawwali da Sani da kuma Tafsiri. Ta ci gaba da

wannan karatu hannun yayanta malam Shehu Muhtin

Sakkwato da mijinta Sarkin Yamman Kware Abdullahi

Bayero, wanda ya ci gaba da karantar da ita bayan ta

aure shi. Ta yi karatu kuma a hannun malamarta

Modibbo Hauwa’u Mammange, yayar wani mashahurin

malami a Sakkwato Malam Bube da Modibbo Mo’e ta

{ofar-rini, ]iyar wani shahararren malami, malam

Akale (uban Mana wanda ya na}alci Mukhtasar, an ce

wanda duk bai karance ta gare shi ba a lokacin, kamar

bai karance ta yadda ya kamata ba saboda }warewarsa

game da ita). Ta sauke Ishiriniya a hannun yayanta

Shehu Muhti.

Ta mai da karatu babbar sana’arta wanda take yi

dare da rana, a koyaushe aka same ta ko dai tana ri}e da

littafi tana karatu ko tana karantarwa, domin ba ta fita

zuwa ko’ina idan ba da larura ba. Tana kuma da yawan

yin salla da tasbihi da sauran ibada.

4

Aure da Iyali

Da shekara 9 aka yi wa Modibbo Kilo aure. Ta auri

Sarkin Yamman Kware Abdullahi Bayero ]an mallam

Isa, autan mujaddadi Shehu Usmanu [anfodiyo. Tana

da abokan zama, uwargida Hajara da mai bi mata Aisha

Inna Kabo, ‘yar Sarkin Kabin Silame, sannan ita

Modibbo Kilo. Ta }ara samun ilmi sosai a hannun

wannan miji nata har ta zama tana karantarwa a gidansa.

Sun yi zaman lafiya kwarai da mijinta, amma daga

baya }addara ta sa suka rabu. (sanadi an ce ta yi wani

shisshigi ne na karatu, a lokacin da aka yi wa

maigidanta wata fatawa, bayan ya ba da nasa bayani sai

ta nuna akwai ]an gyara). Yin haka ga Modibbo Kilo

ba abin mamaki ba ne, saboda ]abi’a ce wadda ta samu

daga malamarta Modibbo Mammange wadda kan gyara

karatu daga cikin gida, ta hanyar ]aga murya, kamar

yadda ]alibinta Waziri Junaidu ya shaida wa ]ansa

malam Ibrahim Gandi.

Bayan rabuwar aurenta da Sarkin Yamma

Abdullahi Bayero, Modibbo ta ci gaba da koyar da

karatu ga }annenta da kuma ‘ya‘yan ‘yan’uwanta da

sauran ]alibai, daga baya ta auri malam Akwara na

shiyar ‘Yola a Sakkwato, malami kuma ]an kasuwa.

Kamar yadda aka ba da bayani an ce, shi ma aurenta ya

mutu da shi saboda al’amarin karatu, inda ta bu]a

murya a wani lokaci da take yin karatu, wanda mijin

nata bai so ba. Bayan sa ba ta sake wani aure ba.

Modibbo Kilo ba ta ta~a haihuwa ba har ta koma ga

mahaliccinta. Modibbo Kilo ta rasu a garin Makka a

shekarar 1976.

5

Ayyukan Modibbo Kilo

Kodayake Modibbo Kilo ta yi ]imbin ayyuka a

Sakkwato da Makka, musamman ~angaren karantarwa

da kuma rubuce-rubuce wa]anda da yawa ba su kawo

ga hannu ba, duk da hakanan na yi }o}arin binciko

ayyukanta, da su]in goshi na sami wa]ansu, wa]anda

na yi wa ta}aitattun nazari a wannan littafi.

Ayyukan da ta yi a Sakkwato

A Sakkwato, Modibbo Kilo ta fara karantarwa a gidan

mahaifinta a Unguwar Takardawa, a lokacin kuma da ta

koma gidanta da ta gada a Shazalawa sai ta mayar da

wannan makaranta tata can, ta kuma karantar a

Hubbaren Shehu Usmanu [anfodiyo. Ta karantar

da ]imbin mata addinin Musulunci har da maza

‘yan’uwanta da ‘ya’yansu wa]anda mahaifinta ke turo

mata don karatu da fatwa da kuma sauran maza masu

neman ilmi. Gidanta kodayaushe cike yake da mata har

da maza masu ]aukar karatu. Ta zama malamar tafsiri

wanda kafin ta fara a makarantarta ta Shazalawa sai da

ta fara jan ba}i ga Modibbo Hauwa’u Mammange a

Hubbaren Shehu. A Sakkwato ta yi rubuce rubuce da

suka danganci ilmi cikin zube da wa}a.

Cikin ]alibanta, akwai Al}ali Mamman ]an

yayanta da Al}ali Isah da Malam Garba da Malam

Ibrahim duk ‘ya‘yan Mallam Usman Muhti da Kande

Nufawa da Modibbo Khadijatu da Igen Laddo da Igen

Gwanfa da Igen [angara da Hafsatu ]iyar Amadu Aja

na kofar Atiku da iyalin wazirin Sakkwato, waziri

Abbas da sauran ]alibai masu yawa.

Akwai kuma mata wa]anda suke aminan

Modibbo Kilo, kamar babbar aminiyarta Fa]ima

mutuniyar {auran Namoda, matar Al}ali Sani wadda

6

suka yi musayar ilmi musamman ta hanyar rubutacciyar

wa}a. Akwai kuma Igen Sabon gida matar waziri

Macci]o. Modibbo Kilo tana da mai mata hidima

wadda ta sa a jikinta }warai da gaske mai suna

Maryamu wato Kurma. A kodayaushe tana tare da

Kurma, kuma kodayake ba ta ji, ita ce take yi mata

yawancin hidimomi. Tare da ita, Modibbo ta yi hijira

kuma har ta rasu a garin Makka.

Ayyukan da ta yi a Makka

Kafin a kawo bayanan irin ayyukan da ta yi a Makka,

zai yi kyau a ba da ta}aitaccen bayani na dalilin barin ta

Sakkwato, domin koma wa garin Makka wanda ta kira

hijira.

An ce ta fa]a wa wani daga cikin ‘yanuwanta

cewa za ta yi hijira zuwa Haramaini, da Sarkin

Musulmi Abubakar na 3 ya sami labari, sai ya ce a gaya

mata kada ta yi, saboda ana bukatar mutane masu ilmi

irin ta a cikin al’umma. Sai ta ce a fa]a masa, shi zai

hana ta yin hijira bayan Annabi (Sallallahu Alaihi wa

sallam) da kuma Mujaddadi Shehu Usmanu [anfodiyo

sun yi? Daga wannan lokaci sai Sarkin Musulmi ya ba

ta cikakken goyon baya, har ya ba ta guzuri na Fam

goma, ya sa aka yi mata Fasfo na shiga }asar Saudi

Arabia, ya kuma tura ta wajen Sarkin Kano domin ya

ha]a ta da ayari wato abokan tafiya. (Hirar da na yi da

zuri’ar gidansu ranar Talata 29/5/2012)

Kamar yadda Modibbo Kilo ta yi bayani a

wa}arta ta hijira da kuma bayanan da ‘yan’uwanta suka

yi mini, ta yi hijira zuwa Makka ne saboda wasu

abubuwa da ta fara gani na gur~acewar al’umma da

kuma abubuwan da take ji a jikinta da zuciyarta na

shau}in saduwa da Annabi Muhammad (Sallallahu

7

alaihi wa sallam). Idan mun lura, al’amarin hijira ga

Modibbo Kilo ba sabon abu ba ne domin mahaifinta ya

yi hijira daga Borno zuwa Sakkwato,

hakanan ]an’uwan kakanta ~angaren uwa, Al}ali

Abdullahi abin da ya za~i ya yi kenan bayan zuwan

Nasara Sakkwato, haka nan ‘yar’uwarta Maryamu ita

ma ta bar Sakkwato ta koma Makka, ]ada ko da niyyar

hijira koko da wata niyya ta daban.

A lokacin da Modibbo Kilo ta zauna a Makka ta

kafa makaranta a garin, a unguwar Jarwal a gidanta

wanda ke kan dutse cikin Hara al- Yemen. A

kodayaushe gidanta cike yake da ]alibai. Ta karantar da

Al}ur’ani da Hadisi da Fi}ihu da sauran fannonin

Musulunci. Tana tafsiri ga mata, ta hanyar amfani da

tafsirin Jalalaini musamman lokacin azumi. Tana

da ]imbin ]alibai masu cika ]akuna da tsakar gida na

gidanta domin ]aukar karatu. Koyaushe za a sami

Modibbo tana karatu ko karantarwa ko rubuce-rubuce,

tana kuma sha’anin Allah ba na duniya ba. [alibai

masu yawa sun sauke Al}ur’ani a hannunta, sun yi

karatun Tauhidi da Hadisi da Fi}ihu da sauransu.

Ta karantar da manyan malamai kamar babban

malamin nan na Sakkwato Sheikh Sidi Attahir Ibrahim

da Kadi Usman Gusau (Shi ne wanda ya gaji tafsirin

Islamic Education Trust wato IET a Sakkwato, daga

hannun marigayi sheikh Halliru Binji kuma ya zama

Khadi a Jihar Sakkwato). Wani malami Sheikh

Abdurrahman Usman Magrabi yana ]aya daga cikin

aminanta a Makka har yana turawa Modibbo matarsa

domin ta ]au karatu. A koyaushe za ta tafi sai ta je da

‘yar rakiya ]iyarsa mai suna Yumma. Koyaushe aka

karantar da matarsa, Yumma tana saurare, sai ta

hardace karatun, ta dawo gida tana yi. Ranar da

8

mahaifinta ya ji yawan karatun da ta ]auko, sai ya ce ta

yi satar karatu tun da ba ita ake karantarwa ba, ya ce ta

koma ta karanta wa Modibbo karatun da ta yi ta saurare,

ta nemi izni daga gare ta, ta kuma kai mata wata ‘yar

kyauta don karatun ya zama mai albarka. Haka ko aka

yi, daga baya Modibbo ta yi mata addu’a na Allah ya sa

wa karatun albarka.

An yi bayanin cewa a Makka Modibbo babbar

malama ce, wadda ba a zama da ita ba a }aru ba.

Saboda jama’a da ]imbin ‘yan makaranta da take da su,

duk lokacin da aka gan ta, za ta zama tare da

jama’a ]uu suna bin ta kamar Basarakiya. Idan tana

karanta wa}o}in bege kamar da ]ai cikin bakinta aka

halitta kalmominsu.

Yanayinta da Halayenta

Modibbo Kilo mutawassi]a ce, ita ba tsawo can ba, ba

kuma gajera ba, mai doguwar fuska ce da dogon wuya.

Ga kalar jikinta fara ce mai kyaun siffa. Yawancin

suturar da take sa wa ta dal}e ce mai kalar shu]i-shu]i,

tana ]inka babban zani har }asa, ta ]ora babban zani a

kanta bayan ta aza abin da ake kira ‘Tiggare’ wanda sai

mai ilmi, masani ka]ai ke amfani da shi.

Modibbo Kilo mai ]a’a ce ga iyaye da son

zumunci kwarai kuma mai fa]in gaskiya ce duk yadda

al’amari ya kasance. Ta}iyya ce mai tsoron

Allah }warai, mai kuma tsentseni ga duniya. Mai kunya

ce da kamun kai, idan kuma tana tafiya }asa-}asa take

duba ba ta son ]aga kai. Tana da yawan kyauta da

taimako, ko abu ya zama shi ka]ai ke gare ta, tana iya

ba da shi, tana kuma yawan aikawa mutane abinci da

sauran abubuwa da Allah Ya hore mata (Al}ali

Riskuwa ]a ga yayarta, ya gaya mini cewa har sai da ya

9

yi korar ]aukar kaya a kansa a lokacin, saboda shi

ne ]an aikenta wajen mutane). Duk da tana da yawan

sadaka da kyauta musamman na abinci, yawancin

mutanen da na tattauna da su sun ce da wuya a ga

lokacin da take cin abinci. Modibbo mai fa]in gaskiya

ce, kuma tun tana yarinya koda ita ta yi laifi ha}i}a za

ta fa]i ita ta aikata shi, saboda fa]in gaskiyarta, duk

‘yan’uwa da abokanta sun san cewa idan ba a son a

bayyana wata rashin gaskiya to kada a yi a gaban ta.

An yi bayanin cewa Modibbo Kilo mai tsaya wa

kanta ce, kuma ba ta son haram ba ta cin sa. Dalilin

haka ne aka ce da ita da jama’arta mata har gini suke yi

a gidanta, su yi ha}on rami su kwa~a laka su yi gini da

kan su. Hakanan suna noma, su yi ‘yan shuke-shuke

domin amfanin gida. Mutane sukan zolayi mai mata

hidima Kurma, su ce, ‚ku mahaukata ne, ku yi noma da

gini da kanku?‛ Sai ta ce ‚Moo-moo di dib-bo, ta-ta ce-

-- mu-mu yi --- ko--- mai ci-ci-ci kin ha-ha laaa lin mu‛,

wato Modibbo ta ce, komai su yi cikin halalinsu.

Kwarjini da Karamar Modibbo Kilo

Modibbo Kilo muzakkarar mace ce kamila, mai

kwarjini da haiba ga mutane. An yi bayanin shakkar ta

da maza da mata ke yi, duk wanda ya tunkare ta tilas ya

shiga taitayinsa, wanda bai da natsuwa da kamala bai

iya matsawa kusa da ita, wanda ba shi da imani ba zai

iya tsayawa gabanta ya da]e ba. Ba ta da fa]a amma

tsayayyiya ce wadda ba wasa a al’amarinta. Mutane

suna }aunar ta da son ganin ta, domin idan ta fito sai

mutane su yi caa a kan ta suna cincirindo a kan ta suna

bin ta kamar Sarki ya fito. Ranar da ta yi hijira ta bar

Sakkwato, sai da aka sa wa mutane kewar tafiyarta,

yawancin mata har da maza sai da suka yi yakkwat,

10

wato zugum suna begen ta. (Hira da na yi da Modibbo

Fa]ima Sarauniya ]iyar Abdurrahman Sarkin Gobir na

Gwadabawa kuma mahaifiyar Dr Omar Bello ranar

20/6/2012 a lokacin tana da shekara fiye da casa’in

duniya). Irin wannan bayani na samu ranar Jumu’a

22/6/2012 daga Safiyyah Ni’imat Harun wadda ta san

Modibbo Kilo a garin Makka a lokacin ita Ni’imat

tana }arama).

Malama Rugayya wadda ta rayu da Modibbo

Kilo a garin Makka ta ba ni wani labari cewa wata rana

cikin azumi da daddare, makarantar Modibbo ta cika da

masu sauraren tafsirinta, sai ta fita tsakar gida kamar za

ta yi wani abu, tana dawowa sai ta ce kowa ya tashi ya

yi gida wajen ibada saboda Lailatul }adri ta bayyana.

Har manyan malamai na Makka na kusa da ita babu

wanda bai yarda da maganarta ba saboda an san ba

ta }arya, sai ta hau ibada hakanan sauran jama’a. (Hira

da malama Rugayya ranar Jumu’a 22/6/2012). A

lokacin da Modibbo Kilo ta fa]o daga jirgi a hanyarta

ta hijira lokacin ratsawarta zuwa Khartoum, har ana

zaton ta suma ko ta rasu, maimakon haka sai ta bayyana

cewa, a lokacin babu abin da ta gani sai Annabi

Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) a gaban ta.

Wasiyya da Rasuwar Modibbo Kilo Wasiyyar Modibbo Kilo

Shekara goma sha ]aya, kafin Modibbo Kilo ta koma

ga Ubangijinta, ta rubuta wata wasiya akan wa}afin

gida wanda ta yi, saboda Allah da ManzonSa. Na sami

wannan wasiya wadda ta rubuta cikin harshen Larabci,

wadda na fassara zuwa harshen Hausa kamar haka:

Bismillahi wal hamdu lillahi wa kafa, was

salamu alal Mus]afa.

11

Bayan haka, wannan wasiyya ce ta Modibbo Kilo

‘yar Al}ali Mahmudu Sakkwato, a lokacin tana da

shekara sittin da hu]u da wata shida. (Na rubuta

wasiyar) ranar Alhamis sha biyu ga watan Jumada

Akhir, shekara ta dubu ]aya da ]ari uku da tamanin da

biyar (1385) Hijiriya, daidai da bakwai ga watan

October, shekara ta dubu ]aya da ]ari tara da sittin da

biyar (1965) Miladiya, daidai da shekara ta dubu ]aya

da ]ari uku da arba’in da biyar, Shamsiyyah (1345).

Bayan haka, na shaida babu Sarki sai Allah,

kuma na shaida Muhammadu manzonSa ne, tsira da

aminci su tabbata a gare shi. Bayan haka, ‚Yaku

‘yan’uwana, wa]anda suka yi imani da Allah da

ManzonSa, saboda haka, na yi muku wasiya a nan cikin

gidana, na kasance da raina da lafiyata da kuma bayan

rasuwata, a cikin wasu kalamai, wa]anda zan ambace

su nan gaba. Ni na sanya amanata ga Allah,

ma]aukakin Sarki, ku dube ni da niyyata zuwa ga Allah

da ManzonSa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare

shi, kuma bayan su, na sa wasiya ga iyalina, na ba su ita,

godiya ta tabbata ga Allah da salati ga manzonSa.

Amanar Allah da ManzonSa ta kasance a wurin ku, Ya

ku wa]anda ake kira, daga ciki akwai Idris Ibrahim

Daura tare da mataimakinsa, da taimakon Allah da

manzonSa, ]ana Muhammadu Ahmadu a sashen }asar

Sakkwato, garin da ake kira Dange, }asar Sarkin

Musulmi wanda ake yi wa la}abin [an-farin, wa]anda

na ba wa amanata bayan rasuwata. Wa]annan mutune

biyu, su za su gudanar da al-amuran wasiyyata, sai

kuma wa]anda suka taimaka musu cikin mahalarta, ina

fatan Allah Ya sa su kasance kamar yadda nake musu

kyakkyawan zaton su kasance. Ina fata Allah Ya kiyaye

su sharrin }addarori, Ya }arfafa su da taimakonSa, Ya

12

yi musu taimako da }arfin ikonSa, har su samu damar

cika alkawarinsu game da zancena. Allah Ya sa ni

Aljanna Firdausi, ni da su da kuma dukkan musulmi.

Amin.

Wannan wasiyya ce zuwa ga mutane daban-

daban kamar, Torankawa da Fulani da Hausawa,

dukkaninsu wa]anda suka yi imani da Allah.

Wallahi tallahi, ku sani ban mallaki komai ba a

cikin wannan duniya, in ba son Allah da ManzonSa da

imani a zuciya ba. Don Allah ga ]alibata Maryam,

wadda ke cikin gidana na Makka, idan Allah Ya kar~i

rayuwata, na bar wa Maryam ha}}ina, kuma kada

kowa ya fitar da ita da wa]anda ke tare da ita daga

gidana har abada. Hakanan ta yi yadda take so da

gidana, ta zauna, ta kuma amshi ku]in haya har sai ta

rasu. Bayan rasuwarta, wannan gidan, ya zama wa}afi

ga Allah da ManzonSa (ta fa]i haka har sau uku).

Amma abinda ya ke~anta gare ni, to zuri’ata su gaje ni.

[alibaina ba}i wa]anda suka fito daga Sakkwato

da sauran garuruwanmu zuwa aikin Hajji a Makka, idan

sun so, to su zauna a gidan har lokacin da suka tashi

komawa gida, ko su zauna har abada da shara]in gyara

gidan da zaman }warai, amma su sani wannan ba

gidan gado ba ne, ba na sayarwa ba ne, ba na haya ba

ne har abada, (ta fa]i haka har sau uku).

Sannan kuma ku sani, duk kayayyakina, da aka

isko a cikin gidana masu amfani, duk da kayan shayina

da makamancinsa, ban yarda kowa ya fitar da su daga

gidana ba har abada, duk wanda ya yi yaji, ya fitar da

wani abu daga ciki, to za mu yi husuma da shi gaban

Allah ranar al}iyama.

Ya ku Muminai da suka halarci jana’izata cikin

yardar Allah, ban yarda a fitar da wani abu na kayana

13

wajen gidana ba, da nufin yin amfani da su a waje ba,

domin wannan gida da kayan da ke cikinsa wa}afi ne

ga Allah da ManzonSa. Hakanan littafaina da takarduna

na musamman, wa]anda ke cikin gidana, duk wanda ya

le}o su, ko ya yi aiki da su, ban yafe masa ba duniya

da lahira, sai wanda na sauwa}a wa idan dai har an

same su a cikin gidana bayan rasuwata, idan kuma ba

haka ba ne, to babu ruwana.

Ina sake maimaita cewa, gidan nan wa}afi ne

don zuri’ata da jama’ata da ]alibaina wa]anda suka

sadu da ni wajen harkar ilmi suna matsayin ba}i. Don

haka gidan, ba gidan gado bane, ba na sayarwa ba ne,

ba na haya ba ne, sai mazauna gidan masu gyaran sa.

Ya ku Muminai, duk wanda ya sa~a wa wannan

wasiyyar da na rubuta da hannuna, ko ya canza ta, da

cewa yana gado na alhali ba ya gado na, to ya sani,

cewa ro}on Allah da na yi, da alfarmar mafificin talikai

Muhammadur Rasulullahi sallallahu alaihi wa sallam,

Ya fi }arfinsa, sannan Ya gaggauta musiba gare shi, tun

a nan duniya, kuma ta bi shi har lahira. Ha}i}a

Ubangiji mai ji ne, mai kuma kar~ar addu’a ne, da

alfarmar shugaban mutane da aljannu.

Wannan gidan da na rubuta wasiyya a kansa,

matsayin wa}afi ga Allah da manzonSa, na saye shi

yana fili, babu komai a cikin sa. Sayen filin ya kasance

ta wasi]ar Shehu Ali ]an Ibrahim, Sarkin Hausawa na

Jarwal, da kimanin ku]i, wa]anda mi}idarinsu ya kai,

Liyar ]ari shida, ku]i hannu, a gidansa, a gaban shaidu.

Filin dutse ne zalla, mai da]in zama, wanda ke saman

duwatsu. Na shiga gyaran gidan tsawon shekara goma,

ba tare da tsayawa ba, kuma babu wanda ya taimaka

mini, sai Allah da ManzonSa. Duk wanda ya san ni, ya

san wahalar da na yi na samun gida a garin Makka, tun

14

daga ranar da aka ]ora mini nauyin biyan ku]i jaka

dubu ashirin, tarifan giris.

Ga sunayen shaiduna a kan wasiyyar wa}afin

gidana, su na ]ora wa nauyi bayan rasuwata, kuma sune

farkon shaidu a garina Sakkwato cikin Nijeriya, bayan

na sa Allah da manzonSa shaidu.

1. Sarkin Musulmi Abubakar ]an Usmanu ]an

Mu’azu, ]an Muhammadu Bello ]an mujaddadi

Usmanu hasken zamani, mai Sakkwato Bubakar.

2. Sai Muhammadul Bukhari wanda ake yi wa

la}abi da malam Moyi, muhtin Sakkwato,

muhtin mahaifina, ]an Al}ali Shehu Mahmudu

]an Muhammadu, wanda ake yi wa la}abi da

malam Ashura, malami mai tsoron Allah, ]an

Gwani Mukhtari, uban gari, ]an malam Musa

Gwani burmama, uban mai mela, Mahmudu

Gwani da mai Gazargamu.

3. Sai Abubakar Atiku wato malam Garba mai

albarka, In sha Allahu, ]an sha}i}ina malam

Shehu Muhti mai rahama.

4. Sai Yusufu ]an Ubandoma. Dukkansu wa]anda

ke zaune a tsakiyar Sakkwato.

5. Sai Aliyu ]an Umar, hakimin Kora-gishiri, a

garin Gwandu.

6. Sai Iliyasu na Wurno a Magaryawa.

7. Sai Aliyu Hargagi na Sambu-darni a Masfala.

8. Sai Shehu Ali.

9. Sai makwabcinaUmar ]an Muhammadu

Bafulatani.

10. Sai Muhamman Lago Misau a Hartal Fo.

A kai wa Bukhari (wannan wasiya), shi gani, shi sani,

in ya lura da batuna, shi ba Atiku ajiya, shi ma shi lura

15

don takan zo ta komo. Ni ba a cuta ta kuma ni ba na

cutarwa In sha Allahu Bukhari da Atiku am. Alhamdu

lillahi. Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai.

Mai wannan wasiya kuma marubuciyarta da

hannunta, ita ce Modibbo Kilo ]iyar Al}ali Mahmudu

Sakkwato Babarambe.

Rasuwar Modibbo Kilo

Ban sami dalilin rasuwar Modibbo Kilo ba, sai dai

lokacin da ta rasu. Modibbo Kilo ta rasu a garin Makka

a shekara ta dubu ]aya da ]ari tara da saba’in da shida

1976 Miladiya.

16

17

Babi Na Biyu

Rubutattun Waqoqin Modibbo Kilo

A wannan babi za a kawo rubutattun wa}o}in Modibbo

Kilo, wa]anda suka samu a hannu, wa]anda kuma na

yi }o}ari na juya daga Hausar ajami zuwa Hausar boko.

Hakanan a wannan babi, na kawo gajerun bayanai game

da wa}o}in, saboda su zama shimfi]a da jagora ga mai

karatu, domin ya gane sa}on da ke cikin wa}o}in. An

bi tsari na gabatar da bayanan wa}o}in kafin a kawo su,

saboda samun sau}i da da]in shiga cikinsu. Da fatan

wannan hanya za ta gamsar da mai karatu.

Nazarin Wa}ar Hijirar Modibbo Kilo da Zamanta a

Makka

A wannan nazari na hijira da zaman Modibbo Kilo a

Makka, za a bi wa}ar da ta rubuta domin a kawo

muhimman abubuwa da suka danganci sa}o ko jigon da

ta bayyana a wa}ar, kamar tashin ta daga Sakkwato da

hanyoyin da ta bi har isar ta garin Makka da abubuwan

da suka faru a kowane mataki da abubuwan da ta ha]u

da su kan hanyarta da kuma ]an bayani game da

rayuwar da ta yi a }asar Saudi Arabia.

Duk da cewa jigon wannan wa}a ka]ai za a ta~a

wajen nazari, a gurguje za a fara da kawo dalilin da ya

sa Modibbo Kilo ta yi hijira, saboda fahimtar sa}on da

ke ]auke a cikin wa}ar.

18

Dalilan Yin Hijirarta

A wannan wa}a Modibbo Kilo ta kawo dalilin da ya sa

ta yi hijira da yadda take ji game da hijirar. An ce ta

fa]a wa wani daga cikin ‘yanuwanta Shehu muhti cewa

za ta yi hijira zuwa Haramaini saboda wasu abubuwa da

ta fara gani na gur~acewar al’umma da kuma abubuwan

da take ji a jikinta da zuciyarta da shau}in da take yi na

saduwa da Annabi Muhammad (Sallallahu alaihi wa

sallam). Sarkin Musulmi Abubakar na 3 ya sami labarin

hijirar, sai ya ce a gaya mata kada ta yi, saboda ana

bukatar mutane masu ilmi irin ta a cikin al’umma. Sai

ta ce a fa]a masa shi zai hana ta yin hijira bayan

Annabi (Sallallahu alaihi wa sallam) da kuma

Mujaddadi Shehu Usmanu [anfodiyo sun yi? Daga

wannan lokaci ne, Sarkin Musulmi ya ba ta cikakken

goyon baya, har ya ba ta guzuri, ya sa aka yi mata Fasfo

na shiga }asar Saudi Arabia, ya kuma tura ta wajen

Sarkin Kano domin ya ha]a ta da ayari wato abokan

tafiya. (Hira da zuri’ar Al}ali Mahmudu ranar

29/5/2012).

A baiti na 44 zuwa 53 Modibbo Kilo ta kawo

bayanan abubuwan da take ji da yadda ta kasance

domin yin wannan hijira, ga wasu daga cikin su kamar

haka. Ta kwatanta kanta da cewa a wannan lokaci ta

koma kamar dabba wadda Zaki ya koro ta fito aguje, ko

Tumaki wa]anda Kura ta koro. Ta zama kamar

majnuniya (marar hankali) saboda haukan son ta zo

haramaini.

19

Tamka gudanowa ta dabba nif fito,

Nan inda Zaki, za ni na Haramaini.

Tamka gudanowat Tumaki nif fito,

Nan kau ga Kuraye zuwa Haramaini.

Tamka jununi niz zamo fa jama’ata,

Sa’af fitowata zuwa Haramaini.

Ta bayyana cewa Allah Sarki Shi ya sa mata son

wannan al’amari a cikin zuciyarta. Ta nuna cewa abin

da take ji (na sirrin zuci) ka]an ta fa]a. Ta ci gaba da

bayanin cewa, ga abin da ta ji Rasulullahi (Sallallahu

alaihi wa sallam) yana ce mata,

Ni dai Rasulullahi yac ce Saudatu,

Taso fito maza zo cikin Haramaini.

Dalilin haka ya sa ta tashi a gigice ba ta ganin kowa sai

bi]ar tafiya. Ta dai ci gaba da fa]ar zillar da take ciki

na wannan tunani kamar dai wadda aka ]aure aka

tuntsire cikin wahala, ta ce hankalinta gaba]aya ya fita

daga kanta, tana tunani da waswasi na yin wannan

hijira ba don komai ba sai don Annabi (Sallallahu alaihi

wa sallam) ya yi tsayin daka a kanta, yana umartar ta da

ta fito zuwa haramaini,

Don Ya Rasulullahi yay yi tsayin daka,

Yac ce fito fa fito zuwaHaramaini.

A wannan lokaci ta yi zaton cewa mutuwa za ta yi

kuma kabarinta na gaba, don haka ba ta yi tsammani za

20

ta ma isa garin Makka ba, amma saboda tauhidi da

imaninta sai ta ci gaba da shiri da tafiya, da sanin Allah

shi ne mai taimakon wanda ya yi imani da Shi.

Idan mun lura, al’amarin hijira ga Modibbo Kilo

ba sabon abu ba ne domin duka a ~angarenta na uwa da

uba an sami wanda ya yi hijira, ~angarenta na wajen

mahaifi daga Borno zuwa Sakkwato kuma ~angaren

mahaifiyarta aka sami ]an’uwan kakanta Al}ali

Abdullahi abin da ya za~i ya yi kenan bayan zuwan

Annasara.

Jigon wa}ar

A nazarin jigo na tafiya ko hijirar Modibbo Kilo, za a bi

wa}ar da ta rubuta game da hijirarta tiryan-tiryan

domin a kawo muhimman abubuwa da suka danganci

sa}o ko jigon hijirar da ta bayyana a wa}ar, tun daga

tashin ta daga Sakkwato zuwa hanyoyin da ta bi har isar

ta garin Makka da kuma abubuwan da suka faru a

kowane mataki.

Kafin haka, duk da cewa jigon wannan wa}a

ka]ai za a ta~a, a gurguje za a fara da gajeruwar

shimfi]a game da yadda Modibbo ta shimfi]a wa}ar,

yin haka zai ba wa masu karatu sanin yanayin wa}ar da

yawan ta. Ga abin da na samu na wa}ar, ta }unshi baiti

fiye da 550, ta kuma zo a tsarin }war biyu ko ’yar

tagwai. Tana da }afiya na ‘ii’ a kowace ga~ar }arshe

ta ]angon }arshe na kowane baiti, kuma mafi yawancin

kalmar da aka yi amfani aka fitar da }afiyar ita ce

kalmar ‘Haramaini’. An rubuta wa}ar gaba]ayanta

cikin karin harshe na Sakkwatanci. Wa}ar tana da

wuyar bi saboda yawan baitocinta da cunkoson

abubuwa da ke }unshe a cikin ta, sai dai bin hanya

21

daki-daki da aka yi wajen bayyana sa}on ya taimaka

wajen fahimtar ta.

Domin warware jigon hijirar tata, Modibbo Kilo

ta kawo hanyoyin da ta bi cikin garuruwa na }asashe da

abubuwan da suka faru da ita tun daga Sakkwato har

zuwa Makka. A baiti na 3 ne ta fara furta jigon wannan

wa}a da kanta tana cewa,

Ni za ni lissafin fita das Sakkwato

Har rash shigowata garin Haramaini.

A {asar Nijeriya Fita daga Sakkwato-

Modibbo ta fita daga Sakkwato ranar Lahadi 12 ga

watan Rajab da hantsi. Fitarta ya sa masoya kuka kuma

ta kwatanta damuwarsu da damuwar musulmi lokacin

da Annabi (Sallallahu alaihi wa sallam) ya fita daga

Makka zuwa Madina (domin hijira). Abubuwan da suka

faru kafin fitar ta sune, ta yi bayanin cewa Sarkin

Musulmi Abubakar na 3 ya yi mata Fasfo, kuma ya ba

ta guzurin fam 10, ya kuma rubuta takarda ga Sarkin

Kano domin ya samar mata abokan tafiya. Ta wuce

zuwa Gusau.

Gusau-

Modibbo Kilo ta sauka a garin Gusau ranar Lahadi da

azahar, ta kwana 3 a gidan wani [an’ambo, jikan

Buharin Tambuwal.

Na sabka nan fa gari na ]an Ashafare ji,

Sambo waliyyi na zuwan haramaini.

22

Da’ azzuhur nik kwana ukku ha}i}a ni,

Wallai gidan [an’ambo na na uwar gari.

Wata da ake cewa Nana ta yi mata alheri, ta ba ta Sule

10 da kwanoni ta kuma yi mata zance mai sanyi. Ta so

zuwa {auran Namoda domin ta yi wa wasu mutane

bankwana, kamar Yugudu da Habsatu da Fatume da

Halimatu da Maryamu da Asma’u da Kande da Buhari.

Da alamu kuma ta so ta je wajen wata ]iyar Sarkin

Gusau Murtada wadda ta kira Fa]ima] ]an Sambo,

wadda ta ce Allah ya ba ta karama goma sha, sauran ta

guda ta zo haramaini da sauran mutane da ta ambata. Ta

kwana uku a Gusau tana shawarwari amma ba ta sami

zuwa {aurar Namoda ba.

Hakanan ta so ta ziyarci wasu waliyyai, misali

Mamman Tukur ]an Binta (na Matuzgi a }asar

Zamfara) da Abubakar Atiku a Katuru amma lokaci ya

tafi, Allah bai nufe ta da zuwa ba. Har yanzu dai a

Gusau ta iske ]an Sarkin Galma, Umar ]an

Hammada ]an Maunuma, }anwar Shehu Usmanu

[anfodiyo wanda ya zo yana rawar jiki da ita, ya ba ta

Sule 5. A Gusau dai ta sadu da ]alibin mahaifinta [am

Marafa da Malam na Kor]on. Abdun Tanin shi ne ya

yi ]awainiya da ita ya kuma yi }o}ari wajen shigar da

ita jirgi.

Ya yi }o}ari ranash shiga jirgi garan

Ga cikin Gusau rannan fa ya yi wahalhali

Abdun Tanin da masoyi Rabbi Ubangiji

Allah ka saka mai fa dunya lahiri

Ta tashi zuwa Zari’a ranar Laraba.

23

Zariya:

Modibbo Kilo ta isa Tudun Wadar Zari’a ranar Jumu’a

wurin wani da ta kira [anKilo jikan Bara’u da waziri

Buhari, jikan Ahmadu ]an Nana Asma’u wanda ya

tarbo ta.1 Ya ba ta shimfi]u da abinci da abin sha, ta

yabe shi da cewa ya yi gadon yin ayyukan alheri daga

kakanninsa zuri’ar Nana Asma’u.

Ga dare na Jum’a nif fa sabka Tudunwada,

Nan inda [anKilo ai ]iyaf fa Bara’u shi,

Ta baro Zari’a ranar Jumu’a da hantsi.

Kano :

Domin warwarwe jigon tafiyarta Modibbo Kilo ta ci

gaba da bayanin gidan Sarkin Kano inda ta yada zango

kamar haka:–

Gidan Sarkin Kano babban gida ne sai ka ce gari,

mai }ofa 4 kamar }ofofin gari. Sunan }ofar kudu

Sakkwato, saboda nan Maryam ]iyar Shehu Usmanu

[anfodiyo ta zauna lokacin da ta auri Sarkin Kano

Ibrahim Dabo. {ofar Arewa kuwa wurin gonakin Sarki

ne inda ake cewa Shekara. {ofar gabas sunanta Yakasai,

shiyar dukkanin ‘ya’yan Sarki mata. {ofar Yamma

sunanta Garko, shiyar sa]aku. Ta yi bayanin cewa

Sarkin Kano yana da mata 4 da bayi wajan 100 da uwar

soronsa Mowa da jakadiya 9 da ‘Yan soronsa 12. Ta ce

ana ba da akushi 700 na abinci kullum safe da yamma.

Modibbo Kilo ta yaba halayen mutanen Kano, tana

cewa halinsu kamar na ‘yan Aljanna, don haka ta ce

1 Tana nufin marigayi ]an Galadiman wazirin Sakkwato Alhaji (Dr)

Bello Gi]a]awa).

24

ha}i}a Allah Ya amsa wa Kanawa ro}on da Shehu

Usman [anfodiyo da Sheikh al Magili suka yi musu.

Ga baiti na 92 da 97 cikin baitocin da ta kawo wannan

bayani:

Akushi ]ari fa bakwai da safe da hantsi dut

Hakanan dare aka yin su don ]ai lahiri.

Kai na ga halin nasu tamka jannata,

Ga zuwa misali nig gudo haramaini.

Modibbo ta isa Kano cikin wannan gida da asuba ranar

Assabar kuma kwananta 52 a garin . Ta ambaci wanda

ta ce ]anta ne Abashe (Abbas) jikan Maje Ringim. Ta

bayyana cewa shi malami ne, adili mai fara’a wanda ya

gaji kakarsa (wato jikan ‘yar’uwar Husaina ce ]iyar

Sarkin Kano Ibrahim Dabo wadda ta auri Isan

Kware ]an Mujaddadi Shehu Usmanu [anfodiyo ).

Alheran da aka yi mata a Kano suna da yawa. Kullum

ana kai mata dangin abinci da abin sha goma sha da

‘ya’yan itace daban-daban da tufafi nau’i- nau’i da ku]i

da goro mai yawa. Kowace Jumu’a kuma ana kawo

mata Sule 20 da goro 100, su kuma wata Umma a ba su

goro 50 da Sule 10 saboda addini, wato domin girmama

ranar Jumu’a.

A Kano Modibbo ta karantar da taron ‘ya’yan

Sarki. Modibbo ta yi bayanin wasu daga cikin ]alibanta

tana yaba wata Aisha, saboda ba ta da fasicci ko ha’inci

ko zamba ko kissa, kuma tana da ]a’a wajen neman

ilmin Al}ur’ani sai dai wawiya ce. Ta kuma ambaci

wata mata Yagudu mai }aunar ta, wadda kullum take

kuka da ba}in cikin za su rabu ranar da Modibbo za ta

tashi tafiya, hakanan saboda ilmin da take ba su, har tai

25

musu addu’ar su ma su sami zuwa Makka. Sai Binta

wadda ta ce ita duk aka bar wa wauta ta Fillani, amma

ba ta da kissa wurin karatu.

Taron ]iyan Sarki Maje Lakwaja Alu,

Sun taru nana garan bi]a kau ilmi.

Da wa]ansu ‘yan sarki galadiman Kano.

-------------------------------------------

Sarkin Kano (Abdullahi Bayero) ya sallame ta, ya ba ta

Fam 10 kamar yadda Sarkin Musulmi Abubakar na 3 ya

ba ta. Wa]annan ‘yan Sarki sun yi mata rakiya zuwa

zangon da za ta tashi zuwa Makka a unguwar Warure ta

Kano, suna kuka ita ma tana yi, suka yi bankwana.

Amma ita Yagudu sai da ta yi kwana 3 tare da ita a

Warure kafin su tashi. Kullum ana aiko musu ci da sha

da ku]i daga gidan Sarki. Wasu sun raka ta har garin

Ringim.

Nit tashi sarkin kau Kano yas sallaman,

Yab ba ni fam goma kamat na ubangari.

Ta bar Kano ranar Laraba, 12 ga watan Ramadan, kuma

Sarkin Kano ya ba da umarnin cewa a cikin masu tafiya,

Bagunbora da Bukhari da Fatume da Kande su dakata a

Farlomi, amma ya ce ita Modibbo da abokan tafiyarta

Habsatu da Maryamu Kurma, su wuce sannan Kurma ta

zama mai hidimar su. Hafsatu ta yi sababi da fushi

amma Modibbo ba ta fa]i dalilin da ya sa ta yi haka ba.

Ayarin mutane 40 sun taso daga Kano.

26

Ringim zuwa Guru: - Sun shige wa]annan garuruwa

cikin bazara kuma cikin watan Ramadan.

Yarwa ({asar Borno):– sun shige ta da tsakar dare,

suka kwana 4 a cikin ta.

{asar Chad

Farlomi:- wato Port Lome cikin Chad, sun kwana 2 sun

wuce.

Atiya:- sun shiga garin Atiya da magriba amma sun bar

wurin da tsakar dare saboda ~arayi, sun yi tafiya rabi

da }afa rabi cikin mota, suna cikin zillar tafiya.

Wadai:- Sun shiga garin da hantsi yinin Lahadi, sun

kwana ]aya a nan, suka sha ruwa lokacin Ramadan, sun

bar nan ran Litinin da azahar.

Adire: - Sun shiga Adire }asar Faranshi wadda take

iyaka ta }asar Chad da Sudan, kuma daga ita sai garin

Jinaina inda ta kira mugun wuri. {asar akwai kafirai,

sun yi gudu da }afa cikin }aya da itace da ruwa da gebe

da dutse.

A {asar Sudan

Jinaina:- sun shiga garin da duhun asuba, saboda

wahalar da suka sha sai rarrafe suke yi a zaune, tilas

suka kwana 14 saboda a lokacin ana cikin ruwan malka.

Tsakar Daji:- kwanansu 25 cikin tsakar daji ba sa ganin

komai sai Zakoki.

27

Niyala – Ta kira wannan gari da sunan Garin Alidinar :

- sun kwana 5 a wannan gari. Ta yi bayanin cewa shi

Alidinar yana da halayya irin na kafirai.

Nihut: –Sun wuce wannan gari zuwa Ubayyid.

Ubayyid:- Garin yana cikin ~angaren Kurdufan -

kwanansu 5 a cikin sa.

Madani:- Shi ne babban birnin Sudan kafin a canza

zuwa Khartoum. Sun yi awa shida cikin Madani sai

jirgi ya iso suka kwana suna tafiya.

Khartoum:- sun shiga jirgi zuwa Khartoum. Jirgi ya

tsaya, mata su 7 sun sauka su yi salla. Kowa ya dawo

an shiga jirgi za a tashi ashe abokiyar tafiyar Modibbo,

Habsatu tana daji. Ita kuma Modibbo Kilo tana ri}e

da }arfen jirgi tana duban Habsatu tana tsaurin kai, da

alamu tana da}ila, tana ta}ama har jirgi ya fara tashi.

Bayan haka sai Modibbo ta sunkuyo (tana dubin yadda

za a bar Habsatu) saboda amanar suna tare da ita. Sai ta

zaburo da }arfi sai ta fa]o }asa, a nan ne ta ce ta ga

Annabi (Sallallahu Alaihi wa sallam) ya yi tsaye gare ta.

Ta fa]i rairan tana makyarkyata, sauran ayari suna kuka

sun yi zaton jirgin ya kashe ta. An bar ta tare da

Habsatu cikin ba}in daji tun assalatu har azahar suna

tafiya, }afafunsu sun sassar}e suna jin su kamar cikin

sar}o}I, sai suka iso wata kasuwa ta }auyawa. Sun yi

tafiya da }afa har }afafunsu suka kumbure. Sun ishe

abokiyar tafiyarsu Maryam, hankalinta a tashe, tana

zullumin ‘yanuwan tafiya, babu ci babu sha, sai kuka da

28

hargowa ana rarrashin ta. Tana zaune zugum shiru cikin

jirgi, ganin su sai ta yi mamakin isowar su.

Umdurman:- Sun iso wannan gari 2 ga watan layya

(Zul Hijjah). Ta zauna a Umdurman da ita da Umma da

Maryamu, amma madugunsu na tafiya shi ya wuce

Haramaini. Su 37 ne masu niyyar tafiya. Ta zauna a

garin wata 3. Ta bar Umdurman 23 ga watan Safar.

Mahattabarta:- Ita ce tashar jirgin }asa ta Umdurman.

Ta iso wannan tasha inda ta manta da akwatinta da

littattafai. Anan an kar~i Fam 65 gare su su uku, sannan

don cin amana aka kar~i wasu Fam 40 ku]in jirgin

Bida’a wato jirgin kaya da za su shiga. Sun wuce zuwa

Jidda.

Jidda:- Sun tashi zuwa Jidda su 40, amma su 4 kawai ne

musulmi, saura kuwa Nasara, sai dai ba su sami matsala

ba domin an kula da su.

Maliya:- Ranar Alhamis 20 ga watan Rabi’ul (Awwal

ko Sani?) suka shiga Maliya. Kyaftin Mucco shi aka ba

wa kula da su, don ya shige da su Jidda, shi kuma ya

kai su gun Gunsur, amma wani bature ya hana su shiga,

ya ce an yanke layi daga kan su, don haka ba a iya

wucewa Jidda. Sun kwana 3 tare da Kyaftin Mucco ba

su sami wucewa ba, sai Modibbo ta du}ufa ta yi ta

addu’a, cikin addu’oin har ta karanta Suratu Yasin }afa

41. Daga nan Kyaftin Mucco ya yi ta yawo da su cikin

maliya har suka kusa isa }asar Hindu (Indiya), kwana

15 suna tafiya kan ruwa bisa Maliya, har tana cewa yin

haka ya sa ta sami albarkar Annabi Yunus da Musa da

Haliru da Zul}arnaini (wa]anda suka yi al’amura cikin

29

ruwa). Duk da cewa wani kyaftin Rasdan ya ce shi

Istanbul ya yi, kyaftin Mucco ya ba shi fam 20 domin

ya mayar da su Sudan. Sun sake dawowa Sudan ranar

Jumu’a 5 ga watan Rabi’ul akhir.

A wannan tafiya cikin maliya ta ga abubuwan al’ajabi

misali yadda ta ga (inuwar) rana da wata zaune ga

Maliya, da }aton Kifi kamar Dorina da manyan Kwa]i

kamar girman ]aki da Tsutsa kamar girman Kifi.

Sannan ta ga duwatsu daban-daban wa]anda ta yi

bayanin su tana cewa. Ta ga wani dutse mai suna Sinfil

wanda ta ce aljani ya yi magana da ibranci ga Annabi

(Sallallahu alaihi wa sallam) da wani mai kamar saniya

da mai kama da ]aki mai murfi da kuma al}aryoyi

daban-dabam, kamar al}aryar Bilkis da al}aryar

Tururuwa da ta Najjashi wanda ya kar~i sahabbai

lokacin hijirar farko a lokacin da suka bi]i mafaka da

sauran abubuwan al’ajabi, wa]anda ba za ta iya fa]a ba.

Baya ga wa]annan abubuwa na al’ajabi da ta

gani, ta kuma sami wasu azzalumai wa]anda suka

cinye mata ku]i, har aka yi musu shari’a, suka kunyata,

kamar Sarkin ruwa wanda ya cinye mata jaka 20, amma

aka sa ya basu jaka 10. Daga baya ya ji tsoro ya ba ta

fam sittin a ~oye yana lallashin ta, ya ce ta rufa masa

asiri. Hakanan Shehun takari ya biya ta jaka guda

saboda fam 4 da ya cinye mata.

Talha: - A Talha ta gamu da taron danginta kuma ta yi

wata 5 tana tafsiri a garin. Wani Alhaji ya so ya zaunar

da ita a Sudan amma ta }i. Ya ba ta fam 2 da takalmi.

30

Barta: - Bayan ta taso daga Talha sai ta zauna wata 9 a

garin Barta, ba ta aikin komai daga addu’oi sai karatun

Al}ur’ani.

Saudi Arabia (Makka)

An ba ta Fam 28 wanda ta biya ku]in jirgi na Tayyara,

wato filin jirgi (domin tashi zuwa Makka).

Alhamdulillah ta iso Makka a cikin watan Sha’aban,

bayan ta shekara 2 bisa hanya. Lokacin da ta iso, ta

sami ha]uwa da abokan tafiyarta Maryamu Kurma da

Habsatu wa]anda suka riga ta isa garin Makka, ta yi

Hajji tare da su, suka gode wa Allah ma]aukakin Sarki

game da samun ]auke farali. Ta tabbatar wa mutane

cewa, sukar da wasu suka yi mata tun daga Sakkwato

suna cewa ba hijira za ta yi ba, hajijiya za ta yi, to

alhamdulillahi hijirarta babu ma’asi wato sa~o a cikin

ta, saboda hijirarta ta addini ce wadda ta yi kama da ta

mahaifinta, kuma ta yi kama da ta Annabi (Sallallahu

alaihi wa sallam) daga Makka zuwa Madina. Don haka

wa]anda suka yi sukar fitar ta masu hasada ne, amma ta

nuna hasadarsu ba ta dame ta ba. A nan ne ta kai ga

kawo }issar Annabi Yusuf (alaihis salam), inda

‘yan’uwansa suka nuna masa hasada da }iyayya

a }arshe ya fi }arfinsu ya sami nasara a kansu ya zama

Sarkin garin Misira. Ta kuma ci gaba da cewa gado ne

ta yi, domin kakanta Gwani Mukhtar ma, ya yi karo da

hasada, amma duk da haka nan ya ci garin Kukawa

ta }asar Borno da ya}i, ya yi mulki shekara takwas da

wata takwas da kwana takwas, sannan ya yi shahada a

fagen fama.

31

Zaman Modibbo Kilo a Makka

A Makka Madibbo ta sadu da wani Mani ]an Malam

Ahmadu Je]o, sannan kuma abokiyarta Bagumbora

wadda ta baro a Sudan, ta ba da ku]i domin a kawo ta

Makka. Bagumbora ba ta sami isowa ba sai bayan

shekara ]aya kuma ko da ta iso sai ta sami Modibbo

tana Madina, ta kuwa matsa a kai ta. An kai ta Madina

amma bayan ta yi wata hu]u a wurinta sai ta rasu.

Modibbo ta dawo Makka tare da wani da ta ce

Ibrahimunta bayan rasuwar Bagumbora.

A cikin wa}ar dai, Modibbo ta kawo bayanai

game da aikin Hajji, wato fita daga Makka zuwa Minna,

wanda ta ce aiki ne mai wuya ainun da [awafi da

Sa’ayi da kuma halartar Arfa. Modibbo Kilo ta fa]akar

da maniyyata da su yi tattalin guzuri na }warai don

harkokin yau da kullum da kuma guzuri na tsoron Allah.

Hakanan ta }ara fa]akarwa, tana cewa a guji aikata

abubuwa marasa kyau lokacin gudanar da aikin Hajji,

misali }arya da girman kai da alfahari da bugun gaba

da izza da son isa da nuna asali ko nuna sarauta da

sauransu. Ta nuna cewa game da aikin Hajji, babu

bambanci tsakanin malami da mai arziki da talaka da ]a

da bawa, duk ]aya suke a haramaini. Modibbo ta }ara

bayyana cewa, ba a zaman banza a Makka sai dai da

sana’a, wasu suna sa}ar tabarmi ko tsawwa (igiya),

wasu na tallan ruwa, wasu wankin tufafi wasu ]aukar

kaya (dako) da sauransu.

Modibbo kilo ta ci gaba da bayyana halayenta na

ba ta }in kowa don hasada, sai dai tana }in mai yin

hasada ga mumini. Hakanan ta ce ba ta }aunar fasi}i,

mai cin amanonin musulmi mai kissa da zamba

munafuki mai }in jama’ar musulmi haka kawai. Ta ci

gaba da cewa ta bar wa masu son duniya duniyarsu su

32

yi ta shagalinsu. Ta yabi Sarkin Musulmi Abubakar na

III, inda ta kira shi jikan Shehu Usmanu [anfodiyo da

Bello da Mu’azu.

Modibo ta kafa makaranta inda ta koyar da maza

da mata fannoni daban–daban na ilmi, har ma ta kai ga

yin tafsiri a garin Makka..

A cikin wannan wa}a dai Modibbo ta fa]i cewa,

Maryamu Kurma ta yi jinyar ciwon ciki na wata tara

kuma a lokacin rasuwarta ta yi ta yin kalmar shahada.

Ta rasu tana da shekara sittin da uku cikin watan Rajab.

Kafin a bisne ta an yi mata wanka aka sa mata turare da

likkafani, an yi mata salla. Modibbo ta ce jikinta ya yi

laushi ya yi haiba ya koma tamkar alharini. An ajiye

gawarta a Babul-Ati} kusa da Mu}ama Ibrahim, kanta

daidai da dutsen Aswad, }afafunta daidai da Ha]im,

bayanta daidai da rijiyar Zam-zam, gabanta daidai da

Multazam. Sannan limamin masallacin (Harami) ya yi

mata salla, ta ce, bisa godabe ko hanyar Aljanna a

daidai Babus-salam. Ta fa]i cewa an yi mata }abari a

wani wuri da ake cewa Mala, inda aka bisne ta.

Modibbo ta }ara da bayanin cewa, Maryamu Kurma ta

sami babban rabo da rasuwarta a Makka, domin dai

kafin ta rasu ta kasance mai ibada da ta}awa da aikata

ayyukan }warai. Don haka ita ma ba hajijiya ta yi ba,

kamar yadda wasu masu tsegumi suke cewa, wai

Modibbo Kilo da Maryamu Kurma ba hijira suka yi ba,

daga Sakkwato zuwa Makka ba, a’a hajijiya suka

yi, }aulin da Modibbo ta }aryata. Ga baitocin da

ke }unshe da wannan bayani.

Bisa godaben Aljanna Liman yai mata,

Salla da jama’atai cikin Haramaini.

33

Rakiyar musulmi da rahma har Babus-salam,

An kai ta Mala can cikin Haramaini.

Madalla Maryamu ta yi samu mai yawa,

Ta gadi jewun Ahmadun Al}ali.

Ita tata ai fa hajijiya ta zam rabo,

Saura fa ni, in wurga can Firdausi.

Haka kuma Modibbo ta yi ro}on Allah shi gafarta mata

tare da Maryamu da Habsatu da A’isha da Bagumbora a

cikin wasu baitoci. Ga abin da ta ce:

Allah ka gafarta gare mu, da su duka,

Allah shi ba mu, mu taru can Firdausi.

Midobbo ta ci gaba da yi wa kanta ro}on Allah Ya ba

ta tawali’u da cikawa mai kyau kamar haka:

Ni dai ina ro}on Ka ba ni tawalu’i,

In kau cika bisa ai fa hanya Ahmadi.

Hakanan ta yi wa iyayenta da kakanninta da masoyanta

masu bin sunnar Annabi Muhammadu (sallallahu alaihi

wa sallam) addu’a.

A }arshen wannan wa}a, Modibbo Kilo ta ba

da bayanin yadda za a gane gidanta idan an je Makka

ana nemanta. Ta ce suna unguwar Har al-Yamal, kusa

da wata kasuwa mai suna Umdan jarwali. Ana sayar da

gawayi da itatuwa da hakukuwan dabbobi a wurin

kuma tana kusa da wani masallacin unguwar gidan

Umdan. Idan an je wurin sai a tambayi gidan Modibbo

Kilo ‘yar Sakkwato ‘yar Al}ali, mai tafsiri, uwar]akin

34

Maryamu Kurma, sai a nuna wa mutum gidan wanda ke

kan dutse. Wannan magana na }unshe a cikin baiti na

533 -542.

Wannan da yaz zam na bi]a ta Makka yau,

Har tal-Yamal shiyya fa Umda’uza’i.

Wannan da zai fa bi]ag gidana kun jiya,

Da]a kassuwa ‘Yabbarno Jarwal zai bi]i.

Modibbo Kilo ta rufe wa}arta da ambaton Allah da

salati ga Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa

sallam) da Alaye da Sahabbai da Tabi’ai. Hakanan ta

kawo ramzin wa}ar, 1374 bayan Hijira, wanda ta

bayyana kamar haka a cikin baiti.

Ramzi na hijiratai fa MINYASALASATA,

Da Alif da Saba’in har fu]u na Muhammadi.

35

Wa}ar Hijira da Zaman Modibbo Kilo a Makka

Bismillahir Rahmanir Rahim

1. Bismil ilahi na fa gode Ubangiji,

Na gode {ur’ani na mai haramaini.

2. Na yo salati ga mai salati Muhammadu,

Har kau da Alu Sahabatun haramaini.

3. Ni za ni lissafin fita das Sakkwato,

Har rash shigowata garin haramaini.

4. Shi ag garin Usmanu babba mujadaddi,

Jikan Muhammadu na na nan haramaini.

5. Rana ta Lahadi sha biyu ga watan Rajab,

Hantsi fitowata zuwa haramaini.

6. Yab ban Amirul muminina fa Rabbu shi,

Shi Bubakar mai son zuwa haramaini.

7. Allah Ka jinkirta ma babba uban gari,

Shi ]an ubanai mumini Uthmani.

8. Shaihun Mu’azun Bello na na mujaddadi,

Allah shi gafarta ma kau raba gardami.

9. Allah Shi ]aukaki al’amurranai tutut,

Dad duniya har barzahu har lahiri.

10. Allah Shi tasshe shi ga tutab Bubakar,

Siddi}u shi na sahibi na Muhammadi.

36

11. Ya gadi Shaihu ubansa mai addini,

Ga kau fa alher ga ri}on {ur’ani.

12. Ya yo fa Fasbo nai gare ni fa shid da ji,

Ya ba ni fam goma da kau murnoni.

13. Domin fa Allah yay yi don fa Muhammadu,

Ba don fa kowa yay yi ni kam na sani.

14. Ya yo takarda inda Sarkin kau Kano,

Ga bi]a abokina zuwa haramaini.

15. Gadon Mu’azu da Bello yay yi da Shaihu kau,

Na tabbata ya yo hali na mujaddadi.

16. Shi ]a na Shaihu Uthmanu ]a na Mu’azu ji,

Shi ]a na Bello, Bello ]a na mujadaddi.

17. Allah Shi gafarta uwa da uba duka,

Allah Shi gafarta shi har [angwaggo shi.

18. Ya gadi Attahir fa mai fa amana,

Haifen Mu’azu da Alu wan raba gardami.

19. Na sabka nan fa gari na ]an Ashafare, ji,

Sambo waliyyi na zuwan haramaini.

20. Da azzuhur nik kwana ukku ha}i}a ni,

Wallai gidan [an-Ambo na na uwag gari.

21. Jikan Buharin Tambuwal Dam-Makka ta,

Haife na Ahmadu ]a na Nana uwag gari.

37

22. Rana ta lahadi nif fa sabka fa nan Gusau,

Nau hankali ya tashi don haramaini.

23. |auna da }arfi babba ta yad Damisa,

Manzonta ya sabko fa nana gare ni.

24. Da sulenta goma kaza da kwanoninta duk,

Da batunta mai sanyi fa nana gare ni.

25. Da]a niy yi bankwana da manzon nata duk,

Don za ni tashi ga zuwa haramaini.

26. Na so zuwa fa }warai mu yo bankwana dut,

Allahu Yaf fa hana ni don haramaini.

27. Ko da Bagumbora, Yagudu da Habsatu,

Ga zuwa fa {aura Rabbi yaf fa hane ni.

28. Ko da fa Fatume ko Halimatu, Maryamu,

Ko da ]iya har Kande a}ali ya tafi.

29. Ko da fa Baubawa bale fa Buhari dut,

Tamka jununi nis shigo haramaini.

30. Na kwana ukku Gusau ina shawarwaki,

Wallai da bankwana ga mai {ur’ani.

31. Dut Rabbi yaf fa hana ni kowace kau jiha,

Niw wakkalo gun Rabbi mai haramaini.

32. Ita a] ]iyas Sarkin Gusau shi Murtada,

Ita Fa]ima] ]an Sambo ]an Ashafa ni.

38

33. Ya ba ta ta gada karama goma sha,

Saura guda ka nufa ta zo haramaini.

34. Na }are littafe gaban Asma’u kau,

Na aika mai }amna gare ki gare ni.

35. Domin amana] ]alibata mallama,

Dangin karatu tab bi]e ki gare ni.

36. In ke ga hali ta fa zo miki mai ladab,

In babu hali Jalla ya ]auke mini.

37. Tamkag gudanowa ta dabba nif fito,

Nan inda Zaki za ni na haramaini.

38. Tamkag gudanowat Tumaki nif fito,

Nan kau ga Kuraye zuwa haramaini.

39. Tamkaj jununi niz zamo fa jama’ata

Sa’af fitowata zuwa haramaini.

40. Allahu Sarki Wanda Yay yi ni mai niya,

Shi yaf fa kimsa min zuwan haramaini.

41. Na so zuwa nan inda kau Mamman Tukur,

Har dud da Katuru ga baffa Atiki.

42. Dut Rabbi Sarki bai nufa in zo ni can,

Allah gwada min shahidai Firdausi.

43. Ya ku masoyana zumaina kun jiya,

Shara]i ku gafarta ni don haramaini.

39

44. Sirri na zucci ka]an fa niz zanta muku,

Domin fa hakki don ku gafarta mini.

45. Ni dai Rasullullahi yac ce Saudatu,

Ta so fito maza zo cikin haramaini.

46. Nit tashi nig gigice Sarki Ya sani,

Ni ban ganin kowa fa sai haramaini.

47. Tamka’ a ]amre a tuntsure nan niz zamo,

Na sha fa zilla don bi]ah haramaini.

48. Don hankalina ya fice ga fa nawa kai,

Daga waswasani a kan zuwa haramaini.

49. Kai na ga mamaki gare ni fa zay yawa,

Tun rad da niy yi shirin zuwa haramaini.

50. Don ya Rasulullahi yay yi tsayin daka,

Yac ce fito fa fito zuwa haramaini.

51. Ni] ]amra kwanana ha}i}an ya cika,

Bisa na yi tsoro mai yawa fa gare ni.

52. Ni] ]amra kabrina ha}i}a ag gaba,

Ni ban zaton ko in iso haramaini.

53. Sai dai fa tauhidi da]a shi nir ri}a,

Allah cika min kau bisa imani.

54. Na iske ‘Ya’ambo Waziri ta Mukkunu,

Birnin Gusau da halin ]iyan dotti~e.

40

55. Halin Buhari Waziri badikkonta shi,

Tay yo fa fara’a mai yawa fa gare ni.

56. Har dud da matan Atto sun yi fa gwargwado,

Har dud da ]an Sarkin fa Galma gare ni.

57. [an Hammada ]a kau na Maunuma kun jiya,

{anwa ga Shaihu mujadaddi Uthmani.

58. Yaz zo da kainai gwaggo, gwaggo Umar fa shi,

Da sulai biyat yab ban zuwa haramaini.

59. Shi ]an Marafa ]alibin nau walidi

Na ]an Yugudu fa na fa ]a fa gare ni.

60. Mallam na Kor]on Madawaki uwammu dai,

Ita a] ]iyab Bello na Shaihu Mujaddadi,

61. Matab Balarabe ]a na Muna da Anbo ta,

Ita ta ]iyak kau Bayaro na uwag gari.

62. Ya yi }o}ari ranas shiga jirgi garan,

Ga cikin Gusau ran nan fa yai wahaloli.

63. Abdun Tanin da masoyi Rabbi Ubangiji,

Allah ka saka mai fa duniya lahiri.

64. Rana ta Larba nif fito Birnin Gusau,

Nis sabka Zariya inda Bello Macaji.

65. Ga dare na Jum’a nif fa sabka Tudun wada,

Nan inda ]an Kilo ai ]iyaf fa Bara’u shi.

41

66. Ya zo shi ya tarbo ni gwaggo fa, gwaggo ho,

Jikan Bara’u da kau Waziri Bukhari.

67. Jikan Waziri Bukhari na,}i tan}wasa

Bini jika Ahmadu ]a na Nana uwag gari.

68. Ita a’ Kilinshin ]an Bukharin Tambuwal,

[an nan na Shehu mujadaddi Usamani.

69. Bai gadi kissoshi fa Allah Ya tsarai,

Nonon Bukhari da yaf fa sha ]an Shehu ji.

70. Allah ka gadas sai gadon ]an Ahmadu,

Nan inda barden Mahdi mai addini.

71. Ya ba mu shimfi]]u abinci dud da sha,

Gadon Waziri Bukhari ]an Dammakka shi.

72. Ita a] ]iyam mallam Bukharin Tambuwal,

Mata ta Ahmadu ]a na Nana uwar gari.

73. Ya yo jihadi Bello yai tsaye mun shiga,

Wallai da kainai ba fahar don asali.

74. Allah Shi saka mai Shi sa kau an kirai,

Ya Rabbi don caffa zuwa ga uban gari.

75. Shi na Amirul Muslimina fa Bubakar,

Jikan Mu’azun Bello ]a na mujadaddi.

76. Hantsi na Jum’a nif fito daz Zariya,

Da]a nau nufi ji]a ga Abdullahi ji.

42

77. Ranas subahin Assibit nis sabka kau,

Ga Kano, daren Lahadi ga Sarki salihi.

78. Da]a niy yi kwanakki fa hamsin har da bi’u,

Na gode Allah inda ]a na Abashe shi.

79. Jikan Maje Ringim Maje fa karofi ji,

Shi hashimi na inda Dabo fa Cigari.

80. Shi mallami na adili mai farra’a,

Ya gadi kakatai Husaina ta Cigari.

81. Domin fa kakannin da ummat tamu kau,

Su as sha}i}ai inda Fa]ima Dabo ji.

82. Dangin abinci kullayaumin goma sha,

Dangin abin sha mai zuma don khairi.

83. Da iri–iri nau’in ]iyan icce ku ji,

Kullum a kai ma fa mai zuwan haramaini.

84. Da tufa da }arfe har da goro fa zay yawa,

Nau’i da nau’i don zuwa haramaini.

85. Mata hu]u da]a ag gare shi fa ba fahar,

Kullum da manzanninsu don addini.

86. Bauya kamar fa wajan ]ari ga fa mai }ida,

Kullum suna nan don bi]ak kau ilmi.

87. {arfe fa ashirin har da goro ]ari ]aya,

Kullum fa Jum’a don zuwa haramaini.

43

88. Goro fa hamsin har da }arfe goma dut,

Ga su Umma kowace Jum’a don addini.

89. Da Uwaf fa soronai fa Mowa mu’awina,

Mai }o}ari ta Mowa mai son ilmi.

90. Jekadiyassa tara uwar fa waje shi ke,

Har dud da Balki tana da son addini.

91. Dibo ga ‘yan soronsa goma fa sha biyu,

‘Yan yara soro, babba nan fa a can wuri.

92. Akushi ]ari fa bakwai da swahe da hantci dut,

Hakanan dare aka yin su don ]ai lahiri.

93. Babban gida na mai yawa tamkag gari,

{ofarsa arba sai ka ce }ofag gari.

94. {ofak kudu sunanta Sakkwato kai jiya,

Shiya’ Uwaddaje ta ]iya ta mujaddadi.

95. {ofa’ Arewa wurin fa gonakkinsa na,

Sunansu Shekara bansa don fa halali.

96. {ofag gabas sunanta Yakasai ita,

Shiyya ta ‘yan Sarki fa mata jami’i.

97. {ofa ta yamma fa Garko as sunanta kau,

Shiyat makubla ai na manya sun tafi.

98. Kai na ga halin nasu tamkaj jannata,

Ga zuwa misali nig gudo haramaini.

44

99. Ha}}an du’a’in Shehu ya zamna Kano,

Da Magili don ladabi ila kau mahshari.

100. Taron ]iyan Sarki Maje Lakwaja Alu,

Sun taru nana garan bi]ak kau ilmi.

101. Da wa]ansu ‘yan Sarki Galadiman Kano

Su Kilinshi har Maigoshi don kau dini

102. Alhamdu lillahi da samun A’ishatu,

Ta sha fa nonon kau gida na mujadaddi.

103. Don babu ha’inci da zamba da kissa kau,

Da]a ta yi ]a’a don bi]a} {ur’ani.

104. Kuma babu fasicci da ha’inci kuma,

Wallahi har tallahi sai wawanci.

105. Ranad da nif fita kau Yagudu fa ta fita,

Das Sakkwato har kau Kano don dini.

106. Kuka takai kullum sununta ka }aruwa,

Domin fa kau rabuwa da ni don ilmi.

107. Haife ta [angara ai na Gomfa kun jiya,

‘Yalladdo haifen Shehu ]an na mujadaddi.

108. Allah ‘kirai ki ga Makka har da Yagudu kau,

Tariya ta Mahdi don ladab mai ilmi.

109. Aibinta wauta nan ta fillani duka,

Ita anka bar ma ba ta kissa ga dini.

45

110. Rakiya ta ‘yan Sarki da sunka yi nan garan,

Har dai fa zango namu can Waruri.

111. Duk sun yi bankwana suna kuka duka,

To gwaggo ni ma na yi don haramaini.

112. Sun tashi sun bar kau Yagudu tana fa nan,

Haife ta datti~e fa babu nifa}i.

113. Kullum a aiko ci da sha }arfe duka,

Ta zamni kwana ukku can Waruri.

114. Hakanan fa Ahmadu ]an fa Hajaru tamu kau,

Wallai ]iya ta Marafa ]an ta mujadaddi.

115. Wallai ]iyan ga fa biyu gidan Isan Kware,

Da fa ]a da jikanya su zam Firdausi.

116. Sun so ni ha}}an sun gwada min so kuma,

Har dud da Basharuna fa kau marhumi.

117. Sun kau gwada min ai irin Usumanu na,

Sun sha fa nonon nan na kau fa mujaddadi.

118. Allah Shi gafarta ma Hajaru Luddu dut,

Domin fa sun haifo hali na mujadaddi.

119. Mun jid da kaya nan ga mota ta shiga,

Ita kau da Adamu har cikin kau Ringi.

120. Sun safka kuka ]ai takai ni ma inai,

Gamuwammu sai Allah fa sai Haramaini.

46

121. Allah Shi gadas she ta manya nan da can,

Har ni da ke da ]iyak Kilo Firdausi.

122. Ta zam a summun abkamun umyun kuma,

Da]a ta yi amre don bi]a Haramaini.

123. Wauta ta ‘yan Sarki da ‘yan fillani,

Na nan gare ta tsarat ta Rabbi da sharri.

124. Sharri na She]annu butullai fasi}ai,

Kuma ga kwa]ai kuma ga zama dujjali.

125. Na ro}i ]akin Ka’aba ga ni ciki nasa,

Allah biya gurinku kun bauta mini.

126. Domin fa Allah don fa Al}ur’ani,

Ba don kwa]ai domin fa moyin Rabbi.

127. Nit tashi Sarkin kau Kano yas sallaman,

Yab ba ni fam goma kamat na ubangari.

128. Dud dut iyalinai fa, sun yi fa gwargwado,

Alhamdulillahi garan, don dini

129. Kuka sukai tamkaf fitata Sakkwato,

Ga fa masu so tamkaf fa Makka ga Ahmadi.

130. Farkon nufa Tabsir ga matan Sakkwato,

Ku tsaya, ku saurara fa, kazibban wuri.

131. Babba] ]iya’ Usmanu ita matat Tafa,

Da uwag-gari da uwad-Daje yaransa, shi.

47

132. Baicin su Daudu, ]iya ta Abdullahi kau,

Mata ta Landijo fa ]anai shahidi,

133. Sai Ukhtiya ‘yas Sambo sai Janajo ji,

Ita ad ]iya’ matat Tafa mutafannini.

134. Bayan su Matar-modi binti uwad-Daje,

Umrinta ha}}an, babu bidi’a zahiri.

135. Baicin su Dikko ]iya ta Ahmadu Gwandu ta,

Haifen Basharun Ukhtiya da Aliyu shi.

136. Zamaninta Habsatu tay yi gwaggo amaliya,

Haifen fa mallam Mani ta mutafannini.

137. Hakanan fa Hauwa ]iya ta Abdul}adiri,

Baban fa, mallam Bube na mashhuri.

138. Bayansu Saudatu ta Kilon Mahmudu ji,

Al}ali ma’arufi na kau addini.

139. Jikan Gwani Mukhtari na fa, uban gari,

Jikan Gwani Mahmudu ]an Musa Gwani.

140. Nis su]e }waryayensu su dud, nig gudu.

Nib bar su, nig gudu, don fa, ba su da hasuli.

141. Alhamdulillahi gari na mujadaddi,

Na sami albarka ga Shaihu mujadaddi.

142. Da]a nit tafo babban gari na Bahashime,

Kakan fa kakana fa, Shaihu mujadaddi.

48

143. Bayansu ha}}an babu mata Hausa dut,

Ga fa yin Jalalaini fa, sai dai kibri.

144. Sai jera }arya ga kwa]ai da kaba’ira,

Ga son fa girma ga fusudi sun boni.

145. Sun yanke tsari nan na manya kaico su,

Sun ]au fushin Shaihummu babba mujadaddi.

146. Kaicommu ha}}an raf fitammu ga duniya,

In mun }i tuba, ba mu samun lahiri.

147. Manyammu sun yi fushi da mu ya ’yan Adam,

Don Allah, don Allah, mu tuba mu sam shiri.

148. Da]a babu ilmi nan ga mata zahiran,

Sai dukiya, }arya fa sai ta ma’asi.

149. Na tuba ‘yab baiwakka Allah Rahimi,

Tubu nasuhan sai da su kaka gafiri,

150. Domin fa, na samo alama’ Annabi,

Jama’aj jahala sun yi murna zahiri,

151. Wasu kam jafa’i wansu kuka zahiri,

Sun duma har abada cikin da-na-sani.

152. Kukansu yai tamka fa, nawa ga mai gani,

Ga rashin zuwana, inda mai {ur’ani.

153. Kukan masoya raf fitata Sakkwato,

Tamkaf fita kau, ya Rasulu ga Makka shi.

49

154. Ha}}an ha}i}an na yi ni, da-na-sani,

Ga rashin zuwa {aura ga ‘ya’ Ashafare shi.

155. Domin guda na yay yi zamne ga zuciya,

Ciyyonsa yaz zamne ni, sai Firdausi.

156. Ai wofofo, kuma wofofo, na tuba ni,

Ya Rabbi ba ni ganin ta can Firdausi.

157. Ni na fa tuba ga Rabbi Sarki, mai muwa,

Bai }addaro in zo azal fa gare ni.

158. Domin fa, fitanad duniya ga fa mumini.

Samun rabo na mai yawa Firdausi.

159. Nib bar Kano sha biyu ga ai Ramalana.

Rana ta Larba, don zuwa haramaini.

160. Sarkin Kano yak karkasa tafiyaf fa tau,

Har ukku, don sau}in mu zo haramaini.

161. Yac ce Bagumbora Bukhari da Fatume,

Har dud da Kande, su dakata Farlomi.

162. Yac ce ku bar wanan fa, she]ana ag garai,

Mai nashi hali bai zuwa haramaini.

163. Yac ce da ke fa da Habsatu, har Maryamu,

Kurma ta zam fidimakku don haramaini.

164. Nic ce na’am, na gode Rabbi fa, na jiya,

Na amshi ni fa batunka Bayaro nasihi.

50

165. Sababin da Habsatu tai fushi har yai yawa,

Allah Ka gafarta ma mai addini.

166. Farkon fa, zango namu Ringim, har Guru,

Ranaf fa bazara ga fa, kau Ramalani.

167. Da tsakad dare mun tashi, mun zo Yarwa mu,

Kwanammu fu]u na munka yo Farlomi.

168. Mun kwana biyu nan mun iso can Atiya,

Da fa kau gurubi munka sabko nan wuri.

169. Da tsakad dare mun tashi mun bar kau wurin,

Domin ~arayi munka bar wannan wuri.

170. Ga rabi }afa, ga rabi fa mota, don mu sam,

Sau}i ga zilla ‘yan Adam haramaini.

171. Da fa]a da kokowa muna dubin ajab,

Da maza da mata arba’in na, don haram.

172. Hantci yinin Lahadi muna can kau Wadai,

Mun kwan guda don shan ruwa Ramadani.

173. Mun yo fa salla Attanin da fa azzuhur,

Mun tashi, mun bar nan fa, don haramaini.

174. Mun zo mu can Adire fa ga mu da kafirai,

Mugun wuri hanya} }asa ta Faransi.

175. Da gudun }afa da }aya itace, har ruwa,

Gebe da dutci, don zuwa haramaini.

51

176. Da dufun subahin mun iso fa Jinaina mu,

Sai rarrafe muka yi da zamne ga lokaci.

177. Mun kwana sha hu]u don ruwan malka, kuma,

Dolemmu cilas, don zuwan haramaini.

178. Mun kwana ishirin nan da kau fa biyat jiya,

Ga tsakaf fa daji sai fa kau Zakoki.

179. Da]a mun iso Kaka biyu kwana ]aya,

Mun tashi ba fashi zuwan haramaini.

180. Mun zo mu can Fashir garin Ali-dinari,

Kwana biyat ]ai mun wuce haramaini.

181. Shi af fa babban kafiri fa, Bamaguje,

Sa’a ta umri nashi ha}}an zahiri.

182. Mun zo Nafut, mun zo mu cana Dubayyaji,

Mun yo biyat mun kau wuce haramaini.

183. Da]a mun shigo jirgi da yaz zo can da mu,

Har can fa Hartum, don mu zo haramaini.

184. Jirgi da yaf fa tsaya ka]an mun ji]a don,

Mata bakwai domin mu yo salloli.

185. Dut ha~e na, na Kano fa masu fatauci,

Sai Habsatu sai ni fa af Fillani.

186. Jirgi da yam motsa fa dut sun kau shige,

Sai Habsatu taw wanzu nana ga daji.

52

187. Bisa na ri}o }arfe na jirgi na tsaya,

Nid dubi Habsatu can tana tsaurin kai.

188. Bayan fa tashi nashi nik ko sunkuyo,

Domin amana Jalla don shi wahidi.

189. Niy yo }azat domin ta nif fa]o }asa,

Nib ba da raina inda Allah {adiri.

190. Jirgi da yab bi ga kau cikina bayyane,

Sai nig ga Annabi yat tsaya fa gare ni, ni.

191. Da rashin sani kafuwa da kau fa ganina,

Su sunka sa ta fita da alfarmomi.

192. Rairan da nif fa]o ina ta makarkata,

Kuka ha}i}a zatonsu ya fa kashe ni, ni.

193. Mu biyu muna tafiya cikin daji ba}i,

Tun assalatu da azzuhur sai Rabbi shi.

194. Mun zo mu Madani kassuwa} }auyawa,

Dud dut }afafummu awa salkoki.

195. Sannan fa sa’a shidda jirgi ya’ iso,

Nin nuna wurga shigo ku zo haramaini.

196. Mun kwana yin tafiya da hantci ya’ iso,

Can kau fa Hartum don zuwa haramaini.

197. Da }afammu munka iso fa nan Undurman,

Bisa ai }afafu namu sun yi fa kunburi.

53

198. Mun iske Maryamu babu ci, kuma babu sha,

Kuka da hargowa ana lallashi.

199. Sai Maryamu na can ga jirgi zamne shu,

Sai ga mu Maryamu tay yi kau mamaki.

200. Mun zo mu biyo ga wata na layya can kuma,

Wallahi Undurman muna ta ta’ajjubi.

201. Nan nif fa zamna ni da Umma da Maryamu,

Shi madugummu yaw wuce haramaini.

202. Suna talatin nan da kau fa bakwai bisa,

Sun yo fa niyya za su na haramaini.

203. Niz zammi Undurman wata na ukku ]ai,

Nit tashi don niyya zuwa haramaini.

204. Ga watan safar nib bar fa Undurman jiya,

Ishirin da ukku garai fa don haramaini.

205. Ranad da niz zo kau Mahattabarta kau,

Nim mance sundu}i bisa nisyani.

206. Dangin fa littaffai da kundaye fa kau,

Sababin fa ayatai fa Jalla mamallaki.

207. Walatuballigihi illa bi shi}}il anfusi

{auli na Rabbi ga Makka inda Muhammadi.

208. Ranad da niz zo sai ka ce basarakiya,

Kandu fa yak kama ni komi babu shi.

54

209. Sun amshi fam sittin da kau fa biyat bisa,

Mu ukku allura da surar ja’iri.

210. Jirgin bida’a munka hau fam arba’in,

Don cin amana taf fa ci su fa zahiri.

211. Tun can Kano mu arba’in na munka zo,

Mota guda ta za mu can haramaini.

212. An samu jirgin Jidda mu kuma arba’in,

Domin mu zo, mu wuce garin haramaini.

213. Mu na fu]u ]ai am musulmi za mu na,

{inginsu Masarawa na da kau Nusrani.

214. Amma suna renommu tamka ‘yan ]iya,

Ni ban kula ba da su ba don haramaini.

215. Ishirin fa nan ga Rabi’u mun shiga Maliya,

Ra’ Alhamis domin mu zo haramaini.

216. Don Kuntumuklis an ka ba fam arba’in.

Mu ukku don shi wuce da mu haramaini.

217. Yab ba ya Kyaftin Micco don shi iso da mu,

Nan Jidda don mu wuce zuwa haramaini.

218. Yaz zo da mu Gunsur Bature yah hana,

Yac ce fa an katce su ba haramaini.

219. Mun kwana ukku da mu da Kyftin Maliya,

Dangin bida’a anka kai haramaini.

55

220. Nan niy yi kau Yasi arba’ina da ]ai duka,

Bisa ai fa Gunsur mai hanin haramaini.

221. Niy yo du’a’i niy yi ro}o mai yawa,

Sa’a guda ta niy yi don haramaini.

222. Kyaftin fa Micco nan fa yai yawo da mu,

Bisa Maliya har can kusan kau Hindi.

223. Kwananmu goma fa sha biyat can Maliya,

Tafiya mukai ga ruwa da ikon Rabbu shi.

224. Na sami albarka ta Annabi Yunusa,

Musa da Haliru har da Zul}arnaini.

225. Daga nan ajab dut na gano shi, ga nau gani,

Nina yi sa’ata, ta kau imani.

226. Ranaf fita fa takai fa zamne ga Maliya,

Har kau wata bisa ai fa kau mamaki.

227. Kifi kamad Dorini, Kwa]]o awa ]aki,

Tsutsa kamat Tunkiya ga Bahar ta

haramaini.

228. Ita az Zubaidatu Rabbi yas sabkam mata,

Sunan La]ifu ga Maliya don fa kau riz}i.

229. Kai na ga dutci sinfil wanda sunansa

Wannan da jinni yai magana Ibranci ga Bahashimi.

230. Ya ce ‘kabash habasha wallahi kau raja raja,

Wallai sayandili yandili da yadduni.

56

231. Ni na ga Ba}arul barri anka gwada mini,

Dutci kamas Sanuwa hanya ta haramaini.

232. Kuma na ga dutci in da haula da }uwwatu,

Allahu Yas sabko da aya sun gwadi.

233. Na yo fa tcinka inda }arya Balki kau,

Har }arya Namlu da }aryatun Najjashi.

234. Ni na ga dutci sai ka ce shigifa fa ta,

Wallai da marfi nan zuwa haramaini.

235. Nan inda Sidi Mujaili yay yi ibada,

Haske awa rana na Abdul}adiri.

236. Ni babu hali in gaya muku dut ajab,

Amma mafalki nawa yai tasdi}i.

237. Dud dut ga Maliya niy yi kallon al’amar,

Na gode Allah na da]o imani.

238. Sunan gari kau Shaikhu Usman nig gani,

Shi aw wurin sabka fa, ai Usmani.

239. Nuri da haske wa fa kau fitila nana,

Allah gwada mini Shaikhu can Firdausi.

240. Kyaftin fa Mucco yaf fa ce kai ]an’uwa,

Ni dai ina ro}o ka zo Sudani.

241. Kyaftin fa Rasdan nawa kai a] ]an’uwa,

Ka mayad da mai himma batun haramaini.

57

242. Ni za ni Istanmbul fa shekarru biyu,

Nika yi fa don haka nif fa komo musawwani.

243. Wannan da yak ko }aryata don she]ana.

Don hasada kibri ku bar mal’uni.

244. Mai sheda }arya mai jidali makiri,

Ga rashin gani kuma fasi}i kazzabi.

245. Sai wanda yas shiga Teku ya’ isa Makkata,

Shi yaf fa fi ni ganin sarautocin {adir.

246. Yac ce ka mai da fa mallama Sudani,

Can inda Shaikhofin da sunka ci Mali.

247. Yab ba shi fam ishirin fa cana musawwa don,

Mu arba’in kuma munka yo Sudani.

248. Ranab biyat ga Rabi’u lahir munka zo,

Mun sabka ran Jumu’a cikin Sudani.

249. Nig gode Allah niy yabo shi Muhammadu,

Don na yi ilmi aja’ibi ga mu}addari.

250. Bayan fa komawanmu yam mutu kafiri,

Gunsur Bature ja’iri Nusrani.

251. Sau}i na Allah yaf fa sabka ga talikai,

Tun shekaran nan har fa yau haramaini.

252. Domin Mushari yak kashe shi da bindiga,

Domin fa kafirci na kau Nusrani.

58

253. Don shi fa ]an Sarki fa na fa Mushari,

Sarki na Makka fa adili Abdullazi.

254. Da]a anka yo wani an kashe shi munafuki,

An kada Fam hamsin ga mai haramaini.

255. Kai barakalla na yi gado ni kuma,

Sa’a ga hijirata ga kau haramaini.

256. Mun yo shari’a ni da su sun kumyata,

An sa Saraki nan cikin wahaloli.

260 Mun yo shari’a nan salasata ashhurin

Ni] ]abgi tarbeza ta ko fa Yahudi.

257. Su dut Sarakin an fa tashi gare su dut,

Da fa]a da ~ar~aci da kau cin irli.

258. Sarkin ruwa yab ba su jikka goma shi,

Domin fa Fam ishirin da yac canye mini.

259. Shaikhun Takari yab biya jikka guda,

Domin fa Fam hu]u wanda yac canye mini.

260. Wannan da yac ci kwabo gare ni fa arba’in,

Shi Fam talatin yaf fa ba Nusrani.

261. Sarkin ruwa nan yay yi tsoro mai yawa,

Yab ba ni Fam tis’in da kau lallashi.

262. Da~ ~oye yac ce mallama fa ki agazan,

Don Allah don ilminki kar ki fa]e ni.

59

263. Wannan da anka fa ba ha}i}an ya’ aje,

Shi Fam talatin wallah yac canye mini.

264. Shi ma ha}i}an yaj ji tsoro na shiya,

Yab ba ni Fam sittin da kau lallashi.

265. Da]a nan shari’a tat tsaya nan tam mutu,

Nib ~oye fam sittin ga mai dukkani.

266. Shi ak Khalil wallahi mai dukkani,

[an Nafa]awa mai tsaron imani.

267. Niz zo ni Talha inda kawun Arfa tau,

Har inda Alhaji mai fa fara’a zahiri.

268. Nis sami mallan Sada ]an Modibbo ji,

Jikan fa gwaggo da baffa mallam Joni shi.

269. Modibbo gwaggo Hajoro yaf fa ubana,

Sarkin Gaya badikko Garba na joni.

270. Niz zo ga kawun Arfa Alami na Ahmadu,

Taro na dangi zay yawan addini.

271. Niy yo wata fa biyat ina tabsiri,

Tamkaf fa Sakkwato sun yi bege na fa ni.

272. Har kau Yagudun Mowa haifen kawu nau,

Shi na Hayatu Na’inna babba ga ilmi.

273. Fara’a da kyauta ga zumunta ga fa kyau,

Ta gadi Mowa da kawu har da Sa’idi.

60

274. Halin Sa’idu gare ta kyauta Ahmadu,

Ilmin Hayatu, kyau na Matar modi.

275. Dud dut jama’a tamu dangi sun gamu,

Da]a Alhaji yas so shi zaunasshe ni.

276. Nik ko }iya musu nit tafowata niya,

Kukansu matan Bello har wasu har da ni.

277. Yab ba ni Fam biyu har da takalmi ku ji,

Ga kau fa fara’a nasihi ga hankali.

278. Bayan fa an komo zumunta Talha kau,

Niz zamni Barta wata tara Sudani.

279. Ni ban yi aiki ko guda ba ha}i}atan,

Sai dai du’a’i sai fa kau {ur’ani,

280. Ban zo ga kowa Rabbu yaf fa isam mini.

Don na ri}e Allah da kau fa Muhammadi.

281. Da]a Abdu yaz zo Makka yat tanbai ni,

An ba shi labari shina haramaini.

282. Sai yai azanci Rabbi Allah Yah hana,

Na gode Allah na yi gadon mallami.

283. Yab ba da Fam minya wa khamsin kun jiya,

Har kau da Fam shidda a kai su gare ni.

284. Sun tarbe kur]i su fa zalimman }asa,

Sun canye kur]insu fa can Sudani.

61

285. Mallam fa manzona Badaure ya iya,

Wai Ingilizanci da cin fa harami.

286. Ya shekare da yawa ga Barta-siwaki nan,

Da]a sai da kur]in Abdu yai haramaini.

287. [an Ali dillalin fa Jakkan Sakkwato,

Shi yay yi }ara tai cikin Sudani.

288. Shai]an Abubakari na Helele kuma,

Babban ~arawo ga shi kuma dujjali.

289. Yac ce uwayenai fa kakanni muke,

Yag girka }aryatai da cin fa harami.

290. Shi yaf fa ]amrai yay yi shekarru biyu,

Ni ba ruwana na wuce haramaini.

291. Ni ba ruwana ban kula ba da su niya.

Ni dai kula da Muhammadu da Ilahi

292. Da]a Habsatu da fa Maryamu nis sa su, su,

Sun zo su Makka fa ni ina Sudani.

293. Ranad da duniya tai dufu ga Talata,

Ran nan suna can Maliya haramaini.

294. Bayan su niz zamna watanni ukku ni,

Ga wata na Sha’aban nis shigo haramaini.

295. Na zo ni Tokar inda manyan Dini kau,

Sun ban fa Fam ishirin fa ]ai babu feni.

62

296. Bayansu ha}}an ban bi]a ba a ba ni ba,

Da]a shekara biyu nis shigo haramaini.

297. Alhmadu lillahi fa jama’a ko’ina,

Allahu Yaf fore su nana gare ni.

298. Wa yarzu}hu min haithu la yahtasib,

Allah da Yaj ji]as ga Annabi nig gani.

299. Fa wa Rabbis sama’i wal ardi Allah Yaf fa]i,

Har can ilakh na kau fa gaskanta fa ni.

300. Ya ce tawwakal alayya fa mumini,

Wallahi riz}i nawa har Firdausi,

301. Domin sanin na kau fa amana Rabbana,

Har kau Rasulullahi har {ur’ani.

302. Alhamdu lillahi fa na ga fa a}iba,

Domin fa tasdi}i da nig gada fa ni.

303. Taron da sunka fa]i fa na yi hajijiya,

Sun dawwamo ga jiwa rashin imani.

304. Mi ar ruwana na ga maganay Yusufu,

Shi Annabi ]an Annabi Ya’}ubu ji.

305. Haka mallamina yaf fa]a min nashi kau,

Sirrin gidansu fa nana Sakkwato ya’ ishi.

306. Kun yo hasara kun fa daumu gare ta kau,

Domin alamata kama da ta mallami.

63

307. Alhamdu lillahi ga tawa jiwaniya,

Na sami albarka da kau fa tabarruki.

308. Kan’ana Yusufu yaf fito har can Masar,

Sababin husudi yaz zamo Sarkin gari.

309. Dibo Gwani Mukhtari Sarki mallami,

Mai tunku]ay ya}i na Allah salihi.

310. Sababin husudi yac ci kau Kukawa,

Shi af fa kakan mallamina adili.

311. Da]a yai takwas da wata takwas kwana takwas,

Yaf fid da ya}i jali yaz zam shahidi.

312. Dibo Gazarmu garinsu }ofa arba’in,

Doki dubu goma iri fa guda ku ji.

313. Aiki da anka yi don biyas son zucciya,

Mi yaf fa unfanam ma mai shi ba]ini.

314. Nir ranci Fam hamsin ga mai dukkani,

Nis sabka Jidda ina yabon rahmani.

315. Bisa kau fa Tayyara rabin sa’a jiya,

Da]a niy yi murna na iso haramaini.

316. Fam kau talatin anka ba ni rashin biyu,

Nig gode Allah nib biya da khalili.

317. Don ko fa an yi ragi ga wannan shekara,

Jirgi da Tayyara ga aikin Jalla shi.

64

318. Da fa ni da Habsatu har da Maryamu mun gamu,

Mun yo fa Hajji munka gode Jalla shi.

319. Alhamdu lillahi ha}i}an la fakhar,

Ni tau jiwa wallahi babu ma’asi.

320. Na tuba Allah am ka gafarta mini,

Domin alamata kama da ta walidi.

321. Domin fa hijrata kama da ta Ahmadu,

Ranaf fifatai Makka za shi Madina ji.

322. Wannan da yai sukaf fitata hasidi,

Shi ba shi aiki nan da kau tauhidi.

323. Nib bar Bagumbora fa ni kau nih hawo,

Don za ni tashi ta’ iso Sudani.

324. Nib bar amana tata inda mutan wurin,

Jama’a ta addini fa nan Sudani.

325. Nis sami Mani ]an fa Mallam Ahmadu,

Na fa Je]o nim maisai kama da Rufa’i.

326. Nis shekare nan Makka sannan nib bi]o,

Domin ta zo ta iso fa nan haramaini.

327. Nib ba da kur]i Jidda inda hukuma,

Da]a nan fa Sha’aban ta’ iso haramaini.

328. Ta zo ga Makkata ni ina fa Madinata,

Da]a taf fa sha kai anka kai ta gare ni.

65

329. Ranad da ta’ isa kau da ajali ta’ iso,

Da]a tai wata hu]u taw wuce zul}idi.

330. Bayan wucewat tasu niy yo Makka ni,

Sannan fa Fatume ta’ iso haramaini.

331. Ta zo da mallam kau fa Ibrahima nau,

Da]a tas shigo can Makka don she]anci

332. {arya zina haka nan ma’asi zahiran,

Sata ga kau fa maza cikin babban gari,

333. Wata ta Balaffoda fa Fatume ai take,

Ta amri Baban-Dudu Bazza taf fice.

334. Kwananta ukku gare shi ha}}an taf fita,

Nan Makka wai mata’ Abashe Waziri shi.

335. Saura fa Kande Bukhari as sauran fa tau,

Tafiya da tay yi nufin zaman Farlomi,

336. Sannan fa Kande tai ta~in da]a hankali,

Wallai na iskoki cikin Farlomi,

337. Nan mallamin jumla fa mallam Lab]o shi,

Yay yo takarda tai fa nana gare ni.

338. Domin fa nan nib bar amana tasu kau,

Domin fa ko wane lokaci zan aiki.

339. Nic ce shi yo mata kau dalilin Sakkwato,

Can inda dangi don ta san unfani.

66

340. Don babu Umma fa ni fa kau da]a na zamo,

Da]a babu hujja don ina haramaini.

341. Yay yo takarda ai fa shi da]a ya yi kau,

Domin dibara ta fa koma can giji.

342. Na gode Allah Wanda Yai baiwa garan.

Baiwa ta imani da kau {ur’ani,

343. Alhamdu lillahi khabarna la fakhar,

Bai furfura ni Ubangiji na rahimi.

344. Insha fa Allahu ina ro}o nasa,

Allah cika muna don fa Annabi [ahiri.

345. Allahu na ro}a Ka gafarta mini,

Fisshe ni dunya lafiya don dini.

346. Fisshe ni kandu Rabbi tsarsan makiri,

Har dud da Shai]annai aduwwan Ahmadi.

347. Sutura ta dunya har da barzahu lakhiri,

Domin fa labari ga tau don dini.

348. Da]a na gano ha}}an batun Modibbo nau,

Har addu’atai wadda yay yi gare ni.

349. Da batun da yai nis sadda}a da]a na gano,

Saura busharatai garan Firdausi.

350. Alhamdu lillahi fa Allah Yarhamu

Bisa ai fa Modibbo fa ]an Ashuri.

67

351. Allah Shi kai mu fa Jannatal Firdausi,

Can inda Fa]ima Sayyida ’yar Ahmadi.

352. Allah Shi ba ku zuwa bisa imani,

Allah Shi ba mu cika da husnul khatimi.

353. Haife ta ]an Modibbo Sarki adili,

Modibbo kawuna wurin Ashafa ni.

354. Allahu na ro}e ka sau fa dubu dubu,

Ka nufe ni in ga ]iya irin Ashafa ni.

355. Don mallama ta saliha mai hattara,

Kuma wofofo ka nufa da mu Firdausi.

356. Domin ]ala}atul }albi }urrin aini ta,

Ita rahatul jismi li ‘ya’ Ashafa ni.

357. Na zam asamun abkamun umyun jiya,

Domin bi]a fa ganin ]iya Ashafa ni.

358. Astagfirullahal azima Ubangiji,

Mun gode Allah mun fa gode Ahmadi.

359. Dunya fa banza ‘yan’uwa banza kuma,

Allah Shi lurasshe mu bin {ur’ani.

360. Domin fa Allah ni Ka gafarta mini,

Ajali fa ya sabko gare ni fa za ni.

361. Ya ku masoyana da ]alibbai, zumai,

Ku dut ku gafarta ni domin babu ni.

68

362. Aiki da niy yo ba]inina zahiri,

Domin Muhammadu za a gafarta mini.

363. Wa}ag ga tau a ta wanzu domin na tafi,

Can inda mai iko na Annabi Rahimi.

364. Ku dai ku yo min addu’a in kun zamo,

Halinku mai kyau don a gafarta mini.

365. Da kure da gangancin da kunka ri}an da shi,

In don kuna bisa kau fa hanya nasihi.

366. In kun }iya don kanku ni ban damu ba,

Na san ina da zaton zuwa Firdausi.

367. Na san fa na yi kiran ku kowa ya sani,

Halin da Yay yi gare ni ba da nifa}i.

368. Ni ba ruwana yau da komi don ku san,

Sai dai bi]af falala ta hanya Khali}i.

369. Ko can fa Allah Ya sani Ya shaida Shi,

Ni ba ni }in kowa bisa ga husudi.

370. Kuma ba ni }amnam mai fusudin ‘yan’uwa,

Mai }in fa muminnai bisa ga u}u}i.

371. Haka zan cikawa ba ni }amna fasi}i,

Mai cin amanonin musulmi makiri.

372. Mai son fa kai mai kissa zamba munafuki,

Mai }in jama’ar Rabbi ba shi da hankali.

69

373. Na yad da kayan ya-kamata na munkari,

Na yad da dunya mutanta domin lahiri.

374. Na yad da dunya inda masu bi]at ta nan,

Na ba su na zamna ga halin walidi.

375. Ni dai inai muku garga]i da fa fa’ida,

Har }a’ida ga batun zuwa haramaini.

376. Mai son shi yo Hajji fa don Firdausi,

In dai da iko jikkuna shika tattali.

377. Kur]i da nashi mutum na kainai na gaya,

Mai hankali mai }o}ari da fa tattali.

378. {arfi da niyya da ]ebe girman duniya,

Sannan shi zo bisa ]a’iri da tawakkuli.

379. Wannan da yai Hajji mujawirran gari.

Wannan da bai yi da]ai ku ce fa }ashimi.

380. Tamka mutum birni mujawirran gari,

Tamkam fa }auyawa }ashimmai don ku ji.

381. Su as Saraki manya–manya fa zalimai,

Su }ashimmai su fa }auyawan gari.

382. Komi amana tasu su fa mujawirai,

Hanya ta Hajji kau ashimmai kun boni.

383. Suna Saraki, zalumai fa munafu}ai,

Ga fa cin harami in da }auyawa ku ji.

70

384. Ko da miji mata abutta ta kawu,

Nan Makka Hajji }ashin su tsorci mujawuri.

385. Ko mallami ko jahili attajiri,

Ko da Saraki sai su zam azzalumi,

386. Domin su canye dukiyakka fa zahiri,

Sannan su jefo ka ga kau wahaloli,

387. Su ba su kumya ba su tsoron Rabbana,

Ga kau }iyayya inda Annabi zahiri.

388. Sai daffa’awa dukiya ga hukuma,

Amsak ku Jidda shi zam kuna bisa ]a’iri.

389. Ni nai misali zahiri fa da ba]ini,

Domin ku niy yo ku fa }auyawan gari.

390. Ko ‘yan ]iyanku da kau fa mata Makka kam,

Ku af fa gonakkinsu ‘yan Hajji ku ji.

391. Ku Sakkwatawa naku kur]i sun tsaya,

Nan Yarwa domin Ingilizi kunka bi.

392. Dak kau fa Farlomi }asaf fa Faransa ji,

Su nasu kau fa daban Jinai na fa don ku ji.

393. Su kau Lubayya ku san fa har fa Siwaki kau,

Su nasu Sudani daban suke don ku ji.

394. Daj Jidda har nan Makka har kau can Riyal,

Su a ’ Su’udiyya cikin babban gari.

71

395. Na yo misali don mutum fa da nashi kau,

In kun }i amsa ku zam cikin danasani.

396. Domin fa zamani kusan ya birkice,

Da]a ba amana nan ga kowa ta tafi.

397. Mai kau nufin khairi da sharri kowane,

A shi san mafificinsu nan haramaini.

398. Kada kau shi ]au komi fa komi na nana,

In don fa kun amso batun haramaini.

399. In ba dibara ba tawakkuli ba sabur,

Kun ]auki wahaloli ga yin haramaini.

400. Insha fa Allahu ku zamni garinku kau,

Kullum da niyya taku har can lahiri,

401. Wannan da ya} }i fa han}uri har gaskiya,

Ya kau }i ai fa nasa’ihi na Mu}addari.

402. Kuka shi kai sannan shi ce dayasani,

Namijin-gari na Makka ba shi da tamkaci.

403. Domin fita dam Makka can fa zuwa Mina,

Shi aw wuyah Hajji ku lura da }auli.

404. Da zuwa ga Arfa da kau fa jifa na fa]i,

Sa’ayi, [awafi na fa]e shi da hamzari.

405. Sai dukiya da fa naka yaro na fa]i,

Tamkas sira]i na fa cana ga lahiri.

72

406. Ba don fitowa Hausa zakkuwa Makka ba,

Shi ba jidali na zuwa haramaini.

407. Amma ina kau ba ku sirri ‘yan’uwa,

In babu wauta ku yi shiri bisa hamzari.

408. Kuma kau ku zam bisa tattalin guzuri ku bar,

Wauta ga yin tafiya da ba ta da kau shiri.

409. Don rad da Sarkin kau Musulmi yaf fito,

Kowat tsaya da]a yai hasara lahiri.

410. [an Shehu ]an fa Mu’azu ]an kau Bello na,

[an nan na Shehu mujadaddi Usmani.

411. Shi an na sha fa bakwai da kau fa mujadaddi,

[aki na Bello fa]in da yay yi mujaddadi.

412. Komi fa zamani fa]in fa mujadaddi,

Wallahi bai tashi fa nai tasdi}i,

413. Domin fa halin nan da anka nufo na yau,

Sai dai a ]au da]a han}uri da tasabburi.

414. In ya }iya nan Makka babu nasa’ihi,

Halin a she}o Makka yai ga mu}addari.

415. Amma ga mai hijira da ya] ]au wakkala,

Yas sai da dunya yab biya Firdausi.

416. Ga irin misali nan awa ni la fahar,

Na sai da dunya na sayo Firdausi.

73

417. Na ro}i Allah Jallah na yi tawalu’i,

Allah Ka tsarshe ni da kau She]ani.

418. Domin ina tsoron Ka Allah Rahimi,

Rahamakka niy yi zato ina tsoron Ka ni.

419. Kuma babu cilas Rabbi ba don nau hali,

Rahamakka ta fi sama }asa don Ahmadi.

420. {arya da girman kai da alfahari ku san,

Su bugun gaba sun kau su nan haramaini.

421. Izza sarauta yakamata da son isa,

Dubin fa asali babu dut haramaini.

422. [an wance na ]an wane ba shi zaman haram,

Sai dai zalilin nan da yay yi tawakkuli.

423. Ara~~e da iri na Ara~~e Shiriffai har Badur,

Sun ya da girma don isa haramaini.

424. Aiki sukai safara tutut komi nana,

Domin fa girman Makka sai miskini.

425. Sarki talakka da mallami sa jahili,

Bawa da ]a daidai zaman haramaini.

426. Komi fa girman naka ka’ isa Makkata,

In babu imani kana kafirci.

427. Wasu aika tabarmi da tsawwa wansu kau,

Da murawufi tallar ruwa wasu kai su ci.

74

428. Wasu inda Ara~~e zaman wanki tutut,

Wasu kau jidak kaya a ba su ijari.

429. Amma karatu har da ilmi ba su so,

Sai dai na boko ba su son addini.

430. Da bugun }asa arwa da lu]u da shan giya,

Bori da bokanci da anka }i dauri.

431. Gurumi da tsafi ga fa goge bayyane,

Gumki da isha}i cikin babban gari.

432. Sharri na dauri da anka kore tawa am,

Dut ya fa komo babu kau imani.

433. Tun Jidda Makka da [aiba har can kau {udus,

Dangi na kufuri Sham da Istanbuli.

434. Don ba ruwan kowa da Allah Rabbana,

Bidi’a ga mallamai da limamman gari.

435. Har duk da Al}allai Sarakin duniya,

Hakanan talakkawa da jahillai ku ji.

436. Da]a mun yi ai fa ta}o–ta}o tun duniya,

Mi a’ isam mu zama da la’anannin gari.

437. Da]a babu tausai babu jin}ai babu so,

Fiski da }arya mumini shi ya boni,

438. Da]a mun gano ha}}an alamam Mahdi kau,

Saura fa tsawan nan ta kau Jibirili.

75

439. Da]a barakallah babu tamkam Makkah,

Sharri da alkher nan cikin babban gari.

440. Amma fa Allah Rabbu Yai mata ]aukaka,

Allah tsare mu shi ba mu husnul khatimi.

441. Ke ab badalin tau ]iyak Kilo saliha,

Mai hattara domin ki niy yi da hamzari.

442. Dominki nif fa fa]i ki lura da nau batu,

Da irinki mai halin sanin addini.

443. Allah da Annabi har da Al}ur’ani,

Yau babu mai }amnassu balle mumini.

444. Balle zumunta muminai kam babu ta,

Sai fasi}ai sai dukiya suka tattali.

445. Mallam fa Mahmudu kau fa Muhammadu,

Har dud da ]anai har Amina, Safiyya ji.

446. Da ]iyak Kilo har Shekhu, Maryam, Kabo ni,

Da Sule da ke da fa Mus]afa har Bello shi.

447. Da Atiku, Faruku da Tambari nawa ji,

Allah Shi gafarta mu domin Ahmadi.

448. Allah Shi gafarta Shi sa mu cikin shiri,

Allah Kasa fa da mu zuwa Firdausi,

449. Har duk da Mallamanmu, ]alibanmu kau,

Amma fa masu fa sonmu don addini.

76

450. Jama’a ta al’ummam Muhammadu Ahmadu,

Su dut fa mai aiki da Al}ur’ani.

451. Wallai ubana sahibin Maibera na,

Wajjen uwa Maibera kawuna ku ji.

452. Ita ko fa jikanya ta Nuhu ]iyak Kilo,

Ita ta ]iyaj jikan zawul arhami.

453. Ke so ni bayan tawa }eya Fa]ima,

Ke so fa Kabo da Shehu bayyane na fa ji.

454. Na tabbata ke ta ]iyad dwatti~e,

Na tabbata nononki bai da nifa}i.

455. Allah Shi sa ki ishe ni ha}}an in gani,

Allah Shi kawo ki cikin haramaini.

456. Allahu yaf fa tsare ki babu nifa}i,

Ke Fa]ima ]an Sambo ]an Ashafani.

457. Ya ba ki Ya yardo da ke ‘yam Murtala,

Kakanki Sambo waliyyi ]an Ashafani.

458. Ba don da Allah Rabbi Yai min baddali,

Ciyo na khabarin Hausa sai shi ishe ni.

459. Alhamdu lillahi da Kab ban Fa]ima,

Badalin ]iyata har miu zo Firdausi.

460. Kwas so ki billahillazi ya so ni, ni,

Kwa} }i ki ban }amnas shi zo Firdausi.

77

461. Ke zam dabinon zucciyata khaliliya,

Na gode Allahu da Yab ban ke fa ni.

462. Kwas so sha}i}}ai naka kai yag girmama,

Kwa} }i su kai na ya} }iya mal’uni.

463. Domin fa taron fasi}ai la’ananni,

Don ba su kumya ba su son kau Ahmadi.

464. Domin }iyayya kau garan ta taz zama

Allah ka la’ane su ka sa su ga tasari.

465. Ni na yi bankwana da ]akin duniya,

Da abin da ab bisa duniya don Ahmadi.

466. Ha}}an batun Usmanu mun ga shi bayyane,

Nan Makkah ya kau bayyano na

Mujadaddi.

467. Balle gida ko da wurin bukka ga yau,

Aka sai shi jikka mai yawa da da]i-da]i.

468. Ni dai jawabina shina bisa masu so,

Nau wanda sunka kula da nau tasdi}i.

469. Don }ila }arshena ga tau maganag ga tau,

Allah Shi yarda da mu Shi ba mu shiga shiri.

470. Na }are labarin fita ta Sakkwato.

Na ba ku labarin zaman Haramaini.

471. Kowa ha}i}an ad da nashi cikin wuri,

A shi sami labarin fita }auyanci.

78

472. Na ba ku labari ka]anna ha}i}ani,

Domin ku yo harama fita }auyanci.

473. Ai barakallah babu tamkam Makka kam,

Ita a} }iyamat wanda ba shi da Dini.

474. Alkher shina nan inda mai imani,

Ita kau wuya na nan fa inda munafuki.

475. Ga dubu–dubu nib ba ku ]an fa ka]an ku ji,

Domin ku ]auki shiri zuwa Haramaini.

476. Balle Munawwara inda Annabi Ahmadu,

Mai ba da shawa inda mai addini.

477. Ni ajiza ta nan ga lisafi ku ji,

Na ba ku labar ]an ka]an Haramaini.

478. Son kai da zamba da cin amana ba su yi,

Shewa da yangad duniya Haramaini.

479. Balle fa raggo, wa ka duba mai isa?

Shi ad da }as}asci da kau yin woyi.

480. {eta da kissa kaza da makirci jiya,

Wauta da hauka ba su yi Haramaini.

481. Shi yak kamata da kau fa alhormomi,

Sai dai a bar ka zaman ka kau ma]rudi.

482. Rana ta Lahadi ni’iso ran nan Kano,

Ra’Attanin Daje taw wuce Haramaini.

79

483. Sittin da biyu na ag gare ta watan Rajab,

Da]a taw wuce ishirin garai Haramaini.

484. Ta zo wata na Rajab fa ta koma garai,

Ga watan da [ibgau yaw wuce na Mujaddadi.

485. Jinya watanta tara tana ciwon ciki,

Amma da tsabta taw wuce Haramaini.

486. {assa da fata anka kai can Mala,

Tamkaf fa ciwon kau ubanta fa mumini.

487. Toka, Turare, Likkafan dut ta gama,

Nan }ar}ashin kai anka ce Haramaini.

488. Har hankali, kalima tana yi sunka ce,

Da fa sunka bar ji sunka san da]a ta tafi.

489. Sun ce jikinta kama da zannan Alharin,

Tafshin jiki, haiba da kau imani.

490. Babal Ati}i anka kai ta fa Maryamu,

Nan gun Ma}aman nan ta kakan Ahmadi.

491. Da]a kanta As’wadu nan }afafun can Ha]im,

Ban nata Zam-zam shi gaba na Multazim.

492. Bisa godaben Aljanna Limam yai mata,

Sallah da jama’atai cikin Haramaini.

493. Rakiyam Musulmi da rahma har Babas-salam,

An kai ta Mala can cikin Haramaini.

80

494. Madalla Maryamu ta yi samu mai yawa,

Ta gadi Jewun Ahmadun Al}ali.

495. Ita tata ai fa hajijiya ta zam rabo,

Saura fa ni in wurgo can Firdausi.

496. Ta ]au kawaici sai fa tasbi tar ri}a,

Bayan fa ta komo bi]af fa halali.

497. Dibo fa Habsatu ta ga hikima zay yawa,

Don ta ga A’isha har magaryan nuri.

498. Dibo Bagumbora da ajalin nata duk,

Kullum tana harda ta Al}ur’ani.

499. Allah Ka gafarta gare mu da su duka,

Allah Shi sa mu mu taru can Firdausi.

500. Niz zo Madina Munawwara nish shekara,

Da]a Umma ta fa wuce Jimadal awwali.

501. Hakanan Bagumbora fa dut sun ribata,

Can kau Ba}i’a inda ]an Affani.

502. Ni kau ina nan inda mai ni yan nufa,

Kullum ina dubin zuwan Izra’ili.

503. Allah Ka sa da]a in cika bisa muminai,

Allac cika muna kau bisa imani.

504. In don fa Allah Yai nufi na tun azal,

Wankanta nana garan ta zo Haramaini.

81

505. Na bar fa za~i inda Allah Rahimi,

Allah Ka sa ni zama cikin Firdausi.

506. Domin fa bawa mai fa kau tauhidi,

Shi ba shi za~i sai fa za~in Rahimi.

507. Na tuba Allah am Ka gafarta mini,

Kai ad da ni Kai ad da rahma Gafiri.

508. Ni dai ina ro}on Ka ba ni tawalu’i,

In kau cika bisa ai fa hanya’ Ahmadi.

509. Alhamdu lillahi ga nawa gane-gane,

Na ro}i Allah don Shi ban Firdausi.

510. Taron uwayena da kakanni duka,

Har dut masoyan nan da sunka bi Ahmadi.

511. Ro}on fa ‘yab boyakka ‘yab bawanka shi,

Mallam fa Mahmudu fa ]an bawanka ji.

512. Ashuri shi na ]an Gwani Mukhtari ji,

Bawanka ]an bawanka Musa Gwani ku ji.

513. Na ce a baya Ati}u nawa mubarakun,

Insha fa Allahu shi samu tabarruki.

514. Da Gwani fa Mahmudu, Gwani Mukhtari ji,

Su ko sha}i}aina ]iyan Musa Gwani.

515. Wallahi har tallahi toro]o na jiya,

Su ‘yan’uwan Shehummu babba mujaddadi.

82

516. Su af fa Baranbo, Misawa kun jiya,

Suna Dilarawa da Marawa ku ji.

517. Sarki na Baranbo Ati}u da Bello ji,

Al}ali liman muminin sodore.

518. Sarkin Katagum Nafa]a Sarkin Shira,

Sarki Sulaimana na Shehu uban gari.

519. Sarkin Gaya mallam fa Garba na Joni,

Shi af fa ]an kau Adamun Baranbo ji.

520. Sambon Ha]ejiya har da Bubakari ku ji,

Mai kau Kazaure da yas shige Katsina ku ji.

521. Modibbo Sarkin Adamawa kun jiya,

Har dud da Sarkin Gombe Sambon Shehu ji.

522. Shi Hashimi na cana walla gidansu ji,

Dud dut fa kakannin ubana kun jiya.

523. Dangin masoyana na Makka da ]alibai,

Sun ce suna gurin ganin mai ilmi.

524. Wannan da yaz zamna bi]a ta Makkata,

Jarwat ta Karu na Tundubawi zai bi]i.

525. Wajje na ]an Sarkin Musulmi shahidi,

Maifaggo }ofan nan ta kau Firdausi.

526. Attahiru ]an Ahmadu na Ati}u shi,

[an nan na Shehu mujadaddi Usmani.

83

527. Nan kau gidan Shehun Rubu’i kun jiya,

Hara ta Sakkwato nan ga ]an dukkani.

528. Nau kau fa Inwani fa Modibbo Kilo,

Ita a] ]iya’ Al}ali kau Mahmudi.

529. Wannan na Sakkwato, kuma wakilina niya,

Shi am Muhammadu Ya Rasulullahi.

530. Kishi na Allah wanda Yay yi gare ni,

Tun Sakkwato har Makka Ya fa tsare ni.

531. Don Ya hana min yin wanin su gare ni,

Alhamdu lillahi ga zatinai fa ni.

532. Da]a niz zamo ya kau hana ni fa kulla sha’i,

Ya ban Muhammadu Sidi ga {ur’ani,

533. Na tuba Ya Allah Ka gafarta ni, ni

Kai ad da ni Sarki Karimi Rahimi.

534. Wannan da yaz zam na bi]a ta Makka yau,

Hartal Yamal shiyya fa Umda’uza’i.

535. Wannan da zai fa bi]ag gidana kun jiya,

Da]a kassuwa’ ‘Yabbarno Jarwal zai bi]i.

536. Sannan shi tambayi kassuwa Hartal yamal,

Shiyya ta Umdan Jarwali fa Kuza’i.

537. Ita kussawa ta gawai ka ba da itatuwa,

Kuma ga fa cana hakukuwan dabbobi.

84

538. Kuma ga Masallacinmu ai fa na jami’i,

Kuma ga fa Tafona da jan dutcin wuri.

539. Kuma ga gidan Umda da ba zani wurin

HartalYamal ke nan misalina ku ji.

540. Sannan shi ce fa ina gidan Modibbo kau,

‘Yas Sakkwato Modibbo mai tafsiri.

541. Wannan uwa] ]akin fa Kurma Maryamu,

Ita a] ]iya’ Al}ali Sakkwato murshidi.

542. Sai kau a nuna mai gida bisa dutci,

Khalga da jan dutci fa yamma ga nau wuri.

543. Sa duk da takona da ba zanen wuri,

Har kau gidan Umda fa yamma gare ni ni.

544. Allah Shi gafarta ma mallamanmu kau,

Hakanan da waliddai da mu da zumammu ji.

545. Hakanan fa kakanni, masoya, ]alibai,

Amma fa khuddamammu masu fa som mu ji.

546. Hakanan fa al’umma ta Annabi Arabi,

Wallahi masu biya ga sunna Arabi.

547. Hakanan ]iyammu da sunka so mu da ‘yan’uwa,

Hakanan ma}wabta masu son {ur’ani.

548. Da]a na ciko kau alkawal fa da niy yi ni,

Domin fa rai ya kai zaman Haramaini.

85

549. Dibo fa Fa]ima mallama a ki lura ke,

Domin dabinon zucciyata ke fa ni.

550. Ga dubu-dubu nib ba ki silale guda,

Don ba iyaka nan ga kau Haramaini.

551. Allahu Sarki Wanda Yay yi Muhammadu,

Yab ba shi Makka ku san fa sirri sai fa shi.

552. Na yo salati ga Ahmaduna Annabi,

Har kau Sahabbainai da Allainai ku ji.

553. Har kau da Tabi’i-tabi’inai su duka,

Shi Hashimi fa na Makka har da Madina ji.

554. Ramzi na Hijiratai fa Minyasalasata,

Da alif da saba’in har fu]u na Muhammadi

555. Tammat bi hamdillahi ni kuma na tsaya,

Da nufi na Allah nan ga kau Haramaini,

Tammat bi hamdillahi wa husni aunihi.

Allahummagfir walidiyya wal sami’ul muminina wal

muminati

86

Nazarin Wa}ar Al}ur’ani

Modibbo Kilo ta rubuta ‘Wa}ar Al}ur’ani’ ne ranar

Jumu’a 22 ga watan Jimada Awwal na shekarar Hijira

ta 1379, wa}ar da ta ce tana zaton ita ce autar wa}a a

wurinta. Ga abin da ta fa]a a cikin wa}ar.

Ishirin da biu ga fa ai Jimada lawwali,

Nit tsara wa}ata zuhur Jum’a jiya.

A cikin sana da]a goma sha ]ai Makkata,

Shi’iri da niy yo nai zato autaniya.

Tammat bihamdillahi ni kam na tsaya,

Don walla tari niy yi niyya in gaya.

Ramzi na Hijira Annabina nig gaya,

SHASA’A[U bana ai cikaf fa habisiya.

Wannan wa}a tana da ]angogi sittin da uku (63). Ta na

kuma ]auke da amsa-amon waje, wanda yake }arewa

da ‘ya’ A cikin wannan wa}a Modibbo ta yi yabon

farawa da na rufewa. Yabon farawa yana }unshe a

cikin baiti na 1-7 inda ta fara da ambaton Allah

(subhanahu wa ta’ala), sannan ta yi salati ga Annabi

Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) da sauran

Annabawa da Alaye da Sahabbai. Hakanan ta yi godiya

ga Allah Ma]aukakin Sarki da ya arzurta ta da sanin

Al}ur’ani da ma’anarsa da kuma yin aiki da shi da

sanin }issoshin bayin Allah managarta, wa]anda aka

ambata a cikin Al}ur’ani. Ga baitocin da ke ]auke da

bayanin haka:

87

Bismil ilahi zan bi]a Allah nufi,

Wannan da yay yi shi bayyana min gaskiya.

Alhamdu lillahi fa na gode mishi,

Na yo salati ga Annabi nai godiya.

Na yo salati ga Alu, Sahabu, Anbiyah,

Ya ba ni {ur’ani inai mai godiya.

Ya ba ni in fita inda }ulu la’ilah,

Asalin uba da uwa ina yin godiya.

Na gode Allah Ya fa ban {ur’ani,

Har kau da }issoshi ina yin godiya.

Ya ba ni aiki kau da Al}ur’ani,

Ya ba ni jin ma’anarsa Ya ban godiya.

Alhamdu lillahi ha}i}an la fakhar,

Kuma ni ina fa zaton shiga Fartaniya.

Daga nan Modibbo ta ]aura ]amarar shiga jigon

wa}arta inda ta yi bayanin cewa:

Ni za ni shi’iri Rabbu ba ni abin nufi,

In bayyana ga nufi zama nai godiya.

Wa}ar ta zo ne game da bayanan abubuwan da ke cikin

Al}ur’ani mai girma, wato abin da ya shafi surorinsa da

kalmominsa da haruffansa da ayoyinsa da hizbi-

hizbinsa da sumuni-sumuninsa da sujadodin karatunsa,

wato wuraren da ake yin sujuda. Hakanan ta kawo

88

yadda ake yin kabbarar ta hanyar kai goshi }asa, a yi

kabbara a ]ago, amma sai tare da alwala ko da taimama,

ga duk mai karatun Al}ur’ani. Hakanan ta

ambaci }ira’a ko nawa ce wajen karatun Al}ur’ani da

sauransu.

A wannan wa}a Modibbo Kilo ta fara da kawo

ta}aitaccen bayanin abin da Al}ur’ani yake ]auke da

shi kamar haka:

i. Kalmomin Al}ur’ani guda 1,300,000

ii. Haruffan Al}ur’ani guda 263,200

iii. Surorin Al}ur’ani 114

iv. Hizbin Al}ur’ani 60

v. Sumunin Al}ur’ani 480

vi. Ayoyin Al}ur’ani 6,666

Modibbi ta nuna abubuwan da ayoyin nan 6,666

suka }unsa, ta karkasa su zuwa kashi–kashi kamar haka.

i.Aya ta 1,000 ta }unshi Amri (Horo)

ii.Aya ta 1,000 ta }unshi Nahyi (Hani)

iii.Aya ta 1,000 ta }unshi Wa’adi (Alkawari)

iv.Aya ta 1,000 ta }unshi Wa’idi ({yacewa)

iv.Aya ta 1,000 tana ]auke da {asasu da

Akhbaru ({issoshi da Labaru)

v.Aya ta 1,000 mai ]auke da Ibaru da

Amsalu (Luraswa da Misalai)

vi.Aya ta 500 ta }unshi Halal da Haram da

Yamini wato (Rantsuwa)

vii.Aya ta 100 ta }unshi Du’a’i da Tasbihi (Addu’a da Tsarkake Ubangiji)

viii. Aya ta 66 ta }unshi Nasikhun da

Mansukhun

89

Ga baitoci, a inda wa]annan bayanai suka fito:

Don yai kalimomi dubu fa ]ari uku,

Da dubu ]ari tara har fa dubu ]ari ]aya.

Sannan haruffa nan dubu fa ]ari ]aya,

Da dubu fa saba’in dubu sittin jiya.

Hakanan kaza fa dubu fa talatin na biya,

Da dubu fa ukku kaza ]ari biyu yat tsaya.

Sura ta {ur’ani ]ari fa da goma sha,

Fu]u har da hizbi nashi sittin na gaya.

Sumuni ]ari fu]u na tamanin na bisa,

Na gode Ahmadu na fa gode mai niya.

Aya dubu shidda, ]ari shidda bisa,

Sittin da shidda suna biya, mu yi godiya.

Aya dubu ku sani batun amri sukai,

Su kau dubu nahyi sukai mu yi godiya.

Aya dubu wa’adi dubu fa wa’idi,

Su kau dubu }isasu da wal ahbaniya.

Aya dubu ibaru fa wal amsalu,

Na cimma sittu fa alfu, na yi fa godiya.

Zan bayyana muku ni]ari fa biyat ku ji,

Raba kau haram da halat yamini na gaya.

Aya ]ari da guda du’a’i tar raka,

Har dud da tasbihi ku zan yin godiya.

90

Modibbo Kilo ta bayyana wasu abubuwa da dama da

ake samu a cikin Al}ur’ani mai tsarki, kamar su

haruffan ]auri da haruffan da ba a yi musu ja ga karatu

da madda da jan]e. Ta ce haruffan ]auri 7 ne wato

‘Agun’ ‘Kha’un’ ‘Hawayyu’. Haruffan da ba su da ja 5

ne, wato ‘Hayyu Rah]in’, haruffa 8 su ne na madda

wato ‚Ma}sun, Aslukumu‛ zakuwar madda harafi 3 ne

‚Siddi da Hamza da Fuyi‛ jan]e wasali sama 2

wasali }asa 2 turi 2, ana samun su a haruffa bakwai,

amma Modibbo ba ta ambace su ba. Baitocin da

suka }unshi wannan bayani su ne:

Mai ]amre {ur’ani fa harafi na bakwai,

Agun, kha’un, hawayyu, ramzi godiya.

Wannan da yaf fa hana ma {ur’ani fa ja,

Harafi biyat na, hayyu rah]in ramziya.

Mai sa shi madda ai fa harafi na takwas,

Na}asun da aslukumu fa ramzin maddiya.

Zakuwa ta madda nan fa harafi ukku na,

Siddi da Hamza, Fuyi ku lura da godiya.

Mai sa fa jan]e bisa tafowa daidai,

Jan]e }asa biyu, kai ku lura da anniya.

Da turi biyu da]a mai hawan juna jiya,

Harafi bakwai na, don ku lura da gaskiya.

Su kau ka kunya inda ba nan yab biyo,

Jan]en ga ukku ku sa ma {ur’an anniya.

91

Harafin da yaf fa biyo fa harafin Siddi shi,

Sai bai kalami nashi na fa ga siddiya.

Haka kuma Modibbo ta ambaci cewa }ira’a, guda 12 ce,

sai dai ba ta sami kawo su ba. Ga maganar cikin baiti

na 32

Kuma kau }ira’a goma sha biyu ag garai,

Wa}afi da ya fa, fa jan]e ha}}an mai wuya.

Modibbo ta ambaci abin da ta kira kututturan Al}ur’ani

amma ba ta yi bayanin su ba. Ta fa]i ‚samma‛ 3 da ke

cikin Al}ur’ani ‚Khalidaini‛ ‚Auliya‛ da ‚Ula’ika‛. Ga

bayanin jerinsu a wa}e:

Sannan kututturai na Al}ur’ani,

Wannan da ba a sani fa, sai na}ali jiya.

Kuma samma na nan ukku fil {ur’ani,

Kuma khalidaini guda ga {ur’an nig gaya.

Kuma auliya, ula’ika shi ]ai shike,

Da yawa kamas su da ni} }ara tsari niya.

Dangane da bayanin wuraren da ake yin sujada lokacin

karatun Al}ur’ani, Modibbo ta kawo wuraren ta kuma

ce, ana yin sujadar ne da taimama ko da alwala.

Hakanan kafin yin sujudar ana fara yin kabbara.

Bari a fara duba duk wuraren da ake yi wa sujada

a cikin Al}ur’ani, kafin a dubi wuraren da Modibbo ta

kawo. Wuraren su ne:

92

i. Surah Al-A’raf aya ta 206

ii. Surah Ar-Ra’d aya ta 15

iii. Surah An-Nahl aya ta 49

iv.Surah Al-Isra’ aya ta 109

v. Surah Maryam aya ta 58

vi. Surah Al-Hajj aya ta 18

vii. Surah Al-Hajj aya ta 77

viii. Surah Al-Furqan aya ta 60

ix. Surah An-Naml aya ta 25

x. Surah As-Sajadah aya ta 15

xi. Surah As-Sad aya ta 24

xii. Surah Al-Fussilat aya ta 37

xiii. Surah Al-Inshiqaq aya ta 21

xiv.Surah An-Najm aya ta 62

xv. Surah Al-Alaq aya ta 19

A wa}arta Modibbo Kilo ta kawo wurare cikin surori

wa]anda ake yin sujada a cikinsu a baiti na 38 zuwa 41

kamar haka:

Kuma kau Sujuda goma sha bi’u na gaya,

Wannan da za a fa yi ga Al}ur’aniya.

Sajada ta farko can cikin La’arafu,

Ra’adu, Ate, Subhana, Maryam na gaya.

Diba ga Zalzala zo ka can Fur}ana,

Can inda Namlu wuce cikin Laraiba ya.

Har Sad da Hemem Fussilat, goshi }asa,

Ka yi kabbara bisa taimama da wulu’iya.

93

Daga wa]annan baitoci, za a fahimci cewa Modibbo

Kilo ta kawo wuraren sujada guda 11ne kamar haka:

i. Surah Al-A’raf

ii. Surah Ar-Ra’d

iii. Surah An-Nahl wadda ta kira Ate

iv.Surah Al-Isra’wadda ta kira Subhana

v. Surah Maryam

vi. Surah Al-Hajj wadda ta kira Zalzala

vii. Surah Al-Furqan

viii. Surah An-Naml

ix. Surah As-Sajadah wadda ta kira Laraiba

x. Surah As-Sad

xi. Surah Fussilat wadda ta kira Hemem Fussilat

Idan kuma muka yi la’akari da baitocin , za mu ga cewa,

duk da Modibbo ta ce wuraren da ake yi wa sujada 12

ne, amma bisa dalili na hilafar malamai sai ta kawo

goma 11 kawai. Kafin a kawo bayanin abinda ke cikin

baitoci na sama, zai yi kyau a fahimtar da mai karatu

cewa, a mazhabar Imam Malik wadda ita Modibbo ke

bi, makruhi ne a yi sujada a wuraren sujada na Suratul

Hajj sujada ta biyu da Suratun Najmi da Inshiqaq da

Qalam. Wannan shi ne dalilin da ya sa Modibbo ba ta

ha]a da wa]annan sujadodi ba a cikin lissafinta.

A wasu wurare kuma, maimakon ta ambaci

sunan sura, sai ta kawo wani abu da zai sa a gane surar,

misali Suratun Nahli da ta kira Ate, saboda yadda surar

ta fara da ‘Ate amrullahi’ da Suratul Hajj wadda ta kira

Zalzala saboda kalmar ‘zalzalata’ da ke cikin aya ta

farko ta surar da Suratus Sajada wadda ta kira ‘Laraiba’

saboda kalmar laraiba ta fito a cikin aya ta 2 ta surar da

Suratul Fussilat wadda ta kira Hamem Fussilat saboda

aya ta farko ta surar ta fara Hamem.

94

Bayan Modibbo Kilo ta }are bayani a kan

wuraren da ake yin sujuda a cikin Al}ur’ani, sai kuma

ta ambaci wa}afi 7, wa]anda ake samu a cikin wasu

surorin Al}ur’ani maigirma, inda ta fa]i cewa, ya zo ne

cikin surorin Ali-Imran da An’am da A’araf da Taubah

da Yasin da Fathu da Tahrim da Muzammil. Bayanin

ya kasance a baiti na 47 zuwa 49 kamar haka:

Nan Ali Imrana wa}af yaf faru shi,

Na biyunsu fil An’ami kai ku yi tambaya,

Sannan ga La’arafu na ukku tsaya ka ji,

Na fu]unsu nan ga fa Taubata kai ka jiya.

Na biyat ga ai fa Yasin na shidda ga Fathu kau,

Na bakwai ga Tahrimi, Muzammilu thamaniya.

A baiti na 50 da 52, Modibbo ta shiga na]e wa}arta da

fa]in ita ajiza (gajiyayya) take, don haka ba za ta iya

bayyana kome da kome ba, amma tana ro}on Allah Ya

kar~a mata, Ya kuma ba ta ladar wannan ]in da ta

kawo. Ta kuma ro}i Allah da Ya arzurta musulmi da

ganin Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam)

ranar tashin al}iyama da shiga Aljanna Firdausi.

Hakanan ta ro}i Allah shi aurar da ita ga Hassan ]an

Sayyida Fa]ima da Aliyu bn Abi [alib.

A baiti na 53, Modibbo Kilo ta sa wa wa}arta

hannu da nuna cewa, ita ]iyar Al}ali Mahmuda ce ta

rubuta ta.

A }arshe, baiti na 61 zuwa 63 ta fa]i ramzin

wa}ar wato SHASA’A[U wanda ya ba da lissafin

1379 na hijirar Annabi Muhammadu (sallallahu alaihi

wa sallam), ta kuma yi godiya ga Allah da salati ga

95

Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) da

Alayensa da Sahabbansa. Ga baitocin kamar haka:

Ramzi na ‘Hijira’ annabina nig gaya,

SHASA’AXU bana ai cifaf fa habisaya.

Alhamdu lillahi ina yin godiya,

Bisa ai fa Sarkin wanda babu awa shiya.

Na yo salati ga Hashumina Ahmadu,

Har kau da Alainai, sahabbainai jiya.

96

Wa}ar Al}ur’ani

1. Bisimil ilahi zan bi]an Allah nufi,

Wannan da Yay yi shi bayyana min godiya.

2. Alhamdu lillahi fa na gode mishi,

Na yo salati ga Annabi nai godiya.

3. Na yo salati ga Alu, Sahbu da Anbiyah,

Ya ba ni {ur’ani inai Mai godiya.

4. Ya ba ni in fita inda }ulu la’ihah,

Asalin uba da uwa ina yin godiya.

5. Na gode Allah Ya fa ban {ur’ani,

Har kau da }issoshi ina yin godiya.

6. Ya ba ni aiki kau da Al}ur’ani,

Ya ba ni jin ma’anarsa Ya ban godiya.

7. Alhamdu lillahi ha}i}an la fakhar,

Kuma ni ina fa zaton shiga fartaniya.

8. Ni za ni shi’iri Rabbu ba ni abin nufi,

In bayyana ga nufi zama nai godiya.

9. Don Yai kalaminai dubu fa ]ari uku,

Da dubu ]ari tara har dubu fa ]ari ]aya.

10. Sannan haruffan nan dubu fa ]ari ]aya,

Da dubu fa saba’in, dubu sittin jiya.

11. Hakanan kaza fa dubu talatin na biya,

Da dubu fa ukku kaza ]ari biyu yat tsaya.

97

12. Sura ta {ur’ani ]ari fa da goma sha,

Fu]u har da hizbi nashi sittin na gaya.

13. Sumuni ]ari fu]u na tamanin na bisa,

Na gode Ahmadu na fa gode mai niya.

14. Aya dubu shidda, ]ari shidda bisa,

Sittin da shidda suna biya, mu yi godiya.

15. Aya dubu ku sani batun amri sukai,

Su kau dubu nahyi sukai mu yi godiya.

16. Aya dubu wa’adi dubu fa wa’idi,

Su kau dubu }isasu da wal akhbariya.

17. Aya dubu ibaru fa wal amsalu,

Na cimma sittu fa alfu, na yi fa godiya.

18. Zan bayyana muku ni, ]ari fa biyat ku ji,

Raba kau haram da halat yamini na gaya.

19. Aya ]ari fa guda du’a’i tar raka,

Har dud da tasbihi ku zan yin godiya.

20. Sittin da shidda fa nasikhun mansukhun,

Ku ‘yanuwana am ku zan yin godiya.

21. Mai ]amre {ur’ani fa harafi na bakwai,

Agun, khahun, hawayyu ramzin godiya.

22. Wannan da yaf fa hana ma {ur’ani fa ja,

Harafi biyat na, hayyu, rah]in ramziya.

23. Mai sa shi madda ai fa harafi na takwas,

Na}sun da aslukumu fa ramzin maddaya.

98

24. Zakuwa ta madda nan fa harafi ukku na,

Siddi da Hamza, Fuyi ku lura da godiya.

25. Mai sa fa Jan]e bisa tafowa daidai,

Jan]en }asa biyu, kai ku lura da anniya.

26. Da Turi biyu da]a mai hawan juna jiya,

Harafi bakwai na don ku lura da gaskiya.

27. Su kau ka kumya inda ba nan yab biyo,

Jan]en ga ukku ku sa ma {ur’an anniya.

28. Harafin da yaf fa biyo fa harafin Siddi shi,

Sai bai kalami na shi na fa ga siddiya.

29. Amma ba}i da yawa ha}i}an na gaza,

Domin fa tsarinai ga wa}a yai wuya.

30. Domin su Dibtara har da Hamza fa mai rai,

Har kau da Hamza kaza matacce kun jiya.

31. Da wasunsu ha}}an ai kasiran yai wuya,

Tsari ga wa}a babu iko nan niya.

32. Kuma kau }ira’a goma sha biyu ag garai,

Wa}afi da Ya da Fa, Jan]e ha}}an mai wuya.

33. Wa}afi bakwai wasu ko takwas na sunka ce,

Nan kau ga {ur’ani na Annabi na shiya.

34. Kwab bar su amdan bai fa yo da]a ta}ama,

Sai dai fa istigfari ya yi ma’asiya.

35. Sannan Kututturrai na Al}ur’ani,

Wannan da ba a sani fa sai na}ali jiya.

99

36. Kuma Samma na nan ukku fil {ur’ani,

Kuma Khalidaini guda ga {ur’an nig gaya.

37. Kuma Auliya ula’ika shi ]ai shike,

Da yawa kamassu da ni} }ara tsari niya.

38. Kuma kau Sujuda goma sha bi’u na gaya,

Wannan da za a fa yi ga Al}ur’aniya.

39. Sajada ta farko can cikin La’arafu,

Ra’adu, Ate, Subhana, Maryam na gaya.

40. Diba ga Zilzala zo ka can Fur}ana,

Can inda Namlu wuce cikin Laraiba ya.

41. Har Sad da, Hemem, Fussilat, goshi }asa,

Ka yi kabbara bisa taimama da wulu’iya.

42. In don wulu’in a] ]abi’a taka kai,

Koko ha}i}a tayammumi ga ]abi’iya.

43. Sai taimama kaka yi zuwa fa sujuda,

In kau wulu’i, kai wuce da sujudiya.

44. Ga wuri na Nafdi kaza da Harda ha}i}atan,

Aikin Muhammadu nawa Manzo nig gaya.

45. Sai kabbara da]a za ka yi goshi }asa,

Bisa in da Sarki wanda Ya’ isa ai biya.

46. Sannan ka kama da]a karatu naka kau,

Taso da kabbara inda wanda fa ya’ iya.

47. Nan Ali Imrana wa}af yaf faru shi,

Na biyunsu fil An’ami, kai ku yi tambaya.

100

48. Sannan ga La’arafu, na ukku tsaya ka ji,

Na fu]unsu nan ga fa Taubata, kai ka jiya.

49. Na biyat ga ai fa Yasin na shidda ga Fathu kau,

Na bakwai ga Tahrimi, Muzammilu thamaniya.

50. Da]a ajizanci yaf fa kammin nit tsaya,

Allah Shi amsam min fa wanga da nig gaya.

51. Allah Shi ba mu ganin Muhammadu nawa ni,

Ranaf fa tashi sa mu Firdausinmu ya.

52. Ya Rabbi zawwijni Hassan ]an Sayyida,

Da Aliyyu mai fa kama da Annabi in raya.

53. Wa}ar Kilon shi mallami Mahmudu ta,

Al}ali Ma’arufi da kowa yaj jiya.

54. Ya ba ni {ur’ani da na}alinai jiya,

Allah Shi ba ni ganin su can ranab biya.

55. Ya ba ni ilmi har da ladabi tarbiya,

Da tawalu’i ya ce ri}e tauhidiya.

56. Ramni da yak kama ni sai nan nit tsaya,

Allah Shi gafarta ma ]an Barambiya.

57. Ishirin da bi’u ga fa ai Jimada Lawwali,

Nit tsara wa}ata zuhur Jum’a jiya.

58. A cikin sana da]a goma sha ]ai Makkata,

Shi’iri da niy yo nai zato autaniya.

59. Tammat bihamdillahi ni kam na tsaya,

Don wallah tari niy yi niyya in gaya.

101

60. Da nufin fa Allah Yag gudana gare ni kau,

Nan Yai nufi kau in tsaya kau nit tsaya.

61. Ramzi na Hijra Annabina nig gaya,

SHASA’A[U bana ai cikaf fa habisaya.

62. Alhamdu lillahi ina yin godiya,

Bisa ai fa Sarki Wanda babu awa Shiya.

63. Na yo salati ga Hashimina Ahmadu,

Har kau da Allainai Sahabbainai jiya.

Tammat bihamdillahi wa husnu aunihi.

102

Nazarin Wa}ar {abli da Ba’adi

A cikin wannan wa}a, Modibbo Kilo ta yi bayanin

kurakuran da ke sa a yi }abla da ba’ada cikin salla da

kuma kurakuran da ba su sa a yi su, saboda wata ‘yarta

A’ishatu wadda ta neme ta da ta ba ta bayanin haka a

cikin wa}a. Modibbo Kilo ta biya bukatar yin haka,

saboda ta kawo bayanin abin da aka tambaye ta, ta

hanyar rubuta wa}a wadda za ta taimaka a yi saurin

ganewa.

A wannan wa}a, baiti na ]aya, Modibbo Kilo ta

fara da yabon farawa ta hanyar gode wa Allah

Ma]aukakin Sarki da yabo ga Annabi Muhammad

(sallallahu alaihi wa sallam) da alayensa da sahabbansa

kamar haka:

Na gode Allah ‘yanuwana nai yabo,

Ga Muhammadu har kau da Alu, Ashabu ni.

Ga abin da aka samu na baitocin wa}ar, babu yabon

rufewa, mai yiwuwa haka ta tsara wa}ar, ko kuma kila

ba a sami }arshen wa}ar ba. Modibbo ta kawo dalilin

da ya sa ta rubuta wa}ar a baiti na 4 da na 5:

Don ko fa A’ishatul Mubaraku tab bi]a,

In rarrabe mata ‘yan uwana dud da ni.

Domin fa A’ishatu ]iyak Kilo tab bi]a,

S ai ko fa masu biya a hanya tamu ni.

Baitocin wa}ar guda 47 ne kuma wa}ar ‘Yar tagwai ce,

wadda ke ]auke da ]ango bi-bi-yu a cikin baiti. Tana

da amsa-amo wanda ke }arewa da ‚ni‛ tun daga farko

103

har }arshen wa}ar, sai dai an sami ta}adarin baiti na 7,

wanda ya }are da ‚ri‛. Wa}ar ba ta zo da ramzi ba.

Modibbo ta furta jigon wa}arta a baiti na 2, inda

ta nuna cewa, bayani za ta yi a kan }abla da ba’ada

cikin salla:

Allah ina ro}on fasaha in fa]i,

Bisa ko ga }abla da ba’ada don sahwi da ni.

Modibbo ta kawo bayanin dalilan da ke sa a yi

sujadar }abli guda takwas, ko da yake ita ta ce tara za ta

kawo. Wuraren kuwa su ne:

i. Idan an mance kabbarori biyu cikin salla, amma ba

kabbarar farko ta harama ba.

ii Idan an mance da surori biyu.

iii Idan an mance sura guda.

iv Idan an mance ‘sami Allahu liman hamidahu’

biyu.

v Idan an mance zaman tsakiyar salla, ga salla mai

raka’a hu]u ko uku.

vi Idan an mance ‘Attahiyatu’ biyu.

vii Idan an yi ragi da }ari a cikin salla.

viii Idan an asirta wurin bayyanawa, kodayake

wannan hukunci a kan maza kawai yake ban da

mata.

A nan magana game da }abla ta tsaya, kuma ta yi

bayanin cewa, duk wanda bai samu gyaran sallarsa ba,

bayan ya yi kuskuren da zai yi wa }abla kuma bai yi ba,

to babu sallarsa.

Duka wannan bayani ya zo a cikin baiti na 13

zuwa 23 kamar haka:

104

Wannan da yab bar kabbarorinai biyu,

In ba ta farko }abla ta shika yi sani.

Wannan da yam mance a surori biyu,

Nan ko ga salla }abla ta shika yi sani.

Wannan da yab bar ko fa suratai guda,

Sukutum ga salla }abla ta shika yi sani.

Wannan da yam mance ga sami’Allah biyu,

Sukutum ga salla }abla ta shika yi sani.

Wannan da yam mance ga yin fa zaman tsaka,

Nan ko ga salla }abla ta shika yi sani.

Wannan da yam mance ga attahiyyatu biyu,

Nan ko ga salla }abla ta shika yi sani.

Wannan da yay yi ragi da }ari tare duk,

Nan ko ga salla }abla ta shika yi sani.

Wannan da ya ’ asirta wurin ko bayyana,

Nan ko ga salla }abla ta shika yi sani.

Wannan fa shara]i na maza na ad da shi,

Don su da sirru da jama’a sani.

Da]a }abla ta cika ‘yanuwa ta tara

Don Allah kui muna addu’a gufrani.

Ku ga washi salla don wa]anga fa

‘yanuwa,

Shi babu salla tashi ha}}an ya boni.

105

A nan an samu sa~ani domin wurin tantacewa an

ga wurare 8 ne alhali Modibbo ta ce wuri 9 za ta kawo,

kamar yadda baiti na 36 na }asa ya nuna:

Da]a na yi }abla tara kaza ba’ada bakwai,

Na bar su ha}}an wallah, Allah Ya sani.

Hakanan Modibbo Kilo ta kawo kurakuran da ake

gyara da sujudar ba’ada. Bayaninta ya nuna cewa

wuraren da ake yin sujudar ba’ada bakwai ne kamar

haka:

i. Yin magana cikin salla bisa mantuwa ii. Yin sallama ga raka’a ta biyu cikin salla mai

raka’a hu]u ko uku bisa ga mantuwa. iii. Yin shakka ga cika ko ragewar salla. iv. Wanda ya yi ragi, ya yi raka’a guda ko biyu

bisa mantuwa. v. Mi}ewa bayan ya yi raka’a ta cika. vi. Idan kokwanto ya auri mai salla. vii. Bayyana karatu wajen assirtawa ga maza

kawai, ba ga mata ba.

Ga baitocin da Modibbo Kilo ta kawo don wannan

bayani, baiti na 25 zuwa 34:

Da]a za ni gun ko ba’ada don anniya,

Ga bakwai da anka yi, don ku lura ku zan tuni.

Da]a wanda yai magana ga salla don shi san,

Bisa mantuwa da]a ba’ada ta shika yi sani.

106

Wannan da yai ko sallama raka’a ta biyu,

Bisa mantuwa da]a ba’ada ta shika yi sani.

Wannan da yai shakka ga salla ta cika,

Ko ta rage da]a ba’ada ta shika yi sani.

Wannan da yai ragi yay yi raka’a guda,

Koko biyu da]a ba’ada ta shika yi sani.

Wannan da yai tsaye, bayan raka’a da rashi,

Da]a yai ruku’i baya ba’ada shikai sani.

Wannan da kokwanto ha}}an yar ri}a,

Koyaushe dum shi kam fa ba’ada fa ta sani.

Wannan da yak ko bayyana fa ga sirru shi bisa mantuwa,

Shi kam fa ba’ada ta kama shi don ku sani.

Fa shara]i bale maza na ad da shi,

Don sud da ba’ada ya jama’a sani.

Kwag gunce salla don wa]anga fa sab’atu

Shi babu salla tashi hakanan ya boni.

Har wa yau, a baiti na 39 zuwa 45, Modibbo Kilo ta

fa]i cewa akwai kurakuran da ba a yi wa }abla ko

ba’ada, kuma duk wanda ya yi su, ya yi kuskure, kuma

ya ~ata sallarsa kamar yadda ta ce a baitin :

Da]a kway yi }abla da ba’ada ai ga wa]anga duk,

Ya ~ata salla tashi babu ta ai fa ni.

Ga abubuwan da za su ~ata wa mutum salla, idan bisa

kuskure ya yi musu }abla ko ba’ada.

107

i. Mance Sami’Allahu guda.

ii. Mance kabbara ]aya, amma ba ta farko ba.

iii. Mance }unuti.

iv. Yin zamanta, wato sallama.

v. Mance Subhana Rabbiyal azim ga ruku’i.

vi. Mance Subhana Rabbiyal a’ala ga sujuda.

vii.Mance Allahumma rabbana walakal hamd.

Modibbo Kilo ta rufe wa}arta, ga alamu, tana so ta san

ko A’ishatu wadda ta yi mata tambayar, ta wadatu da

abin da ta bayyana mata, domin ga abin da ta ce a

baitin }arshe, baiti na 47:

47. Wa}ag ga kir ro}a fa Bintu Aliyyu am,

Ibnu Fanuju ibnu Bukhari a ga nan gwani.

108

Wa}ar {abli da Ba’adi

Bismillahir rahmanir rahim

Shi’iru li Saudatu bintu Mahmudu Gwani al-

Burkhawiyyu {adi Sansanin-sausa baladan, min }abilati

Baranbuen, al’alimu kabirun ta}iyyun mal abidus salihu

al waliyyu, Kadi Sakkwato ibnu Muhammadu Ashura,

Allahumma agfirhu.

1. Na gode Allah ‘yanuwana nai yabo,

Ga Muhammadu har kau da Alu As’habu ni.

2. Allah ina ro}on fasaha in fa]i,

Bisa ko ga }abla da ba’ada don sa awi da ni.

3. Wallahi har tallahi Allah Shahidi,

Ba don riya niy yo ta Allah Ya sani.

4. Don ko fa A’ishatul Mubaraku tab bi]a,

In rarrabe mata ‘yanuwana dud da ni.

5. Domin fa A’ishatu ]iyak Kilo tab bi]a,

Sai ko fa masu biya a hanya tamu ni.

6. Don Allah al- Ulama’u tubu ilaikumu,

Ni jahila nike wallah Allah Ya sani.

7. Don Allah al-Ulama’u ku gyara na boni,

Gigi fa ni jahila nike zahiri.

8. Haka ba]ini ko ka gano ~attare dut,

Don shisshigi na niy yi Allah Ya sani.

109

9. Don ko ina son in ga babban Mursalu,

In ko gano fa mujadaddi Usmanu ni.

10. Don ba ni liddi nan a wa}ar Shaikhu duk,

Shaikhummu Fodiyo wallah Allah Ya sani.

11. Don ko larura ]aliba ta tab bi]an,

Da]a ta yi taslimi da gaske gare ni.

12. Da]a nif fa dubo ko larura nim mata,

Duk dolge nau Allah Shi gafarta mini.

13. Wannan da yab bar kabbarorinai biyu,

In ba ta farko }abla ta shika yi sani.

14. Wannan da yam mance a surori biyu,

Nan ko ga salla }abla ta shika yi sani.

15. Wannan da yab bar ko fa suratai guda,

Sukutum ga salla }abla ta shika yi sani.

16. Wannan da yam mance ga sami’allah biyu,

Sukutum ga salla }abla ta shika yi sani.

17. Wannan da yam mance ga yin fa zaman tsaka,

Nan ko ga salla }abla ta shika yi sani.

18. Wannan da yam mance ga attahiyyatu biyu,

Nan ko ga salla }abla ta shika yi sani.

19. Wannan da yay yi ragi da }ari tare duk,

Nan ko ga salla }abla ta shika yi sani.

20. Wannan da ya’ asirta wurin ko bayyana,

Nan ko ga salla }abla ta shika yi sani.

110

21. Wannan fa shara]i na maza na ad da shi,

Don su da sirru da jama’a sani.

22. Da]a }abla ta cika ‘yanuwa ta tara

Don Allah kui muna addu’a gufrani.

23. Ku gare shi salla don wa]anga fa ‘yanuwa,

Shi babu salla tashi ha}}an ya boni.

24. Don Allah kui yi muna tattali, lura zumai,

Domin mu san lada ga Allah Shi Gwani.

25. Da]a za ni gun ko ba’da don anniya,

Ga bakwai da anka yi, don ku lura ku zan tuni.

26. Da]a wanda yai magana ga salla don shi san,

Bisa mantuwa da]a ba’ada ta shika yi sani.

27. Wannan da yai ko sallama raka’a ta biyu,

Bisa mantuwa da]a ba’ada ta shika yi sani.

28. Wannan da yai shakka ga salla ta cika,

Ko ta rage da]a ba’ada ta shika yi sani.

29. Wannan da yar rage yay yi raka’a guda,

Koko biyu da]a ba’ada ta shika yi sani.

30. Wannan da yai tsaye, bayan raka’a da rashi,

Da]a yai ruku’i ba ya ba’da shikai sani.

31. Wannan da kokwanto ha}}an yar ri}a,

Koyaushe dum shi kam fa ba’ada fa ta sani.

32. Wannan da yak ko bayyana fa ga sirru shi bisa mantuwa,

Shi kam fa ba’ada fa ta kama shi don ku sani.

111

33. Fa shara]i bale maza na ad da shi,

Don sud da ba’ada ya jama’a sani.

34. Kwag gunce salla don wa]anga fa sab’atu

Shi babu salla tashi hakanan ya boni.

35. Don Allah kui muna ijtihadi muminai,

Domin mu san rahma ga Allah Rahmani.

36. Da]a na yi }abla tara kaza ba’ada bakwai,

Na bar su ha}}an wallah Allah Ya sani.

37. Amma wa]anga dud ni fa]i bayan su duk,

Kul ya kurumu fa kulu rakwai ka yi tuntuni.

38. Da]a babu }abla da ba’ada ]ai ga wa]anga duk,

In ya }iya ya yo su, babu su ya boni.

39. Kwam mance sami’Allahu ha}}an guda,

Da]a babu }abla da ba’ada ya jama’a sani.

40. Ko kabbara ]aya ba ta farko ba kab bari,

Da]a babu }abla da ba’ada ya jama’a sani.

41. Ko ko }unuti kab bari ya ]an’uwa,

Da]a babu }abla da ba’ada ya jama’a sani.

42. Koko zamanta da ka yi ga sallama,

Da]a babu }abla da ba’ada ya jama’a sani.

43. Ko Subhana Rabbiyal azim ga ruku’i,

Da]a babu }abla da ba’ada ya jama’a sani.

44. Ko Subhana Rabbiyal a’ala ga sujuda,

Da]a babu }abla da ba’ada ya jama’a sani.

112

45. Koko fa Allahumma Rabbana kab bari,

Da]a babu }abla da ba’ada ya jama’a sani.

46. Da]a kway yi }abla da ba’ada ai ga wa]anga duk ,

Ya ~ata salla tashi babu ta ai fa ni.

47. Wa}ag ga kir ro}a fa bintu Aliyyu am,

Ibnu Fanuju ibnu Bukhari a gan nan gwani.

Nazarin Wa}ar Nasiha Game da Ga~o~i Bakwai

Wannan wa}a ce da Modibbo Kilo ta rubuta, tana yi wa

jama’ar Musulmi maza da mata nasiha, game da kiyaye

ga~o~i bakwai na jikinsu. Baitocin wa}ar guda 40 ne,

kuma ‘Yartagwai ce, mai ]angogin bibiyu cikin baiti.

Tana da amsa-amo wanda ke }arewa da ‘sa’ kuma a

kusan dukkanin baitocin an yi amfani da Kalmar

‚nasa‛ ko farkon ‘masa tun farko har }arshen wa}ar.

Ta amabci sunanta a cikin wannan wa}a

Modibbo ta yi yabon bu]ewa da godiya ga Allah

Ma]aukakin Sarki, tare da yin salati ga Annabi

Muhammad (sallallahu alaihi wasallam), ta kuma

ambaci mala’ikun nan Ra}ibu da Atidu masu rubuta

ayyukan alheri ko na sharri. Bayanin haka na }unshe a

cikin baiti na 1zuwa 15. Misali a baiti na 1 zuwa 2 ga

abin da ta ce:

Alhamdu lillahi muna gode miShi,

Don Shid da iko Jalla mui bege naSa.

Mun yo salati ga Annabinmu Muhammadu,

Har kau da Alu da Sahbu don }auna tasa.

113

Modibbo ta furta jigon wa}arta a baiti na 16 zuwa na

17 inda ta nuna cewa nasiha za ta yi, a kan mutum ya

tsare ga~o~in jikinsa guda bakwai . Ga baitocin a wa}e:

Ya ayyuhal insanu mai fa ga~a bakwai,

Irlinka ke nan kai tsare daula tasa.

Shi za ni zanawa ga~an nan kau bakwai,

Domin a yo ya}i mu san lada tasa.

Bayan wannan bayani da ya gabata, sai Modibbo Kilo

ta shiga tsundum cikin bayanin wa]annan ga~o~i

bakwai, wato ido da kunne da harshe da hanci da ciki

da hannu da al’aura, kamar yadda ta kawo su a cikin

baiti na 18 zuwa 23. Dangane da ido sai ta ce, a guji

dubin haram da shi, haka kunne a bar sauraron haram

da shi. Harshe a daina yin hululu da maganganu batsa

da shi. Hanci kuwa, a bar sha}ar mugun abu na haram

da shi. Ciki kuma a kiyaye ci da sha masa abin haram,

kamar rashawa da sauransu. Hannu a guji ta~a ko ri}a

ko ]aukar abin da duk yake haram da shi. Al’aura kuma

a tsare ta, ka da a saka ta a cikin haram, kamar liwa]i

ko zina. Ga baitocin da ke }unshe da haka:

Kame ido ka bari zuwa ga haramiya,

Kai dai ka yangadud kai tuno kunne nasa.

Ka bari na saurare zuwa ga haramiya,

In ka yi kirki kai ri}e halshe nasa.

Da]a kau ka lura ka bar fululi kai jiya,

Hanci rufe shi, ka bar biyar ra’ayi nasa.

114

Na haramiya kai tsorci Allah Wahidi,

Yo hankali ga cikinka nana ka }i masa.

Rashwa haram da haramiya, kai yo nazar,

Hannunka mai ]auka ta~i ka }iya masa.

Wallahi al’aura tsare ta ka ha}}a}e,

Da zina, liwa]i har da is’haqi nasa.

A baiti na 25, Modibbo ta sake kawo wa]ansu abubuwa

da ke halakar da Musulmi idan ya bi ta tasu, ta yi nasiha

game da su, wato zuciya da duniya da Shai]an da

fasi}ai. Baitin shi ne:

Da]a zucciya na nan da nata bonenta dut,

Shai]an da dunya har da fasi}}ai nasa.

A baiti na 26 zuwa 37 Modibbo ta du}ufa ga yin addu’a

ga kanta da jama’ar Musulmi, tana ro}on Allah Shi

tsare ta da sauran Musulmi daga mugwayen abubuwa,

Ya ba ta damar yin tuban da ba na muzuru ba da ro}on

Allah samun Aljanna Firdausi. Ta ro}i Allah da Ya

tsare Musulmi daga sharrin Shai]an, Ya gafarta musu

zannubansu, mata da maza da malamai da ‘yan’uwa da

ma}wabta da abokai da ‘ya’ya da iyaye da jama’ar

Shehu Usmanu [anfodiyo (radi’allahu anhu) da Ansaru

da Muhajirina da dukkan sauran jama’ar Annabi

Muhammad (sallallahu alaihi wasallam).

A }arshe Modibbo ta yi yabon rufewa a cikin

baiti na 38 zuwa 39, inda ta yi godiya ga Allah, ta kuma

yi salati ga Annabi Muhammad (sallallahu alaihi

wasallam) da Alayensa da Sahabbansa da Tabi’ai

kamar haka:

115

Alhamdu lillahi ina da]a godiya,

Allah Shi ba mu zama ga Firdausi nasa.

Na yo salati ga Alu, Sahbu da Tabi’i,

Allah Shi ba mu farin ciki don so naSa.

Ramzin wa}ar kuwa wanda ta ambata da

SHASASSAZU wato 1367 ya bayyana a cikin baiti

na }arshe, wato na 40, inda Modibbo Kilo take cewa:

Tammat bihamdillahi shi’iratu ta cika,

Ramzi SHASASSAZU nan ga hijiratai nasa.

116

Wa}ar Nasiha Game da Ga~o~i Bakwai

Bismillahir Rahmanir Rahim. Sallallahu alan Nabiyyil

karimi.

Shi’iru li Saudatu binti Mahmud ibnu Muhammadu

Ashura al-Barnawi min }abilati Barinbu’in, lil amri

wan nahyi lil muslimina.

1. Alhamdu lillahi muna gode miShi

Don Shid da iko Jalla mui bege naSa.

2. Mun yo salati ga Annabinmu Muhammadu,

Har kau da Alu da Sahbu, don }amna tasa.

3. Ni wallah son Allah da yarda’ Annabi,

Nika yi ga Fa]ima wofofo har so nasa.

4. Kic ce na’am madalla Saudatu mallama,

Allah Shi ba mu muwafa}a don so naSa.

5. Na shaida son Allah da yarda’ Annabi,

Kika yi garan na san kina bisa so nasa.

6. Wallahi kau na yarda na kuma ha}}a}e,

Kuma na yi khaufi nai raja domi nasa.

7. Modibbo Saudatu arba’ina da shidda am,

Har ta shigo ta bakwai akwai ru’uba nasa.

8. In kam ha}i}an ke ri}e, ke darrafe,

Ni za ni wa’azu gare mu don mu tsare masa.

117

9. Yau shekarakki fa arba’in take kamilan,

Har ke shigo ta da ]ai cikin iko nasa.

10. Wannan da yac cika arba’in kau kamilan,

Sai dai shi ]au aniya ga saurare nasa.

11. In yay yi um au a’a yac ce ya boni,

Domin batunai zai zuwa zane nasa.

12. Domin miyon baki ruwan ko taddawa,

Halshenka al}alami ka zan nazari nasa.

13. Wallai jikinka ha}i}a allo na fa shi,

Ga~~anka ka boni kai ri}e irli nasa.

14. Shi ko Ra}ibu shina tsakanin kafa]a,

Bisa jijiya ta wuya zuwa kunne nasa.

15. Hakanan kazalika shi Atidu fa mun shina,

Wajjen fa aisari kuddukuki ai nasa.

16. Ya ayyuhal insanu mai fa ga~a bakwai,

Irlinka ke nan, kai tsare daula tasa.

17. Su za ni zanawa ga~an nan kau bakwai,

Domin a yo ya}i mu san lada tasa.

18. Kame ido ka bari zuwa ga haramiya,

Kai dai ka yangadud kai tuno kunne nasa.

19. Ka bari na saurare zuwa ga haramiya,

In ka yi kirki kai ri}e halshe nasa.

118

20. Da]a kau ka lura ka bar fululi kai jiya,

Hanci rufe shi, ka bar biyar ra’ayi nasa.

21. Na haramiya kai tsorci Allah Wahidi,

Yo hankali ga cikinka nana ka }i masa.

22. Rashwa haram da haramiya, kai yo nazar,

Hannunka mai ]auka ta~i ka }iya masa.

23. Wallahi al’aura tsare ta ka ha}}a}e,

Da zina liwa]i har da is’haqi nasa.

24. Na tsara al’amari bakwai a ku lura dut,

In kun jiya don Allah kui harama tasa.

25. Da]a zucciya na nan da nata bonenta dut,

Shai]an da dunya har da fasi}}ai nasa.

26. Allah tsare mu Shi ba mu tuba Rabbana,

Ga barin su domin kau mu san tcira naSa.

27. Wallahi har tallahi billahil lazi,

Na gilma kaina inda {ur’ani naSa.

28. Kowwaj Jihadi yat tsare ma wa]anga kam,

Ya tcira shi kau ya shige rahama tasa.

29. Koway yi lalata da yab bi wa]anga kau,

Har yam mace da]a ya shige halaka tasa.

30. Allah tsare mu Shi ba mu tuba mai fari,

Kada dai mu yo tuban Muzurrai can nasa.

119

31. Allahu na ro}e Ka don Kai ad da yi,

Allah Ka ba mu shiga ga Firdausi nasa.

32. Allah Shi gafarta ga walidammu dut,

Har ‘yan’uwammu kaza da mallammai nasa.

33. Har kau uwayen namu ]aki hakaza,

Har kau barori namu khuddami nasa.

34. Har kau ma}wabta ‘yan ]iyammu fa Rabbana,

Har kau abukkai masu so domi nasa.

35. Jama’am Muhammadu muminai dut dut duka,

Allah da kau jama’af fa Usmanu nasa.

36. Har kau da lansaru, muhajirrammu dut,

Su as su Habsatu salihai manya nasa.

37. Har mu da Fa]ima ‘yan’uwammu fa, jumlatan,

Tcarshe mu sharrin nan na Shai]annu nasa.

38. Alhamdu lillahi ina da]a godiya,

Allah Shi ba mu zama ga Firdausi naSa.

39. Na yo salati ga Alu, Sahbu da Tabi’i,

Allah Shi ba mu farin cikin don so naSa.

40. Tammat bihamdillahi shi’iratu ta cika,

Ramzi SHASASSAZU nan ga hijiratai nasa.

Tammat.

120

Nazarin Wa}ar Taya Murna ga Al}ali Umaru

Modibbo Kilo ta rubuta wannan wa}a ne, saboda na]a

kawunta Al}alin Wurno Umaru, a matsayin Limanin

masallacin Shehu na Sakkwato. Baitocin da ke cikin

wa}ar 45 ne, ‘Yartagwai ce, mai ]angogi bi-biyu a baiti.

Tana da amsa-amo na waje. Amsa-amon na waje

yana }arewa da ‘da’ har }arshen wa}ar. An samu

yabon bu]ewa da na furewa da ramzi a cikin wa}ar.

A baiti na 1 ne, Modibbo ta kawo yabon bu]ewa,

a inda ta gode wa Allah ,ta kuma yi salati ga Annabi da

Sahabbansa: Ga abin da ta ce:

Alhamdu lillahi mu gode Ubangiji,

Muna assalatu garai da Sahbu na murshidi.

Shi kuwa jigo ya bayyana a cikin baiti na 2 da na 4,

domin a nan ne Modibbo ta yi bayanin cewa, wa}ar ta

murna ce, don an na]a kawunta Al}ali Umaru

mu}amin limamin masallacin Shehu a Sakkwato. Ta

ambaci cewa ya gadi limancin ne daga kakansa Al}ali

Abdullahi. (Al}ali Abdullahi shi ne ya yi Hijira tare da

Sarkin Musulmi Attahiru, a lokacin da Turawa suka ci

Sakkwato da ya}i). Ga baitocin kamar yadda suke a

wa}e:

Ni za ni shi’iri inda kawuna Umar,

Al}ali Umaru na Wurno nasabin murshidi.

Mun gode Allah mun fito ga Mujadaddi,

Yau ka zamo Liman na Sakkwato Masjidi.

A baiti na 5 da na 6, Modibbo ta kawo muhimmin halin

kawunta mai kyau, wato rashin hassada. Daga baiti na

121

11 zuwa 27, kuma Modibbo ta kawo bayanai. Ta fa]i

asalin kawunta na iyaye da kakanni, wa]anda ta ce duk

wasunsu waliyyai ne. Ga wasu daga cikin baitocin:

[a na na Adde, Aca da Hauwa fa mallama,

Su a] ]iyan Ibbi ]iyatai shahidi.

[a na na Nana, Buhari, Jewu, Ru}ayyatu,

Su a] ]iyan fa Abu ]iyatai shahidi.

[an Bubakar ]an Inna Mau]o da Maigari,

Su a] ]iyan Usmanu ]anai shahidi.

Su duk waliyyaina ]iyan fa waliyyai,

Alhamdu lillahi mu gode Muhammadi.

Daga nan kuma sai imani ya ]ebe ta, ta nuna cewa duk

da wannan kyakkyawan asali da ta bayyana, ba ta kawo

shi don bugun gaba ba, har ta kawo farkon ayar

Al}ur’ani, wadda ta nuna cewa, cikin mutane babu

wanda ya fi wani, sai wanda ya fi tsoron Allah.

Mun dai fa]i domin fa akramakum ila,

Wa }aba’ila lita’arafu ga Mujaddadi.

A baiti na 30 zuwa 31, Modibbo ta yi wa kawunta

addu’ar Allah Ya tsawaita rayuwarsa, Ya tsare shi tare

da al’ummar musulmi daga sharrin mutum da aljani, Ya

ba ita Modibbo tare da sauran musulmi kyakkyawar

cikawa ta imani. Ta sa hannu ga wa}ar, ta hanyar

tabbatar da cewa, ita Kilo ]iyar Al}ali Mahmuda jikan

Gwani Mukhtari ce ta rubuta ta.

A baiti na 35, Modibbo ta ambaci ramzin

122

wa}arta, wato shekarar da ta wallafa ta, wanda lissafin

ya bayar da shekarar hijira SHASFAJI 1383 a inda ta ce:

Ramzi na hijira’ Annabinmu Muhammadu,

Bana SHASFAJI da]a na fa gode Muhammadi.

A cikin baiti na 41 da 44, Modibbo ta ro}i Allah

ma]aukakin Sarki da shi gafarta wa mahaifanta,

wa]anda suke shahidai da sha}i}anta da malamanta

da ]alibanta da ‘ya’yanta da ma}wabtanta da sauran

jama’ar musulmi baki ]aya.

A baiti na 45 kuma na }arshe, Modibbo ta yi

yabon rufewa ta hanyar gode wa Allah da salati ga

Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) inda ta

fa]i cewa:

Tammat bihamdillahi Allah Ya cika,

Da]a na iyas da salati inda Muhammadi.

123

Wa}ar Taya Murna ga Al}ali Umaru

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Sallallahu alan Nabiyyil Karim

1. Alhamdu lillahi mu gode Ubangiji,

Muna assalatu garai da Sahbu na murshidi.

2. Ni za ni shi’iri inda kawuna Umar,

Al}ali Umaru na Wurno nasabin murshidi.

3. Ya gadi Abdullahi Limamin gari,

Bayan fa Al}ali fa ya zam shahidi.

4. Mun gode Allah mun fito ga Mujaddadi,

Yau ka zamo Liman na Sakkwato Masjidi.

5. Ni na ji da]in ka aje faggon wuta,

Ka sami nasabi za ka zam kuma shahidi.

6. Halinka AllahYaf fa diba ya Umar,

Domin fa ]otare da ba ka da hasidi.

7. Saura shahada zamanin Mahdi kuma,

Ga fa]i fa kai na an na ukku ga shahidi.

8. Allahu a’lamu ni zato na niy yi ni,

Ga fa]i gidan nan ukku na asshahidi.

9. Domin alama wadda munka jiya gidan,

Ta bayyana min nai zaton ka fa shahidi.

124

10. Na taulafo ka da kai da Abdu da Ahmadu,

Rana} {iyama don ku kai ni ga Ahmadi.

11. [a na na Adde, Aca da Hauwa fa mallama,

Su a] ]iyan Ibbi ]iyatai shahidi.

12. [a na na Nana, Buhari, Jewu, Ru}ayyatu,

Su a] ]iyan fa Abu ]iyatai shahidi.

13. [an Bubakar ]an Inna Mau]o da Maigari,

Su a] ]iyan Usmanu ]anai shahidi.

14. [an Alfa Baba da Lab]o Abdullahi kau,

Har kau Walijo ]iyan Aliyu na shahidi.

15. [a na na Inna Garge haifen Ummu kau,

Auta ta Al}ali fa Ahmadu shahidi.

16. Su duk waliyyaina ]iyan fa waliyyai,

Alhamdu lillahi mu gode Muhammadi.

17. Shi af fa babban ]a na Ladan Rame kau,

[an {u}iya Mamman ga }adi na murshidi.

18. Su ukku suna a’ sha}i}ai kun jiya,

Kaka na shidda Hassan na Fa]ima Ahmadi.

19. Amma haki}an bai fa]i ba Mujadaddi,

Don babu girman kai ga Shaikhu Mujaddadi.

20. Mu ma muna koyi da Shaikhu Mujaddadi,

Don ba mu girman kai da gausur murshidi.

125

21. Mun dai fa]i domin fa akramakum ila,

Wa }aba’ila lita’arafu ga Mujaddadi.

22. Hauwa’u, A’isha kau uwaye Ali kau,

Sai kau sha}i}i nasu Bayero murshidi.

23. Haife na Hauwa’u uwa ta Shaikhu kau,

Su shidda na babban su Shaikhu Mujadaddi

24. Autanta Bayero Ali Saudi da Maunuma,

’Ya gwaggo su ]ai an na Inna Mujaddadi.

25. Haife na A’isha, Ayi ~i-Alinta ]ai,

Alhamdu lillahi mu gode Ahmadi.

26. Namiji na Ibbi da Muna kau fa uwa uba,

Da uban Salanke su Gab]o shi fa Muhammadi.

27. Su a] ]iyan ~i-Ali ha}}an kun jiya,

Allah Shi ba mu tsari mu tcira ga hasidi.

28. Ni na ta}aita don ishara ta isa,

Domin fa Umaru bai cikin fa muhasadi.

29. Ya gadi Abdullahi Alfa Abubakar,

Da Buhari Sadiri nasu ba shi da hasidi.

30. Allah Shi ]awwala naka umri kawu an,

Allah Shi tsarshe mu aduwwan hasidi.

31. Sharrin mutane har da Aljannu duka,

Allah tsare mu Shi ba mu husnul khatimi.

126

32. Shi’irin Kilon Mahmudu Na’ibi Sakkwato,

Jikan Gwani Mukhtari na fa uban gari.

33. Zamanin fa Abdu na Garba yay yi shi Na’ibin,

Bello uban Modibbo Al}alin gari.

34. Sannan fa yat tu~e su yan na]a Abdu kau,

Shi ]an Aliyu fa wallah Al}alin gari.

35. Ramzi na hijira’ Annabinmu Muhammadu,

Bana SHASFAJI da]a na fa gode Muhammadi.

36. [an kawu na ga Arafa uwa ta Umaru,

Al}ali taubashin Ru}ayyatu shahidi.

37. Al}ali Ahmadu kan ]iyan kun jiya,

Ishirin da ai hu]u na da yaz zam shahidi.

38. Ilmi zumunta ga karimci ba fushi,

Kyawo, balaga shi fa Abdullah hudi,

39. Shi ]an Aliyu Ru}ayyatu fa ]iya’ Abu,

Kakan su Al}ali fa Ahmadu shahidi.

40. Shi bai da hi}di bai da hassada ko ka]an,

Mai faggo }ofan nan ta kau Firdausi.

41. Allah Shi gafarta ma bin Ashura kau,

Jikan Gwani Mukhtari shi ma shahidi.

42. Allah Shi gafarta ma wallidanmu dut,

Har kau sha}i}}ai namu domin Ahmadi.

127

43. Har dud da malamammu ]alibbammu dut,

Da ]iyanmu masu biya ga hanya’ Ahmadi.

44. Dud dut Musulmi tabi’i fa da tabi’i,

Hakanan ma}wabta wanda sunka bi Ahmadi.

45. Tammat bihamdillahi Allah Ya cika,

Da]a na iyas da salati inda Muhammadi.

Tammat Bihamdillahi Wa *Husni Aunihi Was Salatu

Was salamu ala Rasulillahi.

128

Nazarin Wa}ar Burin Modibbo Kilo na Zuwa Makka

Kafin a fara nazarin wannan wa}a, bari a shaida wa mai

karatu cewa, an sami ’yan shafuka ka]an ne na wannan

wa}ar, don haka, ana tsammanin wa}ar ba cikakkiyar

wa}a aka samu ba. Wannan na iya zama dalilin da ya

sa, ba a sami yabon bu]ewa da sauran abubuwa a

cikinta ba. Don haka, kai tsaye, sai aka ga Modibbo

Kilo ta shiga bayanin cewa, idan burinta ya cika, na

tafiya Makka to, ba za ta dawo qasar Hausa (wato

Sakkwato) ba, domin ita wankin zunubai za ta tafi yi

kuma za ta yi zamanta a can garin Makka da Madina

wurin Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam). Ta yi

burin za ta ci gaba da zama a }asa mai tsarki, har ranar

da mutuwa ta same ta kuma tana fatan ta same ta kusa

da Raula. Hakanan ta }ara da cewa, fa]in haka da ta yi,

ya sa ta ji sanyi a ranta, game da wannan tafiyar da za

ta yi.

Modibbo Kilo, ta kawo tawali’u na cewa, ba ta

sani ba ko za ta samu yin wannan tafiya da take nema

ga Allah, ko ba za ta samu ba. A nan, sai kurum ta ro}i

Allah da Ya ]ora ta bisa hanyar gaskiya. Ga baitocin da

suka zo da wannan bayani, wato na 1 zuwa na 7:

In don fa Allah Yan nufo Yay yarda duk,

Ni ba ni komowa ga Hausa zama niya.

Wankin zunubbai za ni na can Makkata.

In zo ni }al-}al inda Manzonai niya.

Sai ko zamana za ni yi can [aibata,

Insha fa Allahu ga Annabi mai niya.

129

Har rad da mutuwa tat tafo mini hakaza,

In gode Allah can ga Rauda mai niya.

Da]a na ji sanyi ]an ka]anna ga zucciya,

Allah Shi kai ni zuwa ga hanyag gaskiya.

Da]a ko ina samun abin ga da nib bi]a,

Gun Rabbu Sarki Wanda babu awa Shiya.

Ko ba ni samu Rabbu Kai a} {adiri,

Allah Shi ba ni biya ga hanyag gaskiya.

A cikin baiti na 8 zuwa 13 kuwa, Modibbo ta ro}i

Allah Ma]aukakin Sarki da Ya ba ta ikon yin wannan

tafiya tare da jama’arta masu tattalin tafiya. Ta }ara da

cewa kuma wa]anda suka yi jinkirin zuwa da wa]anda

Allah Bai }addari su je ba, dukkansu, Allah Ya ba su

ikon bin gaskiya. Ya kuma tara su cikin Aljanna, kamar

yadda ta ro}a a baiti na 12 :

Allah Shi sa mu mu taru birnin Jannata,

Firdausi mai da]i ta muminnai jiya.

A }arshe, ta yi wa Shehu Usmanu [anfodiyo da sauran

musulmi, jama’ar Annabi (sallallahu alaihi wa sallam)

addu’a. A baiti na 14 da 15, Modibbo ta yi godiya ga

Allah da yabon Annabi Muhammad (sallallahu alaihi

wa sallam) da Sahabbansa da Alayensa sannan ta

ambaci sunanta. Ga baitocin

Na gode Allah na yabo shi Muhammadu,

Na yo salati ga Alu, Sahbu abin biya.

130

Tammat bihamdillahi wa}a ta cika,

Da]a Saudatu tay yo ta samu abin biya.

Ta kawo Ramzin wa}ar wato SHASASSAHU 1368

kamar haka:

Wa}a ha}i}an tawa Hijira’ Annabi,

SHASSASAHU ta Allah Shi gafarta niya.

131

Burin Modibbo Kilo Na Zuwa Makka

1. In don fa Allah Yan nufo Yay yarda duk,

Ni ba ni komowa ga Hausa zama niya.

2. Wankin zunubbai za ni na can Makkata.

In zo ni }al-}al inda Manzonai niya.

3. Sai ko zamana za ni yi can [aibata,

Insha fa Allahu ga Annabi mai niya.

4. Har rad da mutuwa tat tafo mini hakaza,

In gode Allah can ga Rauda mai niya.

5. Da]a na ji sanyi ]an ka]anna ga zucciya,

Allah Shi kai ni zuwa ga hanyag gaskiya.

6. Da]a ko ina samun abin ga da nib bi]a,

Gun Rabbu Sarki Wanda babu awa Shiya.

7. Ko ba ni samu Rabbu Kai a} {adiri,

Allah Shi ba ni biya ga hanyag gaskiya.

8. Allah Shi ba ni zuwa da jama’ata duka,

Wannan da sunka yi tattali bisa gaskiya.

9. Wannan da sunka yi jinkiri ga rashin zuwa,

Da wa]anda iko yaf fa kucce duniya.

10.Da wa]anda bai ko }addara ma zuwa zumai,

Allah Shi ba su biya ga hanyag gaskiya.

132

11. Da wa]anda ba su da ai fa ikon saduwa

Bisa }addara, Sarki mu taru fa Janniya.

12. Allah Shi sa mu mu taru birnin Jannata,

Firdausi mai da]i ta muminnai jiya.

13. Dangin Musulmi har masoyanai kuma,

Jama’a Muhammadu har da Usmanummu ya.

14. Na gode Allah na yabo shi Muhammadu,

Na yo salati ga Alu, Sahbu abin biya.

15. Tammat bihamdillahi wa}a ta cika,

Da]a Saudatu tay yo ta samu abin biya.

16.Wa}a ha}i}an tawa Hijira’ Annabi,

SHASSASAHU ta Allah Shi gafarta niya.

Tammat bihamdillahi wa husni aunihi was salatu

was salamu ala Rasulillahi sallallahu alaihi wa sallam.

133

Nazarin Wa}ar Hikaya

Modibbo Kilo ta yi wannan wa}a ne, tana mai ba da

bayani dangane da wani labari da kakanta Al}ali

Abdullahi ]an Ladan Rame ya ba ta, game da wata

gasa da ya yi tare da wani mutum. Ta kira wannan

labari ‘Hikaya’. Baitocin wa}ar 56 ne kuma ‘Yartagwai

ce mai ]angogi bi-biyu. Ta na da amsa-amon waje

mai }arewa da wasalin ‘i’ har zuwa }arshen wa}ar.

Modibbo ta yi amfani da yabon bu]ewa da na

rufewa. Yabon bu]ewa ya fito a cikin baiti na 1 a inda

ta yi godiya ga Allah da salati ga Annabi Muhammad

(sallallahu alaihi wa sallam) da kuma Sahabbai kamar

haka:

Alhamdu lillahi ina yin godiya,

Na yo salati ga Annabi da Sahabu shi.

Sannan ta furta jigon wa}arta a baiti na 2 da cewa,

wa}ar da za ta yi ta hikaya ce wadda kakanta ya sanar

da ita kamar haka:

Wa}ah hikaya ta da nij ji lifammihi,

Wannan da jaddi nawa yay yi ba’a da shi.

A cikin baiti na 5 zuwa 16, Modibbo ta yi bayanin cewa

shi mutumin da ke wannan ba’a ta gasar kilisa da

Al}ali Abdullahi, ya yi zaton Al}alin jahili ne

kuma ]an talakawa ne, ba}auye, saboda ya gan shi da

riga irin ta manoma. Mutumin ya }alubalanci Al}ali da

su yi kilisa, wato tseren hawan doki, saboda ya yi zaton

Al}alin bai iya ta ba. Shi mutumin ya zo da Ingarman

Doki, shi kuma Al}ali ya jawo Doki {uru. A lokacin

da suka hau dawakinsu suka yi kilisa, sai dokin Al}ali

134

Abdullahi {urun nan ya tsere wa Ingarma na wannan

mutumin. Daga nan mutumin sai ya ba da kai.

Don ya gano shi da Ba-ni-masu kun jiya

Rigam manoma yai zato nai jahili.

Shi na fa Al}ali fa Abdullahi shi,

Da]a yai zato nai ]an talakkawa fa shi.

Yac ce ka zo mu yi kau kilisa sahibi

Yac ce na’am shirya, suna ta ba’o’i.

Yac ce na’am ya sahibina na jiya,

Da]a yah hawo Doki na bawa goma shi.

Shi kau fa yah hau nashi {uru sun gamu,

Sun }etare birni suna ta ba’o’i.

Da zaginsa, shi kau nashi ai fa zagi biye,

Sun jera tcera suna ba’o’i don ku ji.

{uru da yat tcere ma Ingarma tuni,

{ura, fuka, Doki da mai shi sun gaji.

Mutumin ya gane cewa, Al}ali mutum ne mai ilmi ba

jahili ba. Daga nan ne fa mutumin ya ri}e shi aboki

kuma masoyi. Ga abin da Modibbo ta ce a cikin baiti na

16.

Da]a yar ri}e shi ri}o zamanai sahibi,

Bai }ara gitta mai zama kau ya gani.

135

Daga baiti na 20 zuwa na 52, Modibbo Kilo ta shiga

ambatar salsalar Al}ali Umaru da kuma zumuncin da

ke tsakanin Al}ali Abdullahi da wani sahibin Shehu

Usmanu [anfodiyo Abubakar Bakiri da sauransu. Ta ci

gaba da kawo kyawawan halayen Al}ali Abdullahi na

son zumunci da ha}uri da kyauta da rashin girman kai

da sauransu. Ga misalin wa]annan bayanai a cikin

wa]anann baitoci:

Kyawon hali, ilmi da kyauta han}uri,

Mai son zumunta mai balaga ba fushi.

Shi ]an Aliyu fa Ru}ayyatu fa ]iya’ Abu,

Jaddinsa Al}ali fa Ahmadu shahidi.

Al}ali Abdullahi ba girman kai,

Kuma babu rowa ga fa kyawo zahiri.

Ga son mutane ga fa ilmi nafi’i,

Kuma ba fusudi bai da tsiwaf fasi}i.

Modibbo ta yi nasihar a bar ta}ama da asali da nasaba

da sauransu, wato mutum ya bar bugun gaba da cewa

shi ]an wane ko jikan wane ne, domin imani da aiki da

shari’a su ne ka]ai za su kai mutum ga shiga aljanna,

ba asali ko nasaba ba. Ga baitoci na 51 da 52 da ke

tabbatar da wannan bayani:

{aba da asli bai da kau fa muruwa,

Sai dai Ba}auye nan da ba shi da hankali.

Ku dai ku yo }aba da tsai da shari’a,

Aslin fa Murratu, kai ku bar tono ku bi.

136

Yabon rufewa ya bayyana a cikin baiti na 53 zuwa 55,

inda Modibbo ta kammala wa}arta da godiya ga Allah

da salati ga Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa

sallam) da Sahabbai da Alaye da Tabi’ai kamar haka:

Na yo salati ga Annabinmu Muhammadu,

Allah Shi ba mu gamo da su Firdausi.

Har kau Sahabbainai da Alaye kuma,

Da fa Tabi’ina da Tabi’i ga fa masu bi.

Tammat bihamdillahi wa}a ta cika,

Wa}a} Kilon Al}ali Sakkwato Na’ibi.

Kamar yadda aka gani a baiti na sama, Modibbo ta sa

wa wa}arta hannu ta hanyar kawo sunanta, domin fa]in

cewa ita ce ta wallafa ta. Hakanan ta bayar da ramzin

wa}ar SHISAFFU wato 1388 bayan hijirar Annabi

(Sallallahu alaihi wa sallam).

137

Wa}ar Hikaya

Bismillahir Rahmanir Rahim. Sallallahu alan Nabiyyil

Karim .

Shi’iru li Modibbo Kilo bint Alkhadi Mahmudu

Sakkwato Na’ibul Khadi ibnu Muhammad Ashura .

1. Alhamdu lillahi ina yin godiya,

Na yo salati ga Annabi da Sahabu shi.

2. Wa}ah hikaya ta da nij ji lifammihi,

Wannan da jaddi nawa yay yi ba’a da shi.

3. Al}ali Abdullahi liman shahidi,

Maifaggo }ofa nan ta kau Firdausi.

4. [a na na limam kau Aliyu fa kun jiya,

Jika na Ahmadu ]a na Ladan Rame shi.

5. Don ya gano shi da Ba-ni-masu kun jiya

Rigam manoma yai zato nai jahili.

6. Shi na fa Al}ali fa Abdullahi shi,

Da]a yai zato nai ]an talakkawa fa shi.

7. Yac ce ka zo mu yi kau kilisa sahibi

Yac ce na’am shirya, suna ta ba’o’i.

8. Yac ce na’am ya sahibina na jiya,

Da]a yah hawo Doki na bawa goma shi.

9. Shi kau fa yah hau nashi {uru sun gamu,

Sun }etare birni suna ta ba’o’i.

138

10. Da zaginsa, shi kau nashi ai fa zagi biye,

Sun jera tcera suna ba’o’i don ku ji.

11. {uru da yat tcere ma Ingarma tuni,

{ura, fuka, Doki da mai shi sun gaji.

12. Da]a sai fa daji yaf fa zame ya’ iso,

Sun sabka an fa ri}e Dawaki don ku ji.

13. Yak kama harda kau khulasa sai ka ce,

Dokin hari da]a Abdu yaf fa ri}o shi, shi.

14. Yac ce tsaya don Allah gafarta mini,

Ka yi rangwame fa gare ni don Allah bari,

15. Yat tabbata ba ]an talakawwa ba na,

Yah ha}}a}e bai gadi kau jahilci.

16. Da]a yar ri}e shi ri}o zamanai sahibi,

Bai }ara gitta mai zama kau ya gani.

17. Na gode Allah na yi kau da]a arziki,

Ya ban hikaya shi uban nau alimi.

18. Domin ba’a, kawun uwata shahidi,

Al}ali jikan Kadi Ahmadu shahidi.

19. Alhamdulillahi ha}i}an la fakhar,

Allah Shi ba mu biyas shari’a zahiri.

20. Kyawon hali, ilmi da kyauta han}uri,

Mai son zumunta mai balaga ba fushi.

139

21. Shi ]an Aliyu, Ru}ayyatu fa ]iya’ Abu,

Jaddinsu Al}ali fa Ahmadu shahidi.

22. [an Bubakar jika na Bayero Toga ji,

Shi as sha}i}in Hauwa inna Mujadaddi.

23. Domin fa Abdullahi Al}alin gari,

Don ya yi tabsiri da tsoronai ku ji.

24. Zamanin fa mallam Mani na mutafannini,

Da Aliyu ]an kau Inna Jangirde ku ji.

25. Ita Fa]ima babba] ]iya’ Almustafa,

Haifen Khadijatu yaf fa Bakiri don ku ji.

26. Bakiri uban Al}ali Ahmadu Gandi shi,

Da Khadijatu wallai ubansu guda ku ji.

27. Dibo fa Mahmudu uwatai Mus]afa,

Wallai sha}i}}aina irin sinini.

28. Kuma mallaminai na kafilinai jiya,

Baban uwa’ Ashafa uban Bakiri ku ji.

29. Mata ta Ahmadu kau Rufa’i ta farin,

Wallai ]iya’ Ashafare Abdur Rahmani ku ji.

30. Sarkin Musulmi ]an fa Shaikhu Mujaddadi,

Shi af fa wa ga ubanmu Isan Shaikhu ji.

31. Mata ta Mus]afa kau ta farin don ku ji,

Da uwaf fa Ashafa Bakiri Ibrahima ji.

140

32. Wallai ubansu guda fa kawun Mus]afa,

Jaddi na Fa]ima, Inna-Jangirde ku ji.

33. Limam fa Usmanu Aliyu ]iyanta na,

Wallai da Ahmadu ]a na Ladan Rame ji.

34. Jaddi na Lab]o, Walijo, Alfa, Mubaraku,

Baban uwassu fa Kubura, Ibrahima ji.

35. Limam fa Usmanu Aliyu tsaya jiya.

Wallahi jikokin fa yab Bakiri ku ji.

36. Al}ali Abdullahi ba girman kai,

Kuma babu rowa ga fa kyawo zahiri.

37. Ga son mutane ga fa ilmin nafi’i,

Kuma ba fusudi bai da tsiwaf fasi}i.

38. Al}ali Gandi yaf fa amri Khadijatu,

Ita at ta farin nan ga Al}ali ku ji.

39. Ta haifi malam kau Bukhari, Ru}ayyatu,

Har kau fa Nana da Jewu saurara ku ji.

40. Ita har da Ibbi, Aliyu, Usmanu ku ji,

Wallai ubansu guda fa Ahmadu {adi ji.

41. Kuma Abdu ya yi fa Lawwali fa gare shi,

Al}ali Ahmadu ]an fa Bakiri don ku ji.

42. Kuma yaf fa sha nono na gwaggonai Abu,

Al}ali Gandi yaz zamo fa ubansa ji.

141

43. Kuma ta karantasshe su Al}ur’ani,

{anwa ta Ibbi ya’ ubannen nasu ji.

44. Su dut da Hawa ]iya ta Ibbi don ku ji,

Da wasunsu har da ]iyan saraki don ku ji.

45. Kuma ga karatu ga rada’atai gidan,

Kuma ga ta gwaggonai fa yaz zam khashimi.

46. Al}adi Abddullahi manya na ku ji,

Kawun uwata adili mashhuri.

47. Daga duniya har barzahu har lahira,

Al}ali Abdullahi mai addini.

48. Modibbo nau ]an mallami Ashuri,

Jikan Gwani Mahmudu ]an Sidi Gwani.

49. Baban uwatai kau Gwani Mukhtari,

Su biyu sha}i}}ai na ]iyan Musa Gwani.

50. Shi a’ abokin kau ba’a jaddi fa nau,

Kawun uwata Abdu Al}hadin gari.

51. {aba da asli bai da kau fa muruwa,

Sai dai Ba}auye nan da ba shi da hankali.

52.Ku dai ku yo }aba da tsai da shari’a,

Aslin fa Murratu, kai ku bar tono ku bi.

53. Na yo salati ga Annabinmu Muhammadu,

Allah Shi ba mu gamo da su Firdausi.

142

54. Har kau Sahabbainai da Alaye kuma,

Da fa Tabi’ina da Tabi’i ga fa masu bi.

55. Tammat bihamdillahi wa}a ta cika,

Wa}ak Kilon Al}ali Sakkwato Na’ibi.

56. Ramzi na Hijira’ Annabina Ahmadu,

Ita ta SHISAFFU ga wanda ad da fa hankali

Tammat bi hamdillahi wa husnu aunihi. Wassalatu

wassalamu ala Muhammadir Rasulillahi sallallahu

alaihi wa sallam.

143

Nazarin Wa}ar Hatsin Bara

Kafin a shiga nazarin wannan wa}a, za a fara sanar da

mai karatu cewa, nazarin baitocin tsakiyar wa}ar

kurum aka samu yi, saboda ba a sami farko da }arshen

wa}ar ba. Hakanan wajen }irga baitocin wa}ar da sa

musu lambobin }idaya, an yi la’akari da baitocin da aka

samu a hannu ne kurum, don haka, ga misali ba lallai ba

ne baiti na ]aya na abin da aka kawo a nan, ya zama

baiti na ]aya na asalin wa}ar. Rashin samun farko

da }arshen wa}ar kuma, shi ya haifar da rashin nazarin

salon bu]ewa da rufewa da sauran abubuwan da aka

saba ta~awa wajen wannan aiki.

Na ra]a wa wannan wa}a suna, ‘Wa}ar Hatsin

Bara’, saboda ta }unshi abubuwa daban-daban,

wa]anda suka ha]a da kar~uwar ijtihadin (sa}on)

Mujaddadi Shehu Usmanu [anfodiyo a duniya da

garga]i da nasiha ga shugabanni da fafutukar Modibbo

Kilo wajen samun muhalli a Makka da sauran su.

A cikin wannan wa}a Moddibo Kilo ta yi

bayanin cewa Shehu Usmanu [anfodiyo ya yi kira na

addinin Musulunci, kiran da Sharifai da Fulani da

Hausawa da wa]anda ba Hausawa ba (Baubayi) da

sauransu suka kar~a, kuma suka yi mubayi’a ga Shehu

Usmanu [anfodiyo da sauran shugabanni irin su malam

Abdullahin Gwandu da Sarakunan Musulmi

Muhammadu Bello da Abubakar Atiku da Ahmad al-

Rufa’i. Baitocin da ke ]auke da wannan bayani su ne

baiti na 2 zuwa 5 kamar haka:

In don kitabi wallah ko Baubawa,

Wallai Sharifi na ga Raudi-jinani.

144

Komi sharifci naka ko fillanci,

Ko da fa Baubawa, ko fa Bahaushi.

Shi Shaikhu yay yi kira ajibu da’iyan,

Jama’a da ad da rabo fa sun kar~am mishi.

Wasu inda Shaikhu, wansu nana ga Bello,

Wasu kau ga Baffa Ati}u wansu Rufa’i.

Ta nuna cewa hatta shariffan Makkah da Madina da

mutanen Bagadaza da Sham (Syria) da Sin (China) da

Fizzan (Moroco) da Agadaz da Barno da Asbin da

Tumbuktu, sun kar~i kiran da Shehu Usmanu ya yi.

Haka kuma Moddibo ta yi addu’a da albarkacin

Babal Ati} da Dutsen Aswadu da Ha]imu da Rukunul

Yamani da Zamzam da Raula da Ba}i’a da abubuwa

masu girma da albarka na garin Makka da Madina da

sauransu, a kan Allah Ya isar mata tare da sauran

miskinan gari wa]anda wasu mutane suka ci amanarsu.

Jabbaru Sarki munka barku da shi duka,

Allah isam muna mu muna ta du’a’i.

Allah isam muna Rabbana ka isam muna,

Allah isam ma fa, kullufin miskini.

Modibbo Kilo ta yi garga]i da nasiha ga malamai da

sarakuna da ‘yan kasuwa da sauran su, da su bar

kasawa game da addinin Musulunci kuma su bar son

duniya. Ta ja hankalin mutane da su dubi rayuwar

hasara ta wasu mutanen da suka gabata domin su sami

darasi, misali Bal’amu wanda ya yi ilimin banza da

Fir’auna da ya yi ]agawar banza ta mulki da {aruna da

145

ya yi dukiyar banza da Barsusi da ya yi ibadar banza.

Hakanan ta }ara da ba da misalan mutane wa]anda

dangantaka ba ta amfane su ba, kamar Azara mahaifin

Annabi Ibrahim (alaihis salam) da Habila ]an Annabi

Adamu, (alaihis salam) da Kan’ana ]an Annabi Nuhu

(alaihis salam) da wasu dangin iyayen Annabi

Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) su Abu-Jahali

da Abu-Lahabi da Abu-[alib.

Wallahi masu fa iddi’a’in duniya,

Wallahi ku dubo Nasara bin Ishaq shi.

Wallahi malamai ku bar son duniya,

Kun san fa Bal’amu ya yi ilmin tasari.

Wallahi Fir’auna dubu fu]u duniya,

Domin Saraki au ku zanka tawalu’i.

‘Yan kassuwa ku tuni ku lura da duniya,

{aruna mali ya zamo masa tasari.

Dangane da mata ta kawo misalai na Wa’ilatu matar

Annabi Nuhu (alaihis salam) da Wa’ilatu matar Annabi

Lu]u (alaihis salam) wa]anda duk dangantakar aure ba

ta amfane su ba, saboda ]agawa da }in bin gaskiyar

addinin Musulunci. Daga }arshe Allah Ya la’anci duk

wa]annan mutane, suka halaka, ta ce ballantana mutum

wanda ya cuce su, da ta bayyana da Wazagi (wata

halitta mai siffa marar kyau), buddari (mai yawan tusa),

kuma Jaki kamar yadda ta ce.

146

Dibo ga Wa’ilatu fa matar Nuhu ta,

Har kau Wa’ilatu ga Lu]u ma]aukaki.

Ba su tsira ha}}an Rabbu ya la’ane su.

Dud bale ga Jaki Buddari Wazagi shi.

Moddibo ta yi godiya ga Allah da Ya ba ta ikon ri}e

kalmar shahada wadda ita ce asalin sunnar Annabi

Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) ba asalin

dangantaka ba. Moddibo ta ci gaba da kawo bayanin

wani mutum wanda ke zalunci da cuta, wanda ta kira

bahili mai }wa]ayi, wawa mai cin irlin mutane, mai

hasada kuma majanuni. A nan ta nuna cewa ba ta yafe

hakkinta da aka ci ba kuma sai ta neme shi a gaban

Allah.

Wallahi har talahi billahillazi,

Ban yarda hakki sai gaban mai mulki.

Har wa yau Moddibo ta ci gaba da bayanin cewa ba a

ta}ama da asali, sai dai bin Al}ur’ani mai girma. Ta

kawo misalin Shehu Usmanu [anfodiyo wanda ya ri}e

shari’ar Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa

sallam) da ‘yarsa Nana Asma’u wadda ba ta dogara da

asalin mahaifinta na zama Bafulatani Batoranke, mai

ilmi kuma mashahurin mujaddadi ba.

Mu ba ruwanmu da ai fa aslin duniya,

Sai dai fa aiki nan da kau {ur’ani.

Moddibo Kilo ta yi bayani dalla-dalla game da saukar

ta Jidda har zuwa garin Makkah inda ta yi wata bakwai,

sannan ta isa garin Madina, ta kuma sake dawowa

147

Makka, inda abokan tafiyarta biyu suka rasu, wato

Habsatu (Kurma) da Bagumbora. Ta ci gaba da bayanin

wuraren da ta fara zama a Makka, har lokacin da Allah

Ya ba ta gidan kanta. Ta ce ta zauna a unguwar

Sullu~awa, cikin wani gida wanda ta gyara a kan

ku]inta na halal Fam arba’in, bayan ta gyara, daga baya

sai aka ce mata wai gidan gado ne, to sai ta ha}ura ta

bar gidan, har can lahira wa]anda suka cuce ta su biya

ta hakkinta. Ga baitocin da suka yi bayanin haka:

Auwal gidan fa na Delu sabka tawa ni,

Ranas shigowata ga Jidda da Makka ni.

Bayan wata fa bakwai da niy yi ana kire,

Niz zo ni [aiba fa nan sana wahid ku ji.

Sannan fa nik komo rashin da]a Habsatu,

Har kau Bagumbora zama na Makka ji.

Niz zamni hara Sullu~awa nan kuma,

Can inda shai]ani ]iyan fa ]iya Hadir.

Nig gyara ai fa gida da nau fam arba’in,

Domin gidansu fa shidda shai]anun gari.

Bayan fa na gyara munafukkan }asa,

Sun ce gidan gado fa ni kau nif fici.

Ni} }yale samnoni fa har can lahira,

Sun sa shi can ga }ire suna murnoni.

Allah Shi rama min fa duniya lahira,

Allah Shi amsam min fa nawa halali.

148

Moddibo ta }ara bayyanin cewa ta zauna a wani wuri

Mukuwar wata shida, amma bayan maigidan wanda ya

shekara goma sha biyu, ba ya nan ya dawo, sai ta bar

gidan. Ta sake bayar da Fam shida ta shiga gidan wani

Aliyu Tabbaki a Unguwar Katsinawa, sai shi kuma ya

yi amarya ya sa a gidan, don haka Moddibo ta sake

barin nan. Ta sake zama a gidan wani Birgish da hayar

sule ]ari shida, a wata unguwa da ake ce wa Hara al

Yamal. Ga abin da ya zo cikin baitoci:

Niz zamni kau Mukuwar watana shidda ni,

Sai ga fa, mai fa gida fa, nif fici yas shigi.

Don shekaratai goma sha biyu ba shi nan,

Ni kau da niy yi kire da yaz zo nif fici.

Hara ta Katsinawa watana ukku na,

Na bada fam shidda sa’annan nis shigi.

Nan inda ai fa Aliyyu shi Tabbaki,

Sai yai amarya yas shige ni nif fici.

Niz zo gidan Birgish fa can Hartal Yamal,

Da sule ]ari shidda sana nan nis shigi.

Jabbaru Sarkin nan na Ahmadu Rahimi,

Nan Yay yi hikma kun da kun fa gare ni.

Bayan Modibbo ta shekara tara a Makka, a shekara ta

goma ne Allah Ma]aukakin Sarki ya ba ta ikon sayen

fili akan dutse a nan unguwar Hara al- Yamal. Ga

baitocin da ke xauke da wannan bayani:

149

Bisa ai fa ikon Rabbi Allah shi ka yi,

Niz zamni Makka sana tara ga ta goma ni.

Ga watan Rajab bana Rabbi Sarki Yai mini,

Hukuminsa albarkam Muhammadu nawa ni.

Nis sai fa dutci Kuntukur Hartal Yamal,

Wallahi fam sittin ina murnoni.

Da farko Modibbo ba ta sami gina filin ba, tana zaune

tare da hadimarta Kurma a cikin bukkar tsumma, kamar

Fulanin daji. Modibbo ta nuna ba ta damu da wannan

zama ba, saboda gado ta yi na irin zaman, daga Annabi

Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) da Mujadaddi

Shehu Usmanu [anfodiyo da kakanninta da mahaifinta

wa]anda suke muhajirai. Ga baitocin da ke qasa suke

qunshe da wannan magana:

Nib bar rabin dutci ina da]a hamdala,

Bukka ta ragga nit tsugunna nan ciki.

Da fa ni da Kurma can cikin kau daji,

Tamkaf fa Fillani, kiyo na fa wari.

Alhamdu lillahi zama ko na zamo,

Tamkar Rasulullahi nig gada fa ni.

Na gadi kakana fa babba Mujadaddi,

Don yai zaman Bukka fa Shaikhu ma]aukaki.

Na gadi kakanni fa nawa muhajirai,

Har kau ubana mallami Mahmudi.

150

Ya gode Allah yai zaman Bukkoki,

Har kau ubanai mallami Ashuri.

Moddibo Kilo ta yi bayanin inda za a same ta, ga wanda

yake bukatar gaininta, a can yalwataccen gidan da ta

mallaka. Ta ce a zo Unguwar Hara al Yamal kusa da

gidan malam Musa mai babbar riga. Wannan shi ne

kwatancin da za a bi, sannan a tambayi gidan Moddibo

Kilo ‘yar Al}alin Sakkwato Mahmuda. In sha Allahu za a

nuna wa mai tambayar gidanta wanda ke kan dutse. Ga

baitocin da suka kawo bayanin:

Wannan da yaz zam na bi]a ta Makka yau,

Hara Yamal shika zo gidan kau mallami.

Musa fa mai babbar fa riga kun jiya,

Ku ri}e kwatancin nan da niy yi da hamzari.

Sannan shi ce fa ina gidan Modibbo kau,

Kilo ~i fa }adi Sakkwato Mahmudi.

Sai kau a nuna mai gida bisa dutci,

Da]a babu }umci ga shi kau fa ma]aukaki.

151

Wa}ar Hatsin Bara

1.Wallai Baraya Alfa kun ji Bafa]ime,

Kakassu kau fa guda da Shaikhu Mujaddadi.

2. In don kitabi wallah ko Baubawa,

Wallai Sharifi na ga Raudi-jinani.

3. Komi sharifci naka ko fillanci,

Ko da fa Baubawa, ko fa Bahaushi.

4. Shi Shaikhu yay yi kira ajibu da’iyan,

Jama’a da ad da rabo fa sun kar~am mishi.

5. Wasu inda Shaikhu, wansu nana ga Bello,

Wasu kau ga Baffa Ati}u wansu Rufa’i.

6. Kaka ubanne har ]iya jikoki,

Sun ]auki himma har zuwan Mahdi shi ji.

7.{aba Muhajirrai tana da fa wauta,

Wannan da ad da fa imtihani, unzuri.

8.Wasu kau shariffai na na Makka, Madinata,

Bagadaza, Sinina wa]an Sham don ku ji.

9.Wasu kau na Firzan wansu Agadas Borno dut,

Wasu kau na Asbin wansu kau Tunbuti.

10.Sun yad da baladi nasu asli nasu dut,

Domin fa kau ya fi su asli sun sani.

152

11.Ko da fa Abdullahi Fodiyo kun jiya,

Ya kau bi]o ya bi shi babba Mujaddadi.

12.Sai kau fa Abdu Gidib-gidib fa Bafa]ime,

Shi as sharifi ba fa sai da kitabi.

13.Mun kau ri}o ha}}an batun fa Mujaddadi,

Da fa Bello, Abdullahi, ba mu tanazu’i.

14.Wallahi mun ga fa al’ajab ga fa Makka mu,

Zakkuwa ta Tukururai ]agawa Makka ji.

15An ba su Al}ali fa ga su shariffai,

Kuma ga karatu babu lotton masjidi.

16.Sun ]au ]agawa mai yawa babban gari,

Ga iddi’a’i inda miskinnan gari.

17.Sun dami miskinai na Makka da anniya.

Tamka Siriddawa ga Sakkwato don ku ji.

18.Sun ce shirifci babu mai shi sai fa su,

Da]a ga kitabi wanda yay yi mujaddadi.

19. Sun ce ubanne Sakkwatawa,

Shi af fa }umci Sakkwatawa so da }i.

20. Mai son fa labarin ubanai Sakkwato,

Sai dai shi yi gare su, ga fa shirifci.

21. Ga kumuwa nan nasu dubbai kau suke,

Ga turmuzai amre na kau tukuri.

153

22. Adassu ~acin muminai miskinnai,

Amma suna tsaro, ga kau dillanci.

23. Sa dud da shaikkokhinsu }auyawan gari,

‘Yan kasuwa duniya da kau dillanci.

24. Sa dud da fadawa barori nasu wai,

Da bugun gaba, sun dami miskinnan gari.

25.Bana mun ji ziza mai yawa babban gari,

Domin sarauta, wa fa }auyawan gari.

26. Albarkacin babal Ati}i da Aswadu,

Domin Ma}ama Multazim da Ha]imu shi.

27. Domin fa Hararu nan, na Isma’ila shi,

Rukunul Yamani Rabbu na yi du’a da shi.

28. Albarkacin Zamzam {uburan Anbiya,

Dut kafatan Makka abin da fa ac ciki,

29. Albarkacin Raula da Fujurar Annabi,

Mada Ba}i’a da kafatan fa, Madina ni.

30. Kuren miskini na Makka Madinata,

Ya ]au husumi, inda Allah {adiri.

31. Baban fa miskinnan Muhammadu Ahmadu,

Kure na miskini fa ba shi gamu da shi.

32. Jabbaru Sarki munka bar ku da Shi duka,

Allah isam muna mu muna ta du’a’i.

154

33. Kitaf fa irlin mumini nan Makkata,

{arya kakai kaicon ka }auyawan gari.

34. Ba don shari’a don muradin zucciya,

{aryakku ta yi yawa fa masu tanazu’i.

35. Allah isam muna Rabbana Ka isam muna,

Allah isam ma fa, kullufin miskini.

36. Kaiconka wawaye ka ce ma samu dai,

‘Yan kassuwa ‘yan dandi }auyawan gari.

38. Ko da Saraki, ko shiriffan gaskiya.

Ara~~e Makka fa iddi’a’i babu shi.

39. Kaicon ka wawa mai fa kibrin duniya,

Shai]an dubu fa takwas fa jannata ya fa ci.

40. Wallahi masu fa iddi’a’in duniya,

Wallahi ku dubo Nasara bin Ishaq shi.

41. Wallahi malammai ku bar son duniya,

Kun san fa Bal’amu ya yi ilmin tasari.

42. Wallahi Fir’auna dubu fu]u duniya,

Domin saraki au ku zamka tawalu’i.

43. ‚Yan kasuwa ku tuni ku lura da duniya,

{aruna mali yaz zamo ma tasari.

44. Mai zucciya ku tsaya ku bar son zucciya,

Hama za shi shiga cikin Tajjaini.

155

45. Ku ko fa jahillai kuna ta fa }unniya,

In kun }i duba tasarin ku biyun gari.

46. Mai iddi’a’in ko ibada jahili,

Ku tsaya ku dibo ba kamar Barsisi shi.

47. Ku ko fa kazibbai munafukkan gari,

Ku tsaya ku dubo kau Musailamu ya boni.

38. Mai iddi’a’i kaico wawa an tsaya,

Ka san fa Azara uban Ibrahimu shi.

49. Dibo ga {abila ka san ]an Adamu,

Ya zam ishara in kau mutakabbiri.

50. Dibo ga Kan’ana ka san ]an Nuhu na,

Jika na Shi’itu ya fa zam mai tasari.

51. Dibo Abu Jahali, Abu Lahabi fa shi,

Su a’ ubannen Ya Rasulu na Hashimi.

51. Dibo Abu kau [alibi fa ka ha}}a}e,

Asalin shirifci ya fito ga tsotsonsa shi.

52.Dibo ga Wa’ilatu fa matar Nuhu ta,

Har kau Wa’ilatu ga Lu]u ma]aukaki.

53. Ba su tsira ha}}an Rabbu Ya la’ane su.

Dud bale ga Jaki Buddari Wazagi shi.

54. Na tuba Allah am Ka gafarta mini,

Allah Ka sa ni zama ga masu tuwali’i.

156

55. Alhamdu lillahi fa }ulu La’ila h

Muhammadu shi af fa asli nawa ni.

56. Ni ban da asli sai fa sunna’ Annabi,

Shi kau fa {ur’ani da aiki na da shi.

57. Tozo da tattone idon azzalumi,

Domin liyar goma na miskinnan gari.

58. Ga }in shiri’a ga bahilci ga kwa]ai,

Kuma ga shi wawa ga fa kitar irli.

59. {asdan fa bagatatan fa babu dalili,

Allah tsare mu da hasidi majanuni.

60. Wallahi har tallahi billahillazi,

Ban yarda hakki sai gaban Mai mulki.

61. Ban yar da imani da kumya taku ma,

Ban yar da irli na ga kazziban gari.

62. Kuma ba ni hauka ban fita ga tawalu’i,

Domin fa banza Rabbi dai Ka isam mini.

64. Sai iddi’a’i ga takardu kun gani,

Wannan na banza ina ku zan ka tawalu’i.

65. Habbo juge fa shari’ar Annabi yar ri}e,

Hakanan fa Shehu Mujadaddi ba asli shi.

66. Ni na ga }aulin gwaggo Nana uwag gari.

Ita ta ]iyan nan kau ta Shaikhu Mujadaddi.

157

67.Shi mumina }arhen fa duniya kun jiya,

Sai dai la’if shi Makka har Mahadi shi ji.

68. Mu ba ruwanmu da ai fa aslin duniya,

Sai dai fa aiki nan da kau {ur’ani.

69. In babu hauka mai fa asli bai fa]i,

Don kau shirifci na ga Shehu Mujadaddi.

70. Dibo Abu kau [alibi da]a ya isa,

Baban Rasulullahi na dibo ka ji.

71. Mi ad da saura inda asli babu bi,

Hanyat tafarki masu asli sunka bi.

72. In ba ku fatawa khaliya,

Har rad da niy yi zama da dauri da yanzu ni.

73. Auwal gidan fa Na-Delu sabka tawa ni,

Ranas shigowata ga Jidda da Makka ni.

74.Bayan wata fa bakwai da niy yi ana }ire,

Niz zo ni [aiba fa nan sana wahid ku ji.

75. Sannan fa nik komo rashin da]a Habsatu,

Har kau Bagumbora zama na Makka ji.

76. Niz zamni hara Sullu~awa nan kuma,

Can inda shai]annai ]iyan fa ]iyan Hadir.

77. Wancan bahili na fa wagga munafuka,

Su biyu sha}iyyai kazibai na uhudi.

158

78. Tac ce ki zamni gidanmu ke fa ]iyata,

Sai kau fa mutuwa taki kazibban gari.

79. Mu ba mu kyauta ba mu kau kirazzuwa,

Kuma ba sayaswa ai kamar fa uwa ki ji.

80. Na gyara ai fa gida da nau fam arba’in,

Domin gidansu fa shidda shai]annun gari.

81. Bayan fa na gyara munafukkan }asa,

Sun ce gidan gado fa ni kau nif fici.

82. Ni} }yale samnoni fa har can lahira,

Sun sa shi can ga }ire suna murnoni.

83. Allah Shi rama min fa duniya lahira,

Allah Shi amsam min fa nawa halali.

84. Allah Shi sa shi zamo masiba tasu kau,

Duniya da barzahu lahira su yi tasari.

85. Niz zo ni har talfo ga [andukkani,

Nic ce }ire biyu tandu bawi don ku ji.

86. {arya munafucci ga mashin ta ta kau,

Namijin fa kibrin duniya da bakhalci.

87. Da son fa girma cin amana tar ri}a,

Yanke }eren gun ce da hali makiri.

88. Sherin Hadiza tana da }ulli nan garan,

Kullum dace ]an tcinta sai kuma nif fushi.

159

89. Sai abban uwassu Hakhar bilmustapha,

Shi amma askin Shaikhu nawa Mujadaddi.

90. Malam fa Muhmudu da Ummi Mustapha,

Wallai sha}i}}ai na irin hirzani.

91. Malam fa Mahmudu Abba Bukari fa nau,

Mai girgije rana zuwa Sifawi.

92. Shi malamin Almustapha kawunsa na,

Nan Shaikhu ya’ amsai shina marubuci.

93. Bubakar Bakiri fa bi mai, mai girgije,

Mai-rago abban }adi, Ahmadu Gandi shi.

94.Ahmadu abban Ru}ayyatu fa Basasi ne,

Modibbo ammin Arfatau fa uwa ku ji.

95.Amma uban Almustafa fa Basasi ne,

Amma uwassu sharifiya fir zani.

96. Shi kau fa abban ai Hajon muna Khadiru,

Baban ubanai fullo Janba}o ku ji.

97. Amma uwa abbansu af fa Basullu~a’,

Nan Makka sai fa ka ce ]iyas sarkin gari.

98. Ta doke jikanya’ Amirul muminina,

Fa shahidi nan Makka, don kishin gijim.

99. Sai jera }arya kulla yaumin kha’ina,

Kyauta ta kha’inci da kau fa nifa}i.

160

100. Bakin mil ni irin Almustafa,

Da]a ba ta kunya ba ta tsoron {adiri.

101. Wai Sullu~awa ‘yan uwan Usmanu na,

Nan Makka tabbashi na Shaihu Mujadaddi.

102. Dangi na ha~e, kaza da fillanin kiyo,

Har Maguzawa Makka yau Attoro]i.

103. Don imtihani wanda Allah Yai musu,

Nan Makka ya duj je shi, har Mahdi shi ji.

104. Niz zamni kau Mukuwar watana shidda ni,

Sai ga fa, mai fa gida fa, nif fici yas shigi.

105. Don shekaratai goma sha biyu ba shi nan,

Ni kau da niy yi kire da yaz zo nif fici.

106. Hara ta Katsinawa watana ukku na,

Na ba da fam shidda sa’annan nis shigi.

107. Nan inda ai fa Aliyyu shi Tabbaki,

Sai yai amarya yas shige ni nif fici.

108. Niz zo gidan Birgish fa can ciki Hartal Yamal,

Da sule ]ari shidda sana nan nis shigi.

109. Jabbaru Sarkin nan na Ahmadu Rahimi,

Nan Yay yi hikma kun da kun fa gare ni.

110. Dan nan fa baban Sakkwatawa dut duka,

Nan Makka }umcin kaffatansu sharifi.

161

111. Haushi da yak kama shi sai yak kumbura,

Da]a hasada take shina zazzagi.

112. Yac ce da mai fili da mai tsoro duka,

Har dud da mai fa gida shina zazzagi.

113. {asdan fa bagtatan, fa billahil lazi,

Da]a ba dalili shi fa a’ Al}ali.

114. Yac ce fa kakanai shirifi kun jiya,

Kakan uwata kau Gazali waliyyi.

115. Mun san fa Allah Shi ka yi ba ]an Adam,

Amma ku bar }arya ga masu dalili.

116. Icce ga daji ba ]iya ba inwa,

Kore na banza ya fito ga Ma]aukaki.

117. Kore ga daji kwance dai sai }una,

Samun fa nau fili fa, ya zama hasidi.

118. Na daina }aulin nan fa nasu, ha}i}a ni,

Da fa shi da Arzika nasu Allah Ya ishi.

119. Domin suna fa ganin mutane zay yawa,

Ni sunka rena don ina mai irli.

120. Ni} }yale samnoni da su da ]iyansu duk,

Don ba ni lalata cikin babban gari.

121. Jika na kawu Gagi da jikan ko Bunu,

Su anka aiko min gida don zagi.

162

123. Aiki na Arzika har da Maigandinsu kau,

Allahu Sarki Rabbi Yar rama mini.

124. Adassu ~acin manya-manya na Hausa dut,

Sun ce bale nan Makka wa miskini.

125. Don ba ni aiki, ba ni kau fa zuwan gari,

Da]a ba rubutu, ba karatu sun tafi.

126. Don babu aiki ko guda fa da ni’iya,

Sai dai karatu wirdi sai fa tawalu’i.

127. Bisa ai fa ikon Rabbi Allah Shi ka yi,

Niz zamni Makka sana tara ga ta goma ni.

128. Ga watan Rajab bana Rabbi Sarki Yai mini,

Hukuminsa albarkam Muhammadu nawa ni.

129. Nis sai fa dutci Kuntukur Hartal Yamal,

Wallahi fam sittin ina murnoni.

130. Don ba karatu ba rubutu yanzu nan,

Sa’a ta Mahdiyya ga kau miskini.

131.[ibar rabin dutci da darni har saye,

Sun tashi jikka ukku ramce munka yi.

132.Don babu tausai babu kau da]a taimako,

Da]a babu girma inda miskini ku ji.

133. Tamka} }iyama na zamana nan Makka yau,

Can lahira ga fa wanda ba shi da dini.

163

134.Da]a ga }iyayya ga jafa’i ga kuma,

Wallahi ramce ga ni kau fa ga dutci.

135. {asdan fa bagatatan da babu dalili,,

Ni} }yale samnoni ina ta tawalu’i.

136. Nib bar rabin dutci ina da]a hamdala,

Bukka ta ragga nit tsugunna nan ciki.

137. Da fa ni da Kurma can cikin kau daji,

Tamkaf fa Fillani, kiyo na fa wari.

138. Alhamdu lillahi zama ko na zamo,

Tamkar Rasulullahi nig gada fa ni.

139. Na gadi kakana fa babba Mujadaddi,

Don yai zaman Bukka fa Shaikhu ma]aukaki.

140. Na gadi kakanni fa nawa muhajirai,

Har kau ubana mallami Mahmudi.

141.Ya gode Allah yai zaman Bukkoki,

Har kau ubanai mallami Ashuri.

142. Wannan da yaz zam na bi]a ta Makka yau,

Hara Yamal shika zo gidan kau mallami.

143. Musa fa mai babbar fa riga kun jiya,

Ku ri}e kwatancin nan da niy yi da hamzari.

144. Sannan shi ce fa ina gidan Modibbo kau,

Kilo ~i fa }adi Sakkwato Mahmudi.

164

145. Sai kau a nuna mai gida bisa dutci,

Da]a babu }umci ga shi kau fa ma]aukaki.

146. Taron fa ‘yan dandi da makirran wuri,

Taron fa Shai]annai munafukkan gari.

146. Don sun }i Allah sun }i Annabi [ahiri,

Da]a ba su son {ur’an suna ta nifa}i.

147.Sun bar shi Allah, wallah ba su fa dibin,

Kanunsu balle ko su san unfani.

148. In don fa sun zo inda muminnai ku ji,

Tamkaw waliyyai sunka zam ga lisani.

149. Da ra]a }iren }arya cikin fa gidaddaji,

A su sami amfaninsu inda hisabi.

165

Babi Na Uku

Rubutun Zube

Labarin Manzancin Annabi Muhammad Da Halifancin

Sahabbai Da Mulkin Daular Usmaniyya

Bismillahi walhamdu lillahi wassalatu wassalamu ala

Rasulillahi

Ina farawa da sunan Allah, kuma godiya ta

tabbata gare Shi tare da salati da sallama ga manzonSa.

Allah Ma]aukakin Sarki Ya ce wa duniya, ‚Ke duniya

ki rayu tsawon ramzin Bismillahi, wato …tana

shu]ewa, shu]ewa da iradarSa.

Tsakanin rayuwar Adamu da Muhammadu,

manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam) shi ne,

Annabi Muhammad ya zo duniya bayan Annabi Adam

ya shekara dubu biyar da ]ari biyar da kuma arba’in

(5540) bisa doron }asa. Duk shekarun da ya yi a duniya,

bai yi kira ga mutane ba.

Annabi Muhammdu (sallallahu alaihi wa sallam),

ya zo kuma bayan ya cika shekara arba’in (40) da zuwa

ne, aka ba shi manzanci, ya yi kiran mutane na shekara

goma (10), ya yi jihadi na shekara goma sha uku (13).

Gaba]aya shekarun rayuwarsa a duniya, shekara sittin

da uku (63). Lokacin shugabancinsa duka-duka shekara

ashirin da uku (23). Ya yi hijira daga Makkatul

Mukarrama zuwa Madinatul Munawwara inda {ubba

take mai daraja, yana da shekara hamsin da uku (53).

Bayan Annabi kuma Manzon Allah, ya shekara goma

sha uku a Makka, sai ya yi hijira zuwa Madina kuma ya

166

zauna a can shekara goma (10) sannan ya }aura wato

ya rasu a can. Daga hijirarsa zuwa ga rubuta wannan

littafi shekara dubu ]aya da ]ari uku da tamanin da

bakwai (1387).

Bayan sa sai Abubakar Siddiq Allah Ya yarda da

shi, sai ya maye gurbinsa tsawon shekara biyu da wata

uku da kwana ]aya.

Bayan sa sai Sayyidina Umar Allah Ya yarda da

shi wanda ya yi halifanci shekara goma (10) da wata

uku, aka kashe shi ta hanyar soka masa wu}a a cikinsa,

yana sallar Asuba cikin masallacin Annabin Allah.

Bayan sa sai Uthman Bin Affan, wanda ya yi

shekara goma sha biyu (12) da kwana biyar, shi ma aka

kashe shi, ta hanyar fille masa kai a cikin masallacin

Manzon Allah, alhali yana zaune cikin Raular Manzon

Allah, Raular Aljanna ma]aukakiya, yana karatun

Al}ur’ani.

Bayan sa sai Khalifa Aliyu ]an Abu [alibi,

Allah Ya yarda da shi, ya yi halifanci shekara biyar, shi

ma aka kashe shi a Kufa da takobi bisa kansa tare

da ]an matarsa ( agola).

Bayan sa sai Husaini ]an Aliyu da Fa]imatuz

Zahara’u shugabar mata, Allah Ya yarda da ita. Ya yi

halifanci wata shida aka kashe shi ta hanyar fille masa

kai, gangar jikinsa na Misra kuma kansa yana Madina.

Bayan sa sai Hassan ]an Aliyu da Fa]imatu ‘yar

Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallam), ya yi

halifanci shekara biyu, sai aka kashe shi tare da

makidar matarsa Ja’adatu, Allah Ya la’ance ta.

Bayan sa sai Mu’awiya ]an Abi Sufyan, ya yi

halifanci shekara goma sha bakwai (17). Bayan sa sai

Yazidu ]an Mu’awiya, ya yi halifanci wata uku, bayan

sa sai Abdul-Malik ]an Marwan ]an Abu Hakim, ya yi

167

wata bakwai, bayan sa kuma sai (Umar) Bin Abdul-

Azeez, ya yi halifanci shekara sittin da wata goma sha

biyar, sannan ya rasu. Shekarunsu, Allah ne masani.

Daga }aurar Annabi Muhammad, manzon Allah

(sallallahu alaihi wa sallam) zuwa lokacin rubuta

wannan littafi, shekara dubu ]aya da ]ari uku da

tamanin da bakwai, (1387), hijirarsa daga Makka zuwa

Madina. Shekarun Aliyya ya rage shekara 113,

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Muna ro}on Allah

samun salama (aminci) da sa’ada wato rabo na gida

biyu (duniya da lahira) da kyakkyawar cikawa.

Bayan }aurar Manzo zuwa gidan rahama da

shekara ]ari hu]u da tamanin da bakwai, sai

Abdul}adir Al-Jelani, gausu kuma sarkin waliyai, ]an

Ummul Khairi ya bayyana, (wanda ya fito daga tsatson

Abubakar, mahaifinsa kuwa daga tsatson Aliyu). Bayan

tafiyar Abdul}adir zuwa ga rahamar Allah tsawon

shekara ]ari bakwai (700), sai Usmanu Mujaddadi,

hasken zamani kuma limamin waliyyai, ya bayyana.

Shekarunsa zuwa lokacin rubuta wannan littafi shekarar

Aliya ta cika ]ari da tamanin da bakwai. Abdul}adir

gausu, sarkin waliyai, ya ba wa Usmanu Mujaddadi tuta,

bayan saduwarsa da rahamar Ubangiji, shekara ]ari tara,

bayan barin sa duniya. Usmanu mujaddadi ya sami

shekara ]ari da hamsin da biyar 155, na barin sa duniya,

ha]uwarsa da rahamar Ubangiji. Shekarunsa a duniya

sittin da uku 63. Rayuwarsa da rasuwarsa zuwa lokacin

da nake rubuta wannan littafi, shekara ]ari biyu da

goma sha takwas (218), shekarar Aliyya tamanin da

uku da kuma shekara bakwai, lokacin da aka kashe

Ahmadu ]an Ibrahim ]an Sarkin Musulmi Abubakar

Atiku Ra~ah, ]an Sarkin Musulmi mujaddadi na biyu,

Muhammadu Bello, ]an Sarkin Musulmi mujaddadi

168

Usmanu hasken zamani. Ahmadu Sardauna, ya rasu

yana mai shahada bisa ga cikar Musulunci hannun

kafiran Enugu, Allah Ya la’ance su amin. Saboda

cikawar lokacinsa ya zo, kamar yadda Allah Ya ce,

‚Wa iza ja’a ajaluhum la yasta’khiruna sa’atan wala yastaqdimun‛ a lokacin shekarar Aliyya ta cika shekara

tamanin da shida 86, lokacin da shahidi Ahmadu

Sardauna ya rasu, Allah Ya yarda da shi, da ni, da

sauran Musulmi da muminai, amin.

Bismillahi Wal Hamdu Lillahi Was Salatu Was Salamu Ala Ashrafil Mursalina.

Farkon Al’amarin Mujadaddi Nuruz Zamani,

Ya tsayu ga kiran mutane zuwa ga Allah, gabas da

yamma, kudu da arewa bayan ya cika shekara arba’in

(40) domin rayar da addini da kuma kau da kafirai

tsawon shekara goma, sannan ya yi hijira, ya yi jihadi

da kafirai. Farkon jihadinsa da hijirarsa da Yunfa,

la’anar Allah ta tabbata a gare shi, ]an Bawa

Jangwarzo, la’anar Allah ta tabbata a gare shi, a cikin

garinsa Gobir Al}alawa, tsawon shekara goma

sha ]aya (11), addinin Allah ya cika ga hannun

mujaddadi Usmanu cikin shekaru ishirin da ]aya (21),

bayan wa]ancan shekaru arba’in da ya yi. Sannan ya

shiga garinsa Sakkwato, ya zauna cikinsa tsawon

shekara biyu (2). Sai ya cika shekara sittin da uku

daidai, sai ya rasu, ya yi }aura zuwa ga rahamar

Ubangiji, Allah Ya yarda da shi. Wato shekarunsa a

duniya, kamar na shugaban talikai, Manzon Allah

(sallallahu alaihi wa sallam) na kira da jihadi. Godiya ta

tabbata ga Allah, bisa ga cikar ni’imarsa ga mujaddadi

Shehu Usmanu a duniya da barzahu da lahira. Ya koma

169

ga rahamar Allah ranar Litinin, uku ga watan Jimada

Akhir, shekara ta dubu da ]ari biyu da talatin da biyu

(1232), hijirar kakansa, Manzon Allah (sallallahu alaihi

wa sallam). Haihuwarsa ranar Litinin da asuba, sha

biyu ga watan Rabi’ul Auwal, ya kuma shigo garin

Sakkwato ranar Litinin, sannan rasuwarsa ranar Litinin

zuwa ga rahamar Ubangiji. Shekarunsa kamar

shekarun shugaban talikai.

Labarin haihuwar mujaddadi Shehu Usmanu ya

zo daidai da shekara sittin da tara na ro}on da

Umar ]an Kha]]abi ya yi, na shekara ]ari, bayan

ro}on da Abubakar Siddiq ya yi (na shekara ]ari)

(Allah Ya yarda da shi), amin. Kuma mujaddadi ya

sami shekara talatin da ]aya na ro}on da Usman ]an

Affan ya yi na shekara ]ari, bayan ro}on da Umaru ]an

Kha]]abi ya yi na shekara ]ari.

Sa’ad da Shehu Usmanu ya cika shekara arba’in

da haihuwa, lokacin ne aka umarci Gausu, sarkin

waliyyai, ]an Ummul Khairi, wancan Abdul}adir

Jelani kuma Kailani, da ya ba shi tuta. (Allah Ya yarda

da shi) Allah Ya ba mu albarkacin sa. Ya ba shi tuta

saboda kiran mutane ga addini da yin hijira da jihadi

cikin garin la’anannu kafirai, Allah Ya la’ane su, amin,

wato Yunfa da jama’arsa izuwa yanzu, saboda

kamannunsu da halayen kafirai.

Farkon kiran Usmanu ya sami shekara goma

cikin ro}on da Usmanu ]an Affan ya yi na shekara ]ari,

Allah Ya yarda da shi. Kuma dai ya sami shekara

ishirin da biyu da kiran da ya yi da jihadinsa tare da

hijirarsa da barin garin [egel, sannan ya amfana da

shekara talatin da biyu, cikin ro}on da Usmanu ]an

Affan ya yi na shekara ]ari, bayan mujaddadi ya cika

170

shekara sittin da uku 63, sai ya koma ga rahamar

Ubangijinsa. Allah Ya yarda da shi, amin.

Labarin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello

Labarin Muhammadu Bello mataimaki, mujaddadi na

biyu ga mahaifinsa. Al’amarin sarautarsa ya zo masa a

shekara ta talatin da uku (33) daga cikin shekara ]ari

wa]anda Usmanu ]an Affan ya ro}a. Allah Ya ba

Muhammadu Bello shekara ishirin da ]aya (21) yana

mulki bayan mubaya’ar da dukkan mutane suka yi

masa. Bayan su (shekarun), sai ya koma zuwa ga

rahamar Allah.

Labarin Abubakar Atiku Sha}i}in Muhammadu Bello

Labarin Abubabakar Atiku, wanda ya tsira daga wuta,

sha}i}insa shi ne Muhammadu Bello, wanda ya yi

shahada a garin Katsina a gaban Gobirawan Katsina,

‘ya‘yan Alko, la’anar Allah ta tabbata a gare su. Shi

kuma Alko ]an Bawa Jangwarzo, la’anar Allah ta

tabbata gare shi da jama’arsa, amin, saboda

kamannunsu da halaye irin na kafirai har zuwa yanzu.

Wa]annan su ne kafiran Katsina, dalili kuwa shi ne,

harbe tutar mujaddadi hasken zamani da suka yi da

kuma ]ansa Amirul muminina (Muhammadu Bello).

{u]bu Atiku wanda ya tsira daga wuta. Duk wanda ya

harbi tutar mujaddadi, ha}i}a ya harbi tutar Manzon

Allah (sallallahu alaihi wa sallam). Allah Ya la’anci

mutanen Ha~e na Katsina, amin.

Jama’ar Musulmi sun yi wa Atiku mubaya’a,

bayan sha}i}insa Bello, game da sha’anin sarautarsa,

wadda ta yi daidai da shekara hamsin da takwas cikin

shekara ]ari da Usman ]an Affan ya ro}a. Shi Atiku ya

shekara biyar yana sarautar Sarkin Musulmi, sannan ya

171

rasu zuwa }ofar Firdausi. Ga baitin wa}a game da

harbin tutar masu albarka:

Fa kwaj ja da mai }arfi ku san shi ka fa]uwa,

Fa kwah halbi tutas Shehu ya halbi Ahmada.

Labarin Sarautar Aliyu [an Muhammadu Bello

Ya hau gadon sarauta a cikin shekara hamsin da bakwai

(57) na shekara ]ari da Usman ]an Affan ya ro}a kuma

ya yi mulki shekarar Usmaniyyar ta saba’in da biyar

(75), bayan mubayi’a da jama’a suka yi masa, sannan

ya koma ga rahamar Allah.

Labarin Sarautar Ahmadu [an Atiku

Game da sarautarsa (Ahmadu ]an Atiku), ya yi ta ne a

cikin shekara ta tamanin da biyu (82) na shekara ]ari da

Usmanu ]an Affan ya ro}a, sannan ya koma ga

rahamar Ubangiji.

Labarin Sarautar Aliyu {arami [an Muhammad Bello

Game da al’amarin sarautarsa, ta kasance shekara ta

tamanin da uku na shekara ]ari da Usman ]an Affan ya

ro}a, sannan ya koma ga rahamar Ubangiji.

Labarin Sarautar Ahmadur Rufa’i [an Mujaddadi Usmanu

Allah Ya ba wa Ahmadur Rufa’i ]an mujaddadi

Usmanu Nuruz Zamani, {u]ubi, Allah Ya yarda da shi

sarauta, a cikin shekara ta tamanin da tara na

shekara ]ari da Usman ]an Affan ya ro}a, sannan ya

koma ga rahamar Ubangijinsa.

172

Labarin Sarautar Abubakar Atiku {arami Mai Ra~ah

[an Muhammadu Bello

Al’amarin sarautarsa ya kasance a shekara ta casa’in da

hu]u na shekara ]ari da Usman ]an Affan ya ro}a,

sannan ya koma ga rahamar Ubangiji.

Labarin Sarautar Mu’azu [an Muhammadu Bello

Al’amarin sarautarsa ya kasance a shekara ta casa’in da

takwas na shekara ]ari da Usman ]an Affan ya ro}a,

sannan ya koma ga rahamar Ubangiji.

Labarin Sarautar Umaru [an Aliyu

Al’amarin sarautarsa ya kasance, shekara biyu na cikon

shekara ]ari da Usman ]an Affan ya ro}a, kuma

ya }ara shekara takwas cikin farkon shekara ]ari da

Aliyu ]an Abu Talib ya ro}a, sannan ya koma ga

rahamar Ubangiji.

Labarin Sarautar Abdu [an Atiku [an Mujaddadi Usmanu

Allah Ya ba shi sarauta, a cikin shekara ashirin na

shekara ]ari da Aliyu ]an Abu Talib ya ro}a, sannan ya

koma ga rahamar Ubangiji, kuma lokacin ne, cikon

shekara ishirin na farkon shekara ]ari na Aliyya, kuma

sa’annan ne Ahlul Kitabi (Turawa), la’anar Allah ta

tabbata a gare su, amin, suka shigo Sakkwato don ~ata

addini a }asa, bisa }udurar Ubangiji, wanda

yake }addaro wa mutane zamani.

Shi ne farkon cikon shekara ashirin na

shekara ]ari da Aliyu ]an Abu Talib ya ro}a, ro}onsa

cikin shekara ]ari da aka ba wa Aliyu, cikin ro}onsa na

shekara ]ari, lokacin rubuta wannan littafi daidai da

shekara tamanin da shida, lokacin da Ahmadu ]an

Ibrahim ]an Atiku Ra~ah ]an Muhammadu Bello ]an

173

mujaddadi Shehu Usmanu, wanda aka sani da Ahmadu

Sardauna, Allah Ya yarda da shi, ya koma ga

Ubangijinsa, yana mai shahada, a hannun kafiran

Enugu, la’anar Allah ta tabbata a gare su. Ahmadu ya

koma zuwa ga }ofar aljanna, ya zauna tare da

kakanninsa, a lokacin shekara goma sha hu]u suka rage

daga ro}on da Aliyu ]an Abu [alibi ya yi na

shekara ]ari, domin shekara tamanin da shida sun cika,

na kammalar shekara ]ari hu]u bayan dubu. Abin da ya

rage na shekarun, shekara goma sha uku lokacin da

nake rubuta littafina, a lokacin shahadar nan ta Ahmadu

Sardauna. Allah ne Masani ga muradinSa.

Labarin Sarautar Attahiru [an Ahmadu

Tsawon sarautarsa wata shida, ya koma wa Ubangijinsa

tare da kakanninsa wa]anda suke zaune bakin }ofar

aljanna, ya rasu yana shahidi a hannun kafiran Bani-

Isra’ila, la’anar Allah ta tabbata a gare su, amin.

Labarin Sarautar Attahiru [an Aliyu Babba

Ya yi sarauta cikin shekara ]ari ]in da Aliyu ]an Abu

Talib ya ro}a, sannan ya koma ga rahamar Ubangiji.

Labarin Sarautar Muhammadu [an Ahmadu

Allah Ya ba shi sarauta a cikin shekara ta arba’in da

biyu da wata biyar cikin shekarun da Aliyu ]an Abu

Talib ya ro}a, sannan ya koma ga rahamar Ubangiji.

Labarin Sarautar Muhammadu [an Muhammadu

Allah Ya ba wa Muhammadu [an Muhammadu, adili

ga addini, sarauta a cikin shekara ta arba’in da tara ban

da wata guda, cikin shekara ]ari da Aliyu ]an Abu

Talib ya ro}a, sannan ya koma ga rahamar Ubangiji.

174

Labarin Sarautar Hassan [an Mu’azu

Allah Ya ba Hassan ]an Mu’azu sarauta, a cikin

shekara ta hamsin da shida da wata takwas a cikin

shekara ]ari ]in da Aliyu ]an Abu Talib ya ro}a,

sannan ya koma ga rahamar Ubangiji.

Labarin Sarautar Abubakar [an Usmanu

Allah Ya ba Abubakar ]an Usmanu raba gardama, ]an

Mu’azu ]an Muhammadu Bello, ]an mujaddadi

Usmanu, hasken zamani, Allah Ya ba mu albarkacin sa

amin, sarauta a cikin shekara ta tamanin da bakwai a

cikin shekara ]ari ]in da Aliyu ]an Abu Talib ya ro}a.

Allah Ya tsawaita shekarunsa har zuwa saduwarsa ga

Muhammadul Mahdi. Shi ne Sarkin musulmi,

mujaddadi na goma sha biyu, mujaddadin }arshen

mujaddadai har zuwa ranar Al}iyama. Allah ka sanya

mu cikin jama’arsa, amin. Wato abin da ya rage cikin

shekara ]ari ]in da Aliyu ]an Abu Talib ya ro}a,

shekara goma sha uku. Allah ne Masani ga muradinSa.

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Wannan shi

ne }arshen }idayar shekara dubu da ]ari hu]u.

Tare da }arewar wannan tarihi, muna ro}onKa

Ya Allah, kada Ka sa mu cikin mutanen da Ka ke yi wa

u}uba, amin. Bayan wannan bayani, Shehu Usmanu ya

yi mulki na tsawon shekara ashirin da uku, sannan mai

bi masa Muhammadu Bello wanda ya shekara ashirin

da ]aya, sannan Abubakar Atiku, shekara biyar, sannan

mai bi masa Aliyu ]an Muhammadu Bello ya shekara

goma sha bakwai, sannan mai bi masa Ahmadu ]an

Atiku, shekara bakwai, sannan mai bi masa Aliyu na

biyu, wata goma, sannan mai bi masa Ahmadur Rufa’i,

shekara shida, sannan mai bi masa Abubakar

Atiku ]an Muhammadu Bello, shekara biyar, sannan

175

mai bi masa Mu’azu ]an Muhammadu Bello, shekara

hu]u, sannan mai bi masa Umaru ]an Aliyu, shekara

tara da wata tara, sannan mai bi masa Abdu na Garba,

shekara goma sha biyu, sai mai bi masa Attahiru ]an

Ahmadu, wata shida, sai mai bi masa Attahiru ]an

Aliyu, shekara goma sha biyu da wata tara, sai mai bi

masa Muhammadu ]an Ahmadu, shekara tara da wata

biyar, sannan mai bi masa Muhammadu ]an

Muhammadu, shekara shida da wata shida, sai mai bi

masa Hassan ]an Mu’azu, shekara bakwai da wata

bakwai, sannan mai bi masa Abubakar ]an Usmanu

raba gardama, yana da shekara talatin da wata takwas

bisa gadon sarauta, a lokacin rubuta wannan littafi.

Modibbo Kilo ta kawo jadawalin sunayen

wa]annan shugabanni na Daular Usmaniyya goma sha

bakwai, kamar yadda suka zo a }asa, sai dai ita ta kawo

su ne cikin tsarin hatimi: 1. Usmanu

2. Bello

3. Atiku

4. Aliyu

5. Ahmadu

6. Aliyu

7. Ahmadur Rufa’i

8. Abubakar

9. Mu’azu

10. Umaru Aliyu

11. Abdu na Garba

12. Attahiru Ahmadu

13. Attahiru Aliyu

14. Muhammadu Ahmadu

15. Muhammadu Tambari

16. Hassan Mu’azu

17. Abubakar Usman

176

Wa]annan su ne sarakuna goma sha bakwai na wannan

daula daga mujaddadi Shehu Usmanu zuwa Abubakar.

Labarin ‘Yan’uwan Mujaddadi Usmanu

‘Yan’uwansa na wajen mahaifinsa, babbansu duka

Mamman Yaro, sannan Aliyu sai Shaihu Usmanu sai

Abdullahi sai Abubakar sai Adde sai Alfa Umaru sai

Na’inna sai kuma Abdullahi. Mazansu tara. Matansu

uku, su ne Maunuma sai Saudatu sai ‘Yargwaggo.

Dukkansu uwarsu ]aya, ubansu ]aya. Don haka

‘yan’uwansa goma sha biyu ne,

‘Ya’yan mahaifiyarsa shida ne. Farko cikin

‘ya’yan mahaifiyarsa, shi ne Aliyu, sannan mujaddadi

Usmanu nuruz zamani, sai Abdullahi Gwandu, sai

Maunuma, sai Saudatu, sai ‘Yargwaggo. Dukkaninsu

‘ya’yan Hauwa’u Sharifiya ne, daga tsatson

Hassan ]an Fa]ima ‘yar Manzon Allah (sallallahu

alaihi wa sallam) da Aliyu ]an Abu [alibi. Tsakaninta

da Hassan maza shida ne.

Sai ‘yan’uwansa na wajen uba, na farkon su

Mamman Yaro Fodiyo (Allah Ya yarda da shi), sai

Abdullahi, sai Abubakar sai Adde sai Alfa Umaru sai

Na’inna. Dukkansu shida ubansu ]aya. Wannan shi ne

labarin ‘ya’yan mahaifinsa da mahaifiyarsa.

Labarin Matan Shehu Usmanu

Matarsa ta farko ita ce Maimunatu, ‘yar’uwarsa kuma

‘yar kawunsa Allah Ya yarda da ita, sai matarsa Gab]o

ita ma ‘yar’uwarsa, ‘yar kawunsa, sai Hauwa’u wadda

ake wa la}abi da Inna Garka, ‘yar Ali Bankeju, sai

Hajju Maranno, sai Janni, sai Shaturu Gumborankeju,

sai Jumbajju, sai Hafsatu, sai Ta-baraya, sai Asma’u,

177

sai Fure, sai Hadijatu Kugga, sannan sa]akarsa

Mariyatu. Allah Ya yarda da dukansu.

Labarin ’Ya’yan Shehu Maza Da Mata

‘Ya’yan Shehu maza da mata guda talatin da tara ne.

‘Ya’yan Maimunatu goma sha ]aya ne, maza takwas,

mata, uku kamar haka:

Maza

1. Aliyu 2. Muhammadu Hajo 3. Muhammadu Alsana 4. Muhammadu 5. Umaru 6. Hassan 7. Husaini 8. Hassan na 2

Mata

1. Habsatu 2. Nana Uwar gari 3. A’ishatu

Dukkaninsu ’ya’yan Maimuna ne da ta haifa tare da

Shehu.

[iyan Gab]o su takwas ne

Babban ]ansa ya haife shi ne, tare da Gab]o, shi

ne babba cikin dukkanin ’ya’yansa maza da mata,

wannan shi ne Muhammadu Sa’adu.

178

Maza

1. Muhammadu Sa’adu 2. Muhammadu Sambo 3. Muhammadu Buhari 4. Muhammadu Firabri

Mata

1. Kadijatul Kubura, ita ce babbar ‘yarsa cikin mata 2. A’ishatu 3. Juwairatu 4. Aminatu

[iyan Hauwa’u wadda ake yi wa la}abi da Inna

Garka, ]iyar Kwaira Ali Bankejo

Maza

1. Muhammadu Bello 2. Abubakar Atiku

Mata

1. Saudatu 2. Fa]imatu 3. Hannatu

[iyan Hajju

Mace

A’isha ce kwai wadda ta rasu a Tukayam.

[iyan Janni su biyu ne

Namiji

Haliru wanda ya yi shahada a Alwasa, wurin ya}i da

Sarkin Adar Abungulu, }anen Keju, Allah Ya la’ance

shi.

179

Mace

Safiya.

[iyan Shaturu ]iyar Shekhun Nuri, Gamborankeju, duk

‘ya’yanta maza ne.

Maza

1. Ahmadul Badawi 2. Abdul Hassan 3. Ash-shazali 4. Ahmadur-rufa’i

[iyan Hajo Maranno uban Aliu Hawa biyu ne:

Namiji

1. Abdul-}adiri Landiju, wanda ya yi shahada a

Zamfaran Keju, la’anar Allah ta tabbata ga

jama’ar arnan Keju Mace

1. Fa]imatu [iyan makubliyarsa Mariyatu su bakwai ne, maza

uku, mata hu]u

Maza

1. Muhammadu 2. Ibrahim Dasuki 3. Isa Mai Kware

Mata

1. Aminatu 2. Hadijatu 3. Hajaru 4. Maryam

Wannan shi ne }arshen labarin ‘ya’yan Shehu Usmanu

talatin da tara, maza ishirin da biyu, mata sha bakwai.

180

Muhammadu Sa’adu shi ne babban ]ansa,

sannan na biyunsu Aliyu babban ]an Maimunatu,

mahaifiyar Nana Asma’u uwargari, sai na ukunsu

Muhammadu Sambo ]an Gab]o, na hu]unsu shi ne

Muhammadu Bello ]an Hauwa’u ]iyar Kwaira, wadda

ake yi wa la}abi da Inna Garka. Isa mai Kware shi

kuwa, mahaifinsa mujaddadi Usmanu ya bar shi

yana ]an shekara uku, wanda shi ne }arshen haihuwar

Shehu a Gwandu, ya rasu yana da shekara hamsin da

tara. Bayan rasuwarsa da shekara ]aya, Ahmadur-

Rufa’i ya rasu, hakanan Uwar daje. Ita kuma Maryam

sai ta rasu bayansu, a }arshen sarautar Umaru ]an

Aliyu. Dukkansu sun ha]u da rahamar Ubangiji.

Jikokin mujaddadi Shehu Usmanu maza da mata

kuwa, dukkansu su ]ari biyar da hamsin ne. Dukkansu

sun koma ga rahamar Ubangiji. Allah Ka ba mu

albarkacinsu, amin.

Labarin ’Ya’yan Muhammadu Bello

’Ya’yan Muhammadu Bello su sittin ne. Maza talatin

da biyu, mata ishirin da takwas.

[ansa na farko shi ne Muhammadu Sa’adu, sai

Haliru sai Usmanu, sai Sarkin Musulmi Aliyu (babba),

sai Sarkin Musulmi Aliyu }arami, sai Umaru, sai

Junaidu, sai Sarkin Musulmi Mu’azu, sai Sa’idu, sai

Yahaya, sai Abdul}adiri, sai Muhammadu, sai Usmanu

na biyu, sai Abdul}adiri na biyu, sai Ibrahima, sai

Musa, sai Mallam Jabbo, sai Muhammadu Sa’adu na

biyu, sai Muhammadu Fodiyo, sai Umaru na biyu, sai

Abdullahi, sai wani Muhammadu, sai Sarkin Musulmi

Abubakar wanda ake yi wa la}abi da Atiku Mai-Ra~ah,

sai Muhammadul Buhari, sai Ahmadu, sai

Abdurrahmani, sai Khalidu, sai Yusufu, sai

181

Abdurra’ufu, sai Muhammadu kuma, sai kuma Ahmadu,

sai Hammadani. ‘Yayansa mata kuwa su ne, Khadijatu

da A’ishatu da Fa]imatu da wata Khadijatu da

Fa]imatu kuma da wata A’ishatu da wata Fa]imatu da

Maryamu da wata Fa]imatu da wata Khadijatu da

Hannatu da Zainabu da wata Ai’shatu da Maimuna da

Fa]imatu kuma da Khadijatu kuma da A’ishatu kuma

da Hauwa’u da Rahmatu da Rabi’atu da Khadijatu

kuma da wata Rabi’atu da wata Khadijatu da Maryam

kuma da Fa]imatu kuma da Hauwa’u kuma da

Fa]imatu kuma da wata Khadijatu.

Labarin Rasuwar ’Ya’yan Shehu Usmanu Muhammadu Sa’adu ya rasu yana da shekara ishirin da

biyar ko goma sha takwas, yana cikin }uruciyarsa da

safiyar sallar fi]iri, wato sallar azumi, sanadin idanun

mutane, sai Aliyu ]an Maimunatu, sai sha}i}insa Sambo,

wanda ya rasu ranar Laraba, yana ]an shekara arba’in da

bakwai, ’yarsa guda ]aya tilo, sunanta Ukhtiya. Bayansa

sai Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, ya rasu yana da

shekara sittin ranar Alhamis da safe, cikin watan Rajab

Hijirar Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) dubu da ]ari

biyu da hamsin da takwas 1258. Bayan rasuwarsa sai

rasuwar sha}i}insa Abubakar Ati}u, ya rasu, hijirar

Annabi na da shekara dubu da ]ari biyu da sittin da uku

1263, yana ]an shekara sittin da biyu. Sai rasuwar

Muhammadu Alsana, sannan Umaru, sannan

Muhammadul Buhari gulbin ilmi, yana da shekara hamsin

da biyar, cikin hijirar Annabi ta shekara dubu ]aya

da ]ari biyu da hamsin da biyar 1255. Sai rasuwar

Muhammadu Sabiru da Muhammadu Mahe, da Hassan

gulbin ilmi, ranar Assabar, yana ]an shekara ishirin da

biyar, hijirar Annabi, dubu ]aya da ]ari biyu da talatin da

uku, an kuma binne shi bayan mahaifinsa. Bayan

182

rasuwarsa, sai rasuwar Abdul}adiri Landijo gulbin ilmi,

ya rayu na kirki, ya kuma rasu shahidi, yana ]an shekara

ishirin da takwas, hijirar Annabi dubu ]aya da ]ari biyu

da hamsin 1250, sai shahidi Haliru da Ibrahimu da

Ahmadur- Rufa’i da Abul-Hassan As Shazali da

Muhammadu da autansa Isa lokacin ro}on Usmanu ]an

Affanu na da shekara tamanin da takwas, hijirar Annabi

kuwa na da dubu da ]ari biyu da tamanin da takwas 1288

bayan rasuwar Ahmadur Rufa’i da shekara ]aya, hijirar

Annabi kuwa na da dubu ]aya da ]ari biyu da tamanin da

tara 1289. Maryam Uwad Daje ta rasu bayan shekara

goma sha shida da rasuwar Ahmadur Rufa’i, wadda ta

rasu ranar goma shah u]u ga watan Azumi. Wannan shi

ne }arshen mutuwar ’ya’yan mujaddadi nuruz zamani.

Labarin Abdullahi [anfodiyo

Abdullahi [anfodiyo shi ne sha}i}in Shehu Usmanu

[anfodiyo kuma wazirinsa, ]alibinsa, hadiminsa, kuma

masoyinsa. Ya samu albarkar Shehu mai yawa, malamin

maluma bayan Shehu, shi ne ]an auta ga mahaifiyarsu

Hauwa’u, sharifiya daga asalin Hassan ]an Aliyu ]an

Abi-[alib da Fa]ima, sai aka ambace shi Abdullahi Toga,

bamasaren Hausa, tsakanin haihuwarsa da Shehu Usmanu

shekara goma, rasuwarsu kuma shekara goma sha uku a

tsakani. Abdullahi ya rasu yana da shekara sittin da shida,

ranar Laraba, shekarar hijirar Annabi ta dubu da ]ari biyu

da arba’in da biyar. (1245) Tsakanin rasuwarsa da

rasuwar Shehu shekara goma sha uku.

Labarin ’Ya’yan Abdullahi Fodiyo

Daga cikin ‘ya’yansa akwai xiyansa talatin da tara kamar

na sha}i}insa. Na farkonsu, Muhammdu tekun ilmi,

shekararsa arba’in da bakwai sannan ya rasu, lokacin

hijirar Annabi na da shekara dubu da ]ari biyu da hamsin,

sai Khalilullahi tekun ilmi, sannan Aliyu mai Laga sannan

183

Muhammadu Sambo, sai Abdul}adiri, sannan Haliru, sai

Abubakar, sai Hassan sai wani Abdul}adiri, sai Abdur

Rahman, sai Isha}a da sauransu da dama. Cikin ‘ya’yansa

mata akwai A’ishatu, sai Khadijatu sannan wata A’ishatu,

sai Fa]imatu sai Maimunatu, sai Zainabu sannan wata

Khadijatu sai wata A’ishatu da sauransu da dama maza da

mata. Dukkansu sun koma zuwa ga rahamar Ubangijinsu.

Allah Ya yarda da dukkaninsu. Wannan shi ne }arshen

maganata game da bincike a kan kakannina. Godiya ta

tabbata ga Allah, salati da sallama su tabbata ga Manzon

Allah (sallallahu alaihi wa sallam). amin.

184

Babi Na Huxu

Waqoqi a Kan Modibbo Kilo

Wa}o}in Fa]ima Zuwa Ga Modibbo Kilo

Ko da dai akwai wa}o}in da aka rubuta a kan Modibbo

Kilo, wa]anda suka zo ga hannu kurum su ne wa}o}in

da Modibbo Fa]ima, aminiya kuma masoyiyar

Modibbo Kilo ta addini, ta rubuta a kan ta ko zuwa gare

ta.

Kamar yadda aka yi nazarin wa}o}in da

Modibbo Kilo ta rubuta a babi na biyu, za a bi hanya

guda wajen gabatar da wa]annan wa}o}i domin a gane

sa}on da ke cikinsu.

Nazarin Wa}ar Ha]uwar Fa]ima da Modibbo Kilo

A baiti na 1 zuwa 2 Modibbo Fa]ima ta bu]e wa}arta

da godiya ga Allah da ambaton Annabi Muhammad

(sallallahu alaihi wa sallam) da Sahabbansa da alayensa

kamar haka:

Bismil ilahi }ultumu kam hamdala,

Sarkimmu kam Ya ba mu, mun gode maSa.

Mun kau bi Manzonai Nabiyyi abin sani,

Hakanan Sahabbainai da Alaye nasa.

Modibbo Fa]ima ta nuna cewa, a koyaushe tana da

ro}on da take yi ga Allah, na su zo garin Mujaddadi

Shehu Usmanu [anfodiyo da kuma Makka da Madina.

185

A nan, ta nuna cewa Allah Ya biya musu bukata ta

farko saura ta biyu:

Shi munka ro}a duk bu}ata kamilan,

Yab ba mu ]ai, saura fa biu ku sani nasa

Yab ba mu, mun tafi Hausa inda Mujadaddi, Saura mu zo Haramaini can Baiti nasa.

Daga can da]a mu wuce Madina muna raha,

Can inda Al-Mukhtari don nasara tasa.

Allah Shi sa, Allah Shi sa, Allah Shi sa,

Kilo Allah sanya da mu cikin yarda tasa.

A baiti na 8 da 10, jigon wa}ar ya fara bayyana saboda

burin Fa]ima ya cika, da ta sami abin da take nema,

wato ganin Modibbo Kilo kuma abin da take fatan

samu nan gaba shi ne shiga Aljanna Firdausi tare da

Modibbon .

Daga dukkanin alamu, Fa]ima ta yi ta samun

labari game da Modibbo Kilo, kuma wannan ita ce

ha]uwar farko tsakanin wa]annan Modibbai har

Fa]ima tana cewa, duk yadda take zaton ta ga Modibbo

Kilo haka ta gan ta sai ma abin da ya zarce tsammaninta.

Ta yi bayanin ta da cewa mai annuri ce, mai koyi da

Annabi Muhammad (sallallahu alaihi wa sallam) mai

kuma zance da Al}ur’ani. Wani abin da Fa]ima ta

ambata shi ne, suna samun fahimtar karatunta

musamman wajen bayyana tafsirin Al}ur’ani. Baitocin

su ne:

186

Da]a ga ni ga Kilo wanga guri ya cika,

Saura Shi kai mu fa cana Firdausi naSa.

Yada nai zaton in gan ta duk haka nig ga ta,

Sai yanda yaz zarce ga ]ammani nasa.

Kai barakalla na ga haske kamilan,

Mai }ayataswa nan ga mai dibi nasa.

Nuri gare ta da haskakawam mas’ala,

Kowa ka son Allah tana }amna tasa.

Koyi da Annabi dud da don shi tar ri}a,

Kuma ba ta zance sai da {ur’ani nasa.

Fa]ima ta kawo kyawawan halayen Modibbo Kilo na

kasancewar ta muzakkara ma raja’i ga Allah da yawan

gode masa, mai tausayi ga tsofaffi na Allah, kuma ta

ri}e su, ri}on }warai. Sannan kuma kowa ya zo wurinta

tana na’am da shi, ta ba shi ci ta ba shi sha, kamar

yadda bayani ya zo a cikin waxannan baitoci, wanda

bai samu zuwa wurinta ba, takan aika masa har gidansa.

Allahu Yai ta muzakkara mai mas’ala,

Mai ko raja’i mai yawan gode masa.

Allahu kau Ya ba ta tausai mai yawa,

Tsoffi na Allah ta ri}e su ri}o nasa.

Kowat tafo, ga ci da sha ga marhaba,

Wani ko fa bai zo har gida aka kai masa.

187

Kilo mai wuyak koyo ga mata sai biya,

Tun duniya har cana Firdausi nasa.

Allahu kau ya mallaka mata ‘yan Adam,

In tay yi foro babu mai gilma masa.

Modibbo tana da wuyar koyo a wanann sashenta

mallaki mutane sosai, domin da zarar ta yi magana a yi

ko a bari anan kar~ar mata nan take. Baiti na 21 Fa]ima

ta ce lalurorinta sun rage da ganin Modibbo Kilo, sai

dai warkewarsu sai a cikin Aljanna Firdausi jiha kuma

zuciyar balta koyaushe bat a hutawa ga tunanin harshen

Modibbo Kilo kuma ku]in biyu ta }ara da fa]ar bat a

son rabuwa da Modibbo Kilo. Ga baitocin da ke xauke

da wannan bayani:

1. Da]a na gane ta tciwarwatata ta rage,

Dub ba ta waraka sai fa Firdausi nasa.

2. Ni dai ina dubin ta Allah Ya sani,

{albi tana can kau tana gode masa.

3. Don zuciyat tau ba ta hutawa lakan,

Sai tuntuni haskenta don nuri nasa.

4. Kukan da niy yi ganin ki Allah Ya sani,

Kilo ba ni son rabuwa da ke don so nasa.

5. Allah Shi kai mu gidammu cana fa lafiya,

Can inda ba rabuwa cikin yarda tasa.

Mai murmushi mai yawan jan tasbaha mai ]a’a ce mai

imani mai maraba da kowa ya zo wurinta ba ta }osawa

188

da shi. Tana da gudun duniya kome take yi tana yi ne

don lahirarta:

1. Mai murmushi ta mai yawan jan tasbaha,

[a’atta tai kyawo da imani nasa.

2. Mai marhaban ta ba ta }osawa da duk,

In ka ishe ta lakan cikin ]a’a tasa.

3. Zuhudi gare ta na duniya ita dai tutut,

Komi takai don lahira taka yi nasa.

Sannan ta rufe w}arta da cewa na yi miki

wannan }asida ne, saboda abin da ke tsakanina da ke

Allah ka]ai Ya san shi. Ta }are da cewa mai halarta

Modibbo ki yi mai kar~ar ku]i kuma ina ro}on Allah

Shi gafarta miki da ni da da jama’ar Musulmi don

albarkacin Almustafa (S.A.W.).

1. Modibbo tau, ni nai }asida don ki san,

Baini wa bainaki wadda am masani nasa.

2. Wallahi sai Sarkinmu Shi ]ai Yas sani,

Baini wa bainaki sai Mala’ikku nasa.

3. Modibbo na ro}e ki, ki mini addu’a,

Allah Shi ba mu muwafa}a don so naSa.

4. Allah Shi gafarta ma Modibbommu nan,

Haka ni da nai fatawa ga addini naSa.

5. Allah Shi gafarce mu don Almus]afa,

Domin Sahabbai dud da Alaye nasa.

189

Ha]uwar Fa]ima da Modibbo Kilo

Bismillahir Rahmanir Rahimi,

Sallallahu Alan Nabiyyil Karimi,

Shi’ir li Fa]ima.

1. Bismil ilahi }ultumu kam hamdala,

Sarkimmu kam Ya ba mu, mun gode maSa.

2. Mun kau bi Manzonai Nabiyyi abin sani,

Hakanan Sahabbainai da Alaye nasa.

3. Allah garai ]ai munka wakkala Ya sani,

Kuma ba mu son wani sai cikin hanya tasa.

4. Shi munka ro}a duk bu}ata kamilan,

Yab ba mu ]ai, saura fa biu ku sani nasa.

5. Yab ba mu, mun tafi Hausa inda Mujadaddi,

Saura mu zo Haramaini can Baiti naSa.

6. Daga can da]a mu wuce Madina muna raha,

Can inda Al-Mukhtari don nasara tasa.

7. Allah Shi sa, Allah Shi sa, Allah Shi sa,

Kilo Allah sanya da mu cikin yarda tasa.

8. Allah muna ro}o, mu gode ma lakan,

Sirran wa jahran na muna gode maSa.

9. Wallahi na gode ma Sarki Ya sani,

Yada nib bi]a yab ba ni don rahama tasa.

190

10. Da]a ga ni ga Kilo wanga guri ya cika,

Saura Shi kai mu fa cana Firdausi nasa.

11. Yada nai zaton in gan ta duk haka nig ga ta,

Sai yanda yaz zarce ga ]ammani nasa.

12. Kai barakalla na ga haske kamilan,

Mai }ayataswa nan ga mai dibi nasa.

13. Nuri gare ta da haskakawam mas’ala,

Kowa ka son Allah tana }amna tasa.

14. Koyi da Annabi du da don shi tar ri}a,

Kuma ba ta zance sai da {ur’ani nasa.

15. Zatil fa hamati ta da da]in mayyaza,

Balle ga tafsiri tana bayyana masa.

16. Allahu Yai ta muzakkara mai mas’ala,

Mai ko raja’i mai yawan gode masa.

17. Allahu kau Ya ba ta tausai mai yawa,

Tsoffi na Allah ta ri}e su ri}o nasa.

18. Kowat tafo, ga ci da sha ga marhaba,

Wani ko fa bai zo har gida aka kai masa.

19. Kilo mai wuyak koyo ga mata sai biya,

Tun duniya har cana Firdausi nasa.

20. Allahu kau Ya mallaka mata ‘yan Adam,

In tay yi foro babu mai gilma masa.

191

21. Da]a na gane ta tciwarwatata ta rage,

Dub ba ta waraka sai fa Firdausi nasa.

22. Ni dai ina dubinta Allah Ya sani,

{albi tana can kau tana gode masa.

23. Don zuciyat tau ba ta hutawa lakan,

Sai tuntuni haskenta don nuri nasa.

24. Kukan da niy yi ganin ki Allah Ya sani,

Kilo ba ni son rabuwa da ke don so nasa.

25. Allah Shi kai mu gidammu cana fa lafiya,

Can inda ba rabuwa cikin yarda tasa.

26. Mai murmushi ta mai yawan jan tasbaha,

[a’atta tai kyawo da imani nasa.

27. Mai marhaban ta ba ta }osawa da duk,

In ka ishe ta lakan cikin ]a’a tasa.

28. Zuhudi gare ta na duniya ita dai tutut,

Komi takai don lahira taka yi nasa.

29. Modibbo tau, ni nai }asida don ki san,

Baini wa bainaki wadda am masani nasa.

30. Wallahi sai Sarkinmu Shi ]ai Yas sani,

Baini wa bainaki sai Mala’ikku nasa.

31. Modibbo na ro}e ki, ki mini addu’a,

Allah Shi ba mu muwafa}a don so nasa.

192

32. Allah Shi gafarta ma Modibbommu nan,

Haka ni da nai fatawa ga addini nasa.

33. Allah Shi gafarce mu don Almus]afa,

Domin Sahabbai dud da Alaye nasa.

Tammat Bihamdillahi.

Allahumma waffi}na bitttiba’i sunnati

Nabiyyika,Muhammadin Sallallahu alaihi wa sallama.

Amin.

193

Nazarin Wa}ar Godiya ga Modibbo Kilo

Wannan wa}a baiti 5 ce [amgoginta bi-bi-yu ne, tana

da amsa-amon waje, wanda ke }arewa da harafin ‘ya’

har }arshen wa}ar.

Malama Fa]ima ta yi godiya ga Modibbo domin

ta karantar da ita da fitar da ita daga duhun jahilci.

Saboda a da can tana cikin ]imuwa da rashin sani sai ta

cece ta, ta fita daga matsalar jahilci. Kuma ta ]ora ta a

kan hanyar }warai mi}a}}iya ta addinin Musulunci

sannan kuma A}ali ya yi wa Modibbo godiya, don

ta ]auke masa nauyin ]awaniyar koyar da wa’azi, sai

ya kasance Modibbo ke warkar da ni ke koyar da

ni }abla da ba’ada.

Waqar Godiya ga Modibbo Kilo

Shi’iru li Fa]ima aydan

1. Wallahi Saudatu ke sanas san na sani,

Can dauri kam na zan cikin jahiliyya.

2. Da kam akwai ni da ]emuwa da rashin sani,

Kilo kinka cetan nif fito jahiliyya.

3. Hanya} }warai duk ke gwada mini na shiga,

Samun ki Saudatu na zamo Mardiyya.

4. Al}ali Yai miki godiya yai addu’a,

Alhamdulillahi batun wa’aziyya.

5. Can dauri shi ka ]awainiya da yawan fa]i,

Kilo kin ka warkas }abla har ba’adiyya.

Tammat

194

Nazarin Wa}ar Bankwana ga Modibbo Kilo Wannan wa}a ce ta bankwana ga Modibbo Kilo ce da

aminiyar ta Malama Fa]ima ta yi mata sa’ar da ita

Modibbo ta ]aura aniyar yin hijira daga Sakkwato zuwa

Makka. Baitocinta 12 ne [angoginta bibbiyu ne, tana da

amsa-amon waje, wanda yake }arewa da ‘ya’ har }arshen

wa}ar. Babu yabon bu]ewa da na rufewa malama

Fa]ima ta bayyana jigon wa}ar tun a baiti 1 zuwa 3,

cikin baitocin malama ta yi bayanin abin sonta,

abin }aunarta kuma aminiyar ta, abida mai }udurin yin

hijira zuwa Makka. Modibbo Kilo ce take yi wa

bankwana tana ro}on Allah Shi kai ta lafiya, ta huta

lafiya a can, kuma ta ce Modibbo Allah Shi ba ki abin

nufi, wato Shi cika mata nufinta sannan Allah Shi kai

Modibbo Madina lafiya, don shi ya iya yin kome da kowa.

Ga baitocin da ke bayyana wannan zance a }asa:

1. Na so abin so tun da nis so abi da,

Mai son zuwa haramani kullum safiya.

2. Modibbo an Allah shi kai ki da lafiya,

Allah Shi futasshe ki sarkin lafiya.

3. Modibbo an Allah shi ba ki abin nufi,

A Shi kai ki cana Madina don Shi ya iya.

A cikin baiti na 6 Fa]ima ta yi bayani cewa ni, ina nan

ina yi miki (Modibbo) addu’a marece da safiya, Allah Shi

cika miki burinki na tafiya zuwa haramaini Makka da

Madina in ki ka je ki ka sauka ke zama lafiya }alau idan

haka ta samu na fi ki murna, don mu }aru da gaskiya ni

da ke, baitocin kamar haka:

4. In kinka tafi haramaini Allah Ya sani,

Na fi ki murna don mu }aru da gaskiya.

195

5. Gurinki ina can zamne dud da abin nufi,

Wurdimmu dai Allah Shi kai ki da lafiya.

6. Allah Shi kai ki, Shi sa ki zamna lafiya,

Shi ad du’a’ina maraice da safiya.

A baiti na 7 da na 12 Fa]aima ta ce muna da nufin yin

hijira mu same ki a cana haramaini lafiya idan Allah Ya

nufa sai dai ki sani tafiyar nan da za ki yi, ki bar ni ta ishe

ni, ta sha mini kai, domin ke bar maraya wanda ba shi da

tarbiyya ni dai ina cewa, Allah Shi kyauta wannan

al’amari kuma wa}ar nan taki ta sa ni damuwa, don na ga

har ke fitar da zango a Barno, kuma ga shi har ke ]aure

kaya ke ]ora a kanki don shirin tafiya.

Waqar Bankwana ga Modibbo Kilo

Bismillahir Rahmanir Rahimi. Wasallallahu, ala man la

Nabiyi ba’ada.

Shi’ir li Fa]ima.

1. Na so abin so tun da nis so abida,

Mai son zuwa Haramaini kullun safiya.

2. Modibbo am Allah Shi kai ki da lafiya,

Allah Shi futasshe ki Sarkin lafiya.

3. Modibbo am Allah Shi ba ki abin nufi,

A Shi kai ki cana Madina don Shi Ya’ iya.

4. In kinka tafi Haramaini Allah Ya sani,

Na fi ki murna don mu }aru da gaskiya.

196

5. Gurinki na can zamne dud da abin nufi,

Wurdinmu dai Allah Shi kai ki da lafiya.

6. Allah Shi kai ki, Shi sa ki zamna lafiya,

Shi ad du’a’ina maraice da safiya.

7. Mu ma muna da nufa zuwa in Yan nufa,

Allah Shi sa mu ishe ku cana da lafiya.

8. Amma zuwan ga ki bar ni, shi kau ya isan,

Allah Shi kyauta tun da Shi ]ai Ya’ iya.

9. In kit tafi kib bar ni ko ke ke sani,

Ke bar maraye wanda ba shi da tarbiyya.

10. Zan so, musiba na ga ]akin duniya,

Mai tad da ciyyo na da yamutce zucciya.

11. Wa}a}}i ta ]ebe ni na ga awa fahar,

Ke fid da zango nig gani mai anniya.

12. Haka nig ga har ke ]amra kaya ke aza,

Ke fid da zango Borno ke ]au anniya.

Tammat.

197

Ratayen Waqoqin Modibbo Kilo

198

199

200

201

202

203

204

205

206

207

208

209

210

211

212

213

214

215

216

217

218

219

220

221

222

223

224

225

226

227

228

229

230

231

232

233

234

235

236

237

238

239

240

241

242

243

244

245

246

247

248

249

250

251

252

253

254

255

256

257

258

259

260

261

262

263

264

265

266

267

268

269

270

271

272

273

274

275

276

277

278

279

280

281

282

283

284

285

286

287

288

289

290

291

292

293

294

295

296

297

298

299

300

301

302

303

304

305

306

307

308

309

310

311

312

313

314